Sashe 93
Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dam dam ƙirjin Najwa ya buga tunani ta shiga yi ko ƙila gidan kakanninsa aka fara kawota kafin a kaita gidanta, dan dama duk kuɗin mai kuɗi yana da 'yan uwa talaka da 'yan kauye, wannan lissafin da ta yi yasa ta ɗan samawa kanta natsuwa kaɗan duk da wani ɓangare yana gaya mata ɗazun taji matar data tuƙosu tace an zo gidanta, haka ta ruɗa kanta da tunani daban daban har suka shiga cikin gidan ta rasa wanne ne matsaya a zuciyarta dan a rikice take. Har aka shigar da ita ɗakinta wanda yake cike da ƙamshin fentin da aka yi, waɗanda suka riga shiga ciki sai guɗa suke yi, ga ɗakin ya cika da mutane saboda kujerunta sun cike ɗakin babu fili sosai, dole sai dai wasu su shiga su fito wasu ma su samu damar shiga, Najwa dai sai da suka danganata da gadonta kafin suka ajeta ta zauna a gefe su kuma suka shiga ganin ɗaki, goggo tana cewa.
Gida kam Tubarakallah sai dai ba kamar wancen na farko ba, Najwa Allah yasa nan É—in gidan zamanki ne yasa nan É—in arzikinki yake.
Nan mata suka amsa da Amin. Sameeha kam tun sadda aka shiga da Najwa ta fito ta tsaya a ƙofar ɗaki tana jiran umma ta fito su wuce, umma kuma tana ciki tana cewa a fito da Najwa a kaita ɗakin maman mijinta sannan a haɗata da kishiyarta duk suna a cikin gidan yanzu 'yar uwar ango ke faɗa, A wannan lokacin ne Najwa ta yaye mayafinta ta miƙe kamar wacce aka tsikara tana daga kai sama tare sa juyawa tana ƙarewa dakin kallo, gaggo tace.
Ke miye haka? ki bari in mun tafi sai ki ƙarewa ɗakin kallo yadda kike so, mayar da yafi muje gurin maman mijinki.
Gaggo gaskiya bana tunanin nan ne gidan da Mujaheed zai aje ni, ko dai anyi musayar ɗaukar amarya ne bamu sani ba, ƙila nan za a kawo wata ba ni ba.
Dalla rufe mana baki ki saka gyale ki zo muje, sai ki adana maganarki in angon yazo sai ki tambaye shi.
Najwa kam a wannan lokacin ji tayi kamar ana zare mata lakka a jikinta dan gabaɗaya ji taji ba tada ƙarfi, gaggo ta ja gyalen ta yafa mata ta kama hannunta tamkar gunki ta jata, ita kuma tana binta kamar rakumi da akala, ganin komai take yi kamar mafarki har yanzu zuciyarta ta gasa gane zahirin da idanunta suke gane mata, haka suka isa ɗakin mama da ita suka zauna a kan tabarma da aka shimfida a falo, ɗaki kam sai tashin daddawa da kayan miya da mama ke sayarwa, nan fa suka gaggaisa, umma tace.
To mama ga amanar 'ya mun kawo muku fatan zaku riƙe mana ita da kyau, in tayi kuskure a riƙa tsawatar mata ana nusar da ita.
In Sha Allah mun karɓi wannan amanar Allah ya kaɗe fitina ya haɗa kanta da abokiyar zamanta. 'yata in kinga an yi miki ba daidai ki riƙa faɗa domin a gyara, rayuwar duniya zomu zauna zo nu saɓa ne, ga kishiyarki nan Safara'u tsawon shekara bakwai kenan ina tare da ita babu wata matsala tana yi mini biyayya da mijinta dai dai gwargwado, sannan kiyi ƙoƙari ki riƙe 'ya'yanta tamkar naki gasu nan Baba da kuma Jamila, Allah ya kauda shaiɗan a cikin zamanmu.
Duk matan dake É—akin suka amsa da Amin, Safara'u ta yashe baki tana cewa.
Sannu da zuwa amaryarmu Ƙanwata, fatan kin zo lafiya da kuma shirin ayyukan gidan nan dan samun lada, ni wlh ina ta murna da zuwanki saboda nima zan huta da wasu ayyukan, Allah ya bamu haƙurin zama.
Ta faɗa, wanda mama ce dake gefenta ta riƙa zunkuɗarta akan ta yi shuru ta san ba hankali ne da ita ba ta riƙa sakin magana tamkar saukar injin markaɗa, matan dake ciki suka ce amin amma suna cike da mamakin maganarta, kowa dai da yadda ya fahimci maganarta. Najwa kam zufa ne ya rufeta duk ta jiƙa kayan jikinta tana jin wani hajijiya akanta tamkar saukan aradu, har yanzu gani take bata farka daga mummunar mafarkin da take yi ba, fatan ta ta buɗe ido ta ganta a gadon inna, haka suka basu abubuwan da ake bawa uwar ango kamar yadda al'ada ta tanadar, suka miƙe tare da yi wa Mama sallama suka mayar da amarya ɗakinta umma tana cewa.
Najwa mu zamu tafi ayi ta haƙuri da rayuwa kinga dai ba ke kaɗai bace a gunsa, ki kama kanki dan na kula wannan uwargidan taki ba tada seti, ki nuna tarbiyya da iliminki a cikin zamanku, ki kama mahaifiyarsa tamkar naki, sai kiga komai yana zuwa miki cikin sauƙi.
Umma tana kaiwa nan a maganarta sai ta juya ta yiwa matan da ke ɗakin sallama ta fito, sauran ma suka fara fita sai ya rage mata kaɗan ne a ɗakin, koda suka fito sun tadda babu motoci dan kawo su kawai suka yi ko wacce ta koma da kanta, Umma dai da Sameeha tuni suka shige mota tare da matan da suka zo suka wuce, Hajiya ma tun ɗazu suka wuce dan Amarya tana shiga ɗakinta suka fito ko ɗakin mama basu je ba saboda haniyar tayi musu yawa. Matan da suka fito da niyyar a mayar dasu haka suka koma cikin gida zuwa ɗakin amarya suna masifar motoci sun gudu, wasu suka fara faɗar ko sisi basu ruƙo ba duk sun zata za a dawo dasu tunda ai ance mai kuɗi ne, dama dai abin duk karya ce nan magana sai ta zama abin gulma, haka suka haɗu su duka suka fito akan su taka a ƙafa in kuma sun samu motar bus a bakin titi sai su hau in sun isa gida baba ko inna sa biya, ƙarshe hatta ƙawayen da suka yiwa Najwa ƙawance basu zauna ba sunbi ayari aka bar Najwa ita kaɗai a ɗaki, sai a falo da 'yan uwan ango suka samu damar shigowa bayan tafiyar 'yan uwanta, a wannan lokacin zazzaɓi mai zafi ne ya rufe Najwa dan har wani nauyi kanta yayi mata saboda sara mata da yake yi, har zuwa lokacin ta kasa gasgata tsakanin mafarki take yi ko zahiri ne, haka ta kwanta daga gefe tana fitar da numfashi mai zafi sannan bugun da zuciyarta ke yi yasa sam jikinta ba ƙarfi ya ƙara narkewa, da kyar ta iya jawo jakarta dake gefe ta ciro wayarta ta cireta a key ta shiga wajen kira ta dannawa Mujaheed kira.
Mujaheed tun ɗazu yana a can saman layinsu tare da wasu abokansa suna hira wanda rabi cikin zullumi yake da fargaban yadda Najwa zata ɗauki lamarinsa, shima bai san ya yi wauta ba sai yanzu da ƙarya ta kare masa ruwa ya ƙarewa ɗan kada, addu'a kawai yake yi Allah yasa ya shawo kanta ta haƙura duk da a ɗan fahimtarta da ya yi Najwa tana son rayuwar hutu da jin daɗi, kullun lissafinta gidan da zata zauna da irin rayuwar da zasu gudanar, yana cikin wannan fargaba ne yaji kira ya shigo wayarsa sai ya dubwa yaga ita ce, nan take yaji zuciyarsa ta tsinke yana niman rasa natsuwarsa, har ta kusa tsinkewa kan ya ɗaga tare da kara wayar a kunne ya miƙe ya bar inda abokansa suke hira ya maƙale jikin wani gida yana saurarenta ba tare da yace komai ba, Najwa cikin dakiya tace masa.
Mujaheed ya naga haka? ina ji kamar mafarki nake yi an kawo ni wani gida ba wanda kavce mini ba, wai da mamanka zan zauna har da kishiya, dan Allah idan barci nake ka farkad da ni, dan lissafina ya kubce na gaza gane tsananin mafarki da zahiri.
Najwa my love gidanki ne nan a zahiri ba mafarki ba, ki bari anjima inna shigo zan yi miki bayanin komai.
Najwa dake kwance sai taji wani ƙarfi ya taso mata ta tashi zaune ta kuma ware idonta tana waigen ɗakin da kyau, sai ta miƙe ta shiga kallon ko ina har zuwa ƙofar data gani wanda ɗazun taji ana cewa bayi ne, taje ta buɗe ƙofar ta leƙa ta dawo ta zauna tana cewa.
Kana nufin duk abin da na gani gaske ne ba mafarki ba, kana nufin zahiri nake gani, kana nufin nan ne gidan da zan zauna da mamanka da kishiya, ashe ma kana da mata baka faɗa mini ba, kana nufin duk zantukanka ƙarya ce ba gaskiya ba, Mujaheed kai wanene? waye ya aiko ka gareni domin ka ƙuntata mini ka tozarta ni a idon maƙiyana, shikenan yau maƙiyana sun ga ƙasƙantaccen gidan da zan zauna bayan na gama yin bayanin gidana babbane filat ne da kayan more rayuwa, kutumar uban can kayyasa to wallahi da sake!
Ta ƙare maganar da ƙarfi sai ta kashe wayarta ta mayar jaka ta aje mayafi ta fito falo, wanda 'yan uwan Ango sun yi shuru suna saurarem maganar da take yi, fitowarta yasa suka bita da kallo itama tana binsu da kallo tare da ƙanƙance idonta, ta kama ƙugu ta soma kallon falon, ga kujeru fa sun cike ɗakin dan dama ba kalar irin ɗakin bane shiyasa suka cike guri, sai ta wuce kitchen shima kallo tayi masa na shaf duk da yana da ɗan girma amma ba sosai ba, kuma ya ɗauki kaya domin har da kitchen cabinet aka yi mata mai kyau, sai ta juyo ta rungume hannyenta a ƙirji tana duban matan dake ciki.
Ku fice mini da gani tun kafin in muku ƙaramar hauka, kun zo kun jaɓe mini a kujera kuna tumurmusa sai ka ce daga gidan ubanku aka kawo.
Haba amarya me yayi zafi daga cin arziki, dama mun zauna ne mu rage miki kewa kar a barki ke kaÉ—ai.
Dalla yaya Jimmai ki fito mu tafi kin tsaya yi mata bayani, ba kiga 'yar rainin hankali bace mara mutunci.