Sashe 80
Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun ranar data bar gidan Najwa take jin ranta babu daɗi dan bata taɓa zaton Najwa zata yi mata haka ba, duk da tasan itace ta ci amanar ta amma amintarsu da kuma taimakon data yi mata na samun cikar burinta bata cancanci irin wannan wulaƙancin ba, yanzu babban tashin hankalinta data san sirrinta data jima tana ɓoyewa, tasan kuma halin Najwa muddun ta matsa mata to zata iya tona mata asiri, dole ne ta nima hanyar sulhu su ahirya ta kuma rabu da Aminu shine kaɗai mafita a garera dan ba zata so abinda tabirne ya tonu ba. Har zuwa washe gari da tunanin ta tashi ta yanke zuwa gidan Najwa dan suyi sulhu. Wajen ƙarfe sha biyun rana ta je gidan sai dai maigadi ya tabbatar mata da babu kowa a gidan tun safe da suka fita da Aminu basu dawo gidan ba, sannan koda ta kira wayarta a kashe cikin sanyin guiwa ta koma gida da tunanin gobe in Allah ya kaimu zata koma ta sameta, kamar zata wuce gidansu Binafa sai kuma ta fasa ta koma gida ta kwanta dakinsu ba jimawa barci ya ɗauke ta saboda jiya bata samu barcin kirki ba.
Yayanta Taju daya shigo gidan a hargitse ya wuce sashin mahaifinsu, nan ya same shi a falo ya zauna ya zayyana masa komai na saƙon da Najwa ta tura masa, ba ƙaramin tashin hankali babansu ya shiga ba dan haka cikin ɓacin rai suka baro part ɗinsa suka shiga sashinsu, a falo suka tadda mamanta nan itama suka sanar da ita salati take ta yi dan itama ta girgiza, Yaya Taju ya tambayi Nafeesan tana ina? Hajiyarsu tace tana ɗakinta a sama, cikin azama ya wuce zuwa ɗakin yadda ya bankaɗa ƙofar ta buɗe yasa Nafessa ta farka a firgice, sai dai kafin ta wastsake daga barci Taju ya rufeta da duka da belt ɗin wandonsa daya cire, ta shiga kwalla ihu tana kiran a ceceta sai dai babu wanda ya zo har sai da yayi mata lilis ya farfasa mata jiki kafin ya tsaya da dukan dan kansa yana mayar da numfashi, cikin huci yace.
Tashi muje falon ƙasa.
Bata yi watawata ba ta miƙe duk da ya tsamama mata jiki, haka ya tasa ƙeyarta suka sauko ƙasa, yadda taga fuskar mahaifinsu da Hajiyarsu shine ya ƙara mata tashin hankali dan nan take kwakwalwarta ta harbo mata da asirinta ya tonu Najwa ta tona mata asiri. Nafeesa ta gurfana a gabansu a ƙasa, Taju ya zauna a cushing ya ɗauko wayarsa ya soma karanta mata saƙon da aka turo masa, jikinta babu inda baya rawa dan sosai ta kaɗu da jin kamar Hamisu ne ya tona mata asiri ba Najwa ba, ana zaton wuta a makareta sai ga shi a masaka, Najwa ta bayar zata tona mata asiri sai gashi Hamisu ne yaci amanarta bayan ya ɓata mata rayuwa, sai ta rushe da kuka mai tsanani duk jijiyoyin kanta sun tashi tasan asirinta ya gama tonuwa, ƙarin takaici har da asirin Binafa ya tona, Taju ne ya daka mata tsawa akan ta faɗa musu gaskiyar abinda ya faru in kuma tayi masa ƙarya saiya karyata in yaso ayi jinyarta, to ya zata ɓoye ma bayan ranar wanka ba a ɓoyon cibi, dole ne ta amsa ƙaddararta tunda kuwa Alhaki kuikuyo ne ta tabbatar da hakkin Sameeha ne ƙila ya soma bibiyarta, tunda tasan da ita aka haɗa komai kusan itace ke ɗaura Nahwa akan yin wasu abubuwa, cikin kuka ta basu labari ta tabbatar musu da hakan ya faru harma da rayuwar da Binafa keyi na lesbian bata ɓoye ba, salati kawai iyayen suke yi Taju kuwa miƙewa yayi jikinsa babu inda bata rawa saboda masifa, ya shiga ya ɗauki Number ɗin da aka turo masa saƙon ya soma kira, sai dai baya shiga kwata kwata, ya dubeta a tsawace.
Ki bani number É—in Hamisu yanzu na kirashi.
Duk da ba waya a hannunta ta haddace number É—insa, nan take ta karanto masa ya saka a wayarsa ya kira, da aka É—aga wayar sai dai macece suka ji, Yaya Taju yace.
Ina me wayar ki bashi.
Sai suka ji ta buÉ—e murya tana cewa.
Baby baby kazo ana kiranka a waya.
Taju sansarai yayi yana jin kayan takaici, har Hamisu ya amsa wayar yana cewa.
Hello waye ne ke magana naga number ne.
Taju ya haÉ—iye miyau kwad na talaici yace cikin faÉ—a.
Da yayan Nafeesa kake magana, wato irin cin amanar da kayi mana kenan ka rabata da mutuncinta sannan ka sa ƙafa ka rabu da ita saboda mugunta, to dan haka ina so mu haɗu ka zo gidamu domin a yi sulhu a gyara lamarin tunda kai ka ɓata ta kai ne zaka aureta..
Kut wlh ni yanzu babu Nafeesa a rayuwata domin kuwa makon daya gabata nayi aure, dama inata son kusan abinda ya faru domin na nima tafiyar ku, don Allah kuyi haƙuri tsautsayi ne amma ina yi mata fatan alkhairi allah ya bata miji nagari, saboda wlh inna ce zan aureta zamanmu bazai yi daɗi ba saboda zargi ne zai shiga tsakaninmu.
Kutumar kaza kazanka ne, ka lalata mana yarinya sannan kana cewa ba zaka aureta ba, to ko yau kayi aure saika auri Nafisa in ba haka ba kuwa ka saurare sammaci daga kotu.
Hmmm yaya kenan, in kuka yi haka ai 'yarku kuka ciwa mutunci domin duk wanɗanda basu san me takaikata zasu sani, kunga kun ɓata sunan gidanku da zubewar mutuncinku, ni kuma duk abinda nayi ado ne wlh babu abinda zai ɓata mutunci na tunda nasan yadda zan kare kaina. Nafisa ko kyautarta kuka bani wlh bazan iya aurenta ba domin na ci moriyar ganga, kuma zuri'arku babu tarbiyya daga 'yan lesbian sai mai bin maza, idan kuma kace zaka ja maganar ina shirye daku.
Sai kit ya kashe wayarsa, tsabar jikin Taju daya yi sanyi komawa yayi ya zauna yama kasa magana, Iyayensu ma kasa maganar suka yi dan a handsfree ya saka wayar sunji duk maganarsa, Nafeesa kuwa kukan baƙin ciki take yi wanda yake cike da dana sani, ƙarin haushinta wai yayi aure ita ya gama da ita, mahaifiyarsu ce ta katse shurun da cewa.
Ya riga ya gama cutar damu kuma kema kin cucemu Nafeesa, yadda nake kula da tarbiyyarku ban taɓa zaton haka ba, dan haka ni zai fi kyau a bar maganar dan mu tsire da mutuncinmu shi kuma mu bar shi da Allah, sai mu tari matsalar mu samu wani mu haɗashi aure da ita, dan wlh aurenta shine namu rufin asirin.
Hmmmm Allah ya kyauta, kuma dole mu bar maganar, sannan Taju ina so Ka yiwa malam Sadi mai yiwa yara karatun islamiyar nan gidan magana ko zai iya aurenta, bana so ka rufe masa matsalarta ka sanar da shi in ya amince sati mai zuwa za a ɗaura aurensu, zan bashi gida kyauta da zasu zauna da ita ke kuma daga yau karna sake ganin ƙafarki koda a tsakar gida ne, sannan Hajiya ki amsa wayarta ki kawo mini. Batun Binafa kuma Taju kaje ka sanar da iyayenta.
Alhaji yana gama faɗar haka ya miƙe ya bar sashin, Nafeesa ta ƙara rushewa da kuka akan haɗin da za ayi mata da Sadi, duk da ba mummuna bane amma bayi da komai talaka ne futuk, kuma babban ci baya ne a auransa ita da take da wayewa da ilimin zamani. Tsawan da Taju ya daka mata yasa tayi shiru ya cigaba da dura mata zagi yana cewa.
Hukuncin Abbansu shine dai dai, haka ya fice daga falon rai a ɓace, Hajiyarsu ta miƙe ta kamota ta zaunar a cushing ta shiga rarrashinta tana cewa.
Dama ki daina wannan kukan kiyi fatan Sadi ya amince da aurenki domin kuwa auren nan shine kaɗai rufin asirinmu, jin daɗi da gata yasa kika saka mana da mummunar tabo amma dai dai gwargwado ina kula da tarbiyyarku, kiyi haƙuri ki barwa Allah zaɓinsa yasa hakan ya zama miki alkhairi, kuma In Sha Allah za ayi miki biki na gata kamar yadda akewa kowa kinji.
Nafeesa ta ɗaura kanta a kan cinyar momynsu tana yin marayan kuka jikinta har ciccira yake yi, dana sani sosai ya wanke zuciyarta wanda take jin dama ana mayar da hannun agogo baya tabbas da ta gyara kuskuran data aikata, tana jin dole ne ta nima yafiyar Sameeha wata ƙila ta samu sassauci daga halin ta taje ciki, dole ne ta saduda ta amsa ƙaddarar data kira da hannunta wanda tarin son zuciya ya kaita ya baro, fatanta Allah yasa Sadi ya yarda da aurenta, a yanzu ba tada zaɓi face zaɓin iyayenta da kuma karɓan ƙaddararta, wataƙila ta samu dacewa ta rabauta, sannan dama ba tada mashinshini ko wanda tasan zai aureta a yanzu, sai ta kara sakin kuka mai tsuna zuciya, ta tuna da Aminu da kuma Najwa tasan itama ko bajima ko ba daɗe dole asiri zai tonu, zata bar Aminu bari na har abada dan ta kama dahir, sannan zata yi ƙoƙarin sanar da Najwa gaskiya ko ƙila zata hankalta ta kama aurenta da kyau, Momyn ta cigaba da buga bayanta ita kuma kukan nadama take fiyarta gwanin tausayi.
[5/7, 9:44 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*
48.
Nafeesa sai da zazzaɓi mai zafi ya rufeta saboda kukan data yi, da kyar momynsu ta lallaɓata ta kaita ɗaki ta samu barci, sai ta fito ta cigaba da ayyukanta. Taju daya fita yayan Binafa ya kira a waya ya tambaye shi ko yana gida, sai yace yana nan a haka suka aje wayar ya ɗauki motarsa zuwa gidan. Daya isa part ɗin mazan gidan ya wuce ya same shi a ɗakinsa wato falo, yana ganinsa ya miƙe cikin fara'a ya miƙa masa hannu suka gaisa kana suka zauna a cushing, Taju yace cikin zolaya.