← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 103

Sashe 77

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Aminu ya amsa da amin yana jin hawaye yana cika masa ido sai kewar mahaifiyarsa ya taso masa, ya mike yana yiwa su baba sallama suma fatan alkhairi suka yi masa sai ya wuce, Ikram ce ta kwalawa su Abi kira, da suka fito tace suje gurin babansu ya fita, Sameeha kam tausayin Aminu ne ya kamata sai ta miƙe ta shiga ɗaki tana matsar kwalla, Ikram ma tabi bayanta duk jikinta a sanyaye sosai itama taji tausayinsa, Najwa kuwa suman zaune tayi tana hawaye mara sauti sai yanzu ne jikinta yayi sanyi jin wai Aminu ya saketa bayan ya tona mata asiri sannan kuma ya rabu da ita ta zama bazawara, Abun da ciwo aure da kwana ɗaya an saketa, wannan wane irin mummunar ƙaddara ce yake binta, ita kam ta shiga uku ta lalace ta samu biyan buƙata a lokaci guda kuma a lokaci ɗaya ta rasa komai, sai kawai ta ruse da kuka mai sauti.

Shikenan na sara komai a lokacin da nake farin cikin na samu, ni kenan banda sa'a a rayuwata, jiya jiya aka ɗaura yau ya sakeni ina zan saka kaina naji saukin wannan baƙin ciki, inna dama sai da kika yi mini baki gashinan ya bini, kun tsaneni saboda na zaɓawa kaina abinda nake so.

Ta cigaba da muka baba ya miƙe yana cewa.

Najwa ai shi mugun abu É—an aike ne muddun ka aikashi wlh sai ya dawo maka, kaÉ—an ma kika gani Allah ya tsayar a kanki ya kuma shiryeki, ke Zulai tashi mu tafi gida, Halima mun gode Allah ya jikan Ahmadu ya yafe masa.

Baba ya ƙare maganarsa yayi gaba, Inna ma godiya ta yiwa Umma akan in an kwana biyu zata dawo sai tabi bayan baba Umma tayi mata rakiya har gate, Junaid ne ya tasa ƙeyar Najwa suka wuce tana kuka wiwi, Zaidu kam miƙewa yayi ya ɗauko buta ya zuba ruwa a inda Najwa ta zauna tayi musu fitsari, ya bi bayan umma data shiga ɗaki suka zauna jugum jugum Ikram ta katse shurunsu da cewa.

Ashe Najwa ta jima tana aikata mana mugun abu wlh ta bani mamaki, ashe makashinka yana tare da kai, gashi ba aje ko ina ba ta wulaƙanta ya saketa a gabanmu kuma jiya aka ɗaura aure yau an saketa, Allah ya kyauta ta gyara mana imaninmu.

Ameen, amma ina so mubar maganar haka dan ba tada daÉ—i, Sameeha sai komai ya wuce a ranki tunda gaskiya tayi halinta ki kama mijinki da kyau, sannan batun yara ki barsu a nan kawai in kin zo hutu kya gansu, bana so a takurawa Ibrahim.

Laaa umma ai baida matsala shima yace da Aminu zai bar mana su, yana da son yara.

Duk da haka ki barsu anan hankali na zai fi kwanciya.

Amma umma bakya ganin su Hauwa zasu nima takura miki in suna nan.

Cewar Sameeha, Zaidu yayi murmushi yana cewa.

Ai da ba yanzu bane Sameeha sun san munfi karfinsu, ai basu isa su kawo mana iskanci ba wlh dan sun san wanda kike aure.

Nan Ikram tasa dariya tana cewa.

Wlh kuwa ai ba zasu yi mana hauka ba, kunsan ni mai ya bani dariya Najwa harda fitsarin Zaune tsabar borin kunya, duk fa wannan maganganun tabarman kunya ta naɗe da hauka, Allah dai ya shieyeta amma tasan munyi gaba hassada kuma ta cigaba da yi muna samun ɗaukaka, zan saka Shamsu ya saka mana kare a gidanmu yadda duk randa ta tako ƙafarta tazo gidana nasa suyi mata rakiya shegiya.

Amma ba kida kirki Ikram nasan ma ba zata zo ba, ai abin da kunya.

Cewar Sameeha tana murmushi, shigowar su Abi da ledar biscuit da chocolate yasa su sauya hira, Zaidu kam sai sam barka yakewa kansa da Allah ya raba shi da Najwa, ɗan ko a ƙafa aka ɗaura masa ita baya jin zai jata.
[5/3, 8:36 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

46.

Aminu.

Bayan ya sayowa yara kayan ciye ciye sai ya shiga mota ya wuce zuwa babban gida dan so yake yau Hauwa ta gane kuranta, yana tafiya yana duban a gogo wanda ya nuna kusan goma da mintuna yasan sun ɓata lokaci sosai a gidan umma, sai ya ji zuciyarsa fes kamar ya sauke wani mai nauyi, na farko ya wanke Sameeha ya kuma bata yaransu sannan kuma ya rabu da Najwa da yake jinsa kamar an ɗaura masa ƙarfe a wiya, yanzu ya zama free sai kuma ya mayar da hankalinta kan batun aikinsa, da farko da aka yi masa tayin aikin yaƙi amsa saboda yaransa da suke hannunsa, yaji ba zai iya barin mahaifarsa ba gwara a ɗaura wani akan tafiya London ɗin, su kuma sun fi so shi ya yi tafiyar domin sun san ba zai basu kunya ba, yafi ƙarfin wata da suke ta binsa da wannan maganar dan har bashi lokaci suka yi akan wataƙila ya sauta ra'ayinsa,sai gashi kuma cikin yardan Allah ya amsa musu da zai yi tafiyar ɗazun da safe ya kiransu, dan yana so yayi nesa da kowa ya yi rayuwa a inda ba wanda ya sanshi, kuma yana so ya mayar da hankalinsa wajen niman lafiya a can ƙila ya dace ya samu lafiyar, da tunani barkatai ya isa babban gida yayi parking a ƙofar gate ya fito ya shiga gidan, ya samu mata da yara ana ta hayaniya da alama basu daɗe da gama karyawa dan yaga kofuna da robobin na suka ci ƙosar birjik a tsakar gida, matan da suka fara ganinsa suka fara sakin guda suna ga Ango ga Ango, Aminu kam murmushin takaici yake yi yana gaishe su, a tsakar gidan ya tsaya ya tambayi Salma data fito daga ɗakin Sa'a ina Hauwa ta kira masa ita, tace masa to kana ta isa shashin Laure ta faɗa mata saƙon Aminu sai cewa tayi ta dawo tace masa ya zo sashin Laure, Aminu ya yi guntun murmushi ya ce.

Ki ce mata ta fito tsakar gidan sauri nake yi.

Salma ta koma ta faɗa mata sai gata tazo buguzum buguzum ta ƙaraso tana cewa.

Haba Ango saurin me kake yi ko amarya tayi ce kira. To gani ya kwanan amarya fatan ka yaba da zaɓina.

Ta ƙare maganar tana tsayawa a gabansa.

Aminu ya kalleta ido cikin ido yana cewa.

Gaskiya kam na yaba da zaɓinki wanda kika saka son zuciya a ciki da son kai, ban ɗauka tsanar da kika yiwa Sameeha har ya kai haka ba, ki rasa wacce zaki aura mini sai 'yar uwarta saboda kawai ki muzguna mata.

Haba Aminu meye laifina dan na zaɓa maka matar da zata share maka hawaye ta kula da kai, yarinya mahaddaciya mai tarbiyya kuma.

Bata rufe baki ba ya daga hannu ya wanka mata lafiyayyen mari kafin ta dawo dai dai ya ƙara marinta a ɗayan kuncin, a gigice Hauwa ta dafe duka kuncinta tana kallonsa a razane idonta a warwaje cike da tsantsar mamaki da tsoro tace.

Ni ka mara Aminu daga abun arziki, in yi maka fari ni kayi mini baƙi, ko dai su Sameeha sun bi boka da malamai sun sauya maka tunani.

Bata rufe baki ba ya dunƙula hannu ya nausa mata a baki wanda nan take bakin ya fashe ya soma jini, Hauwa ta tsandara ihu ta baje a ƙasa tana cewa.

Shikenan sun rabani da É—an uwana innalillahi wa inna ilaihir raji'un, Aminu ni kake duka ina matsayin yayarka.

Aminu ya daka mata uwar tsawa wanda yasa mutane duk suka taru akansu, waÉ—anda suke nesa ma da basu san ana yi ba suka matso.
Chapter 77 · 0% Book details