← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 103

Sashe 71

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana faɗar haka ya juya, itama tabi bayansa tana ware ɗankwali ta ɗaura akai ta fice. Suna shiga ta samu gefe ta zauna nesa da 'yan uwanta, baba ya kalleta rai ɓace.

Ya aka yi kika haÉ—u da Aminu har kuka yanke shawarar auren juna, domin an saka bikinki lokacin bai daÉ—e sosai da sakin Sameeha ba.

Ni fa yayarsa Hauwa ta roƙeni Allah da Annabi in yarda da auren ɗan uwansu saboda ta yaba da hankalina, har aka ɗaura bamu haɗu da Aminu ba dan bai san nice matar da Hauwa ta zaɓar masa ba, saboda ita ce ta buƙaci kar ya sani, amma muna waya da juna sai dai bai ɗauki muryata ba.

Yanzu dama Najwa duk wannan shirin Hauwa ce munafuka, duk yadda suke da Sameeha basa ƙaunarta amma suka jawoki a jiki domin su ƙara muzguna mata duk da ya rabu da ita, idan ita ta saka son rai a ciki ke meyasa ba zaki duba alaƙarki da Sameeha ba ki ƙi yarda da buƙatar ta, yanzu kin kyauta mana kenan? kina son ki zama silar lalawar zumuncinmu da iyalen yaya Amadu.

Cewar inna cike da tsantsar damuwa, yaya Junaid ya ce cikin faÉ—a.

Ni wlh ban yarda da maganar yarinyar nan ba karya take yi, ita tasan yadda ta tusa kanta garesu har suka yarda ya aureta, na tabbatar mugun son duniyarta yasa ta zaɓi auren mijin Sameeha.

Zan yarda da bayaninka domin lokacin da su Sameeha suka bar lagos suka dawo nan Kaduna, yarinyar nan da ta je gidan ta haɗu da mijin Sameeha, ta dawo gida tana yi nuni surutu akan mijin Sameeha shine daidai irin mijin da take so ta aure, a lokacin na kwaɓeta tace mijin ta bar maganar, ashe abin yana ranta saida ta san yadda tayi ta samu ta aureshi, Allah ya wadaran halinki Najwa, basan a ina kika samo irin wannan son zuciyar ba, idan kin shuka alkhairi zaki gani haka ma in sharrin kika shuka In Sha Allah za ki gani.

Inna kiyi haƙuri kar ki yi mata mugun baki, tunda an riga an ɗaura mu bita da fatan alkhairi Allah kuma ya shiryeki.

Inji Sadiq da yake shi ustaz ne, nan dai suka cigaba da yi mata faɗa, suka yi mata kaca kaca Najwa dai sunne kai tayi tana ta ƙunƙune sam babu abinda ya shiga jikinta na faɗar da suke yi mata, cewa ma take a zuciya.

Na kusa bar muku gidan gabaÉ—aya na huta, kuma wlh sai kun nimeni zan zo ma gidan.

Tana faɗe tana kwafa, su kuma suna cigaba da yi mata faɗa, daga bisani suka yi mata nasiha sai suka sallameta ta fito su kuma suka cigaba da tattaunawa. Najwa tana shiga ɗakinta ta samu Nafeesa ta fita taro wasu 'yan ajinsu na islamiya sun zo basu gane gidan ba, sai ta bar waya a chargy ita kuma Najwa ta ɗauki wayar akan tayi waya da Aminu tace masa ya turo mota da wuri na ɗaukar amarya, ta zauna a bakin gado ta duba contact ɗinta bai hau kan wayar Nafeesa ba saboda a email take saving, Allah yasa ta haddace number ɗin Aminu akanta, sai tayi dialing number, abinda ya ɗaure mata kai ganin sunan Amina ya fito daga number, wato akwai number ɗin a wayar anyi saving, da sauri ta cire Number ɗin ta duba wajen kira, tana kuwa dubawa taga ko jiya sunyi waya, nan take ta shiga WhatsApp ɗinta ta duba number ɗin taga chart ɗin su suna magana a online, jikin Najwa ya soma rawa sai dai bata yarda ta bayyana hakan a fili ba saboda kar sauran ƙawayenta su gane, ta shiga chart ɗinsu taga hira sosai suka yi sai dai kafin ta karanta taji muryar Nafeesa sun shigo gidan sai kawai tayi saurin fita ta goge duk abinda ta san ta duba ta miƙe da sauri ta isa ta mayar da wayar a chargy, ta juyo kenan sai gasu sun shigo da fara'a ta isa ta rungume 'yan matan da suka zo su biyu, sai gumi take yi kamar wacce ta haɗiye ƙarfe dan ta kaɗu sosai dacin dunduniyar da Nafeesa take yi mata, hakan yana nufin ta fara hulɗa da Aminu ne domin ya aureta ne ko kuma ta tona mata asiri itama ta rasa mijinta kamar yadda ta rasa saurayinta, ta kaɗu sosai dan tasan babu sirrinta wanda Nafeesa bata sani ba, haka dai take ta saƙa a zuciya tana yiwa mutane yake suna hira dan ta kasa saka musu baki, bata sake marmarin ɗaukar wayar ba sai in an kirata ne Nafeesa ta ɗaga ta yiwa mutane kwatance dan ba zata yarsa wayar ta shiga hannun Najwa ba saboda tsaro, sai a lokacin ne taji dama bata saka mata sim ba dan kar ta gane suna magana da Aminu. Haka suka yi yinin bikinsu cike da armashi duk da bakin amarya a fashe yake, kuma ta cigaba da sauya kaya ana gyara mata kwalliya, a ranar salla dai tace haɗawa zata yi in an kaita gidanta sai ta rama dan bata son abinda zai ɓata kwalliyarta, sai dai abinda Nafeesa tayi mata ya tsaya mata a rai, tana saƙa da warwara akan irin hukuncin da zata ɗauka a kanta.

Bayan sallar magrib ne aka zo da motar ɗaukar amarya, Hauwa da Laure da sauran dangi dasu aka zo ɗaukar amarya, dan a lokacin ne suka ga ya dace su bayyana kansu yadda su Sameeha zasu kurɓi gumar mamaki, sai dai abinda basu sani ba sun riga da sun san Aminu ne mijin Najwa, shiyasa suka yita baza ido su gansu amma ba ko ɗaya hatta ummansu ma basu ganta ba, hakan yasa suka yi zargin ƙila sun sani, sai bayan sallar isha'i aka basu amarya, koda ƙanwar baban Najwa Salima wacce take aure a Kano ta kama Najwa ta kaita ɗakin Inna akan ko zata ƙara yi mata faɗa, cewa tayi.

Allah ya kaita gidanta lafiya ya sadata da alkhairin gidan ya rabata da sharrinsa. Zaku iya tafiya.

Daga haka taja baki tayi shuru Najwa kam ko irin kukan nan ta rungumo inna bata yi ba, sai ta miƙe ta fice dan hankalinta yayi gidanta a kaita kawai saboda ta gaji da takurar innar, inna kuwa siriri hawaye ne ya sauko mata tana tunanin makomar auren 'yarta wanda har yanzu zuciyarta ta kasa kwanciya da shi, haka aka saka Najwa a mota suka wuce da ita gidanta tare da 'yan rakiyar 'yan uwa da ƙawayenta, sai dai dangin Inna da yawa babu wanda yaje dan sosai lamarin ya bata musu rai, wasu ma yamma nayi suka bar gidan, dangin Baba ne da su basu ga aibun auren ba sune suka yi shagalin biki cikin farin ciki da rakiyar amarya.

*****

Sameeha.

Suna isa gida Zaidu ya saka Anwar ya É—auko katuwar tamarba ya shimfiÉ—a musu a tsakar gida, nan suka zauna kowa yana mayar da numfashi mai cike da damuwa, umma ce ta katse shurunsu da cewa.

Zaidu da kai da Ikram banji daÉ—in abinda kuka aikata ba, koma meye ai aure suka yi ba haramci ba, sannan ma Aminu baya tare da Sameeha.

Amma umma ai wannan cin amana ne wlh koda ya rabu da ita, ya rasa wacce sai aura ba sai Najwa hakan bai dace ba, itama munafuka in ba ta saka son zuciyata ba ai tasan ana barin halak dan kunya.

Cewar Ikram tana share kwallarta, Umma ta dubeta tana cewa.

Ai ni kun gama zubar mini da mutunci tunda kuka yi abin kunya a gidan biki, ko ba komai Najwa 'yar uwarku ce bai dace in rai ya ɓaci hankali ya gushe ba, to ma da Aminu ya je ya ɗauko wacce bamu sani ba ai gwara ya aura wacce muka sani kodan tarbiyyar yaran nan su Abi.

Kefa umma gabaɗaya bansan meyasa kika kasa hango laifin Najwa ba, to bari kuji a ɗan nazarin dana yi na gano komai daya faru a tsakanin mutuwar auren Sameeha. Idan nace muku Najwa tana da saka hannu dumu dumu wajen yiwa Sameeha sharrin lesbian wlh babu musu ko kaffara, domin an saka bikin Najwa wata shida bayan mutuwar auren Sameeha, kuma wlh Najwa tana da masaniyar Aminu ne mijin da zata aura, zan iya ce muku Najwa bakinta ɗaya dasu Hauwa dan in har Hauwa bata yarda ya auri Najwa ba hakan bazai taba yuwuwa ba, bikinta saura wata hutdu aka saka nasu Ikram wanda akayi da wata biyu kafin aka zo aka yi na Najwa yau, kenan akwai wata a ƙasa, ko Aminu bai san Najwa ce matarsa ba ko kuma ya sani da biyu ya yarda dan ya ƙuntata miki Sameeha. Amma 'yan uwan Aminu da Najwa da saka hannunsu a cikin sharrin da aka yi miki aurenki ya mutu.

Wlh na yarda da kai yaya domin biri yayi kama da mutum, domin lokacin da aka yi walimar dawowar su Anty Sameeha naga yadda Najwa take shige musu suke magana banga wata alamar hantara ko rashin mutunci a tsakaninta dasu ba kamar yadda suke nuna mini. Ina kyautata zaton Najwa tana son Aninu tun lokacin data fara zuwa gidan ta ganshi, wataƙila son duniyarta yasa ta ke ganin zata iya aurensa, amma gaskiya zata yi halinta In Sha Allah.

Cewar Ikram, Sameeha kam zuwa yanzu hawaye take yi dan har lokacin bata fita da mamakin Aminu ba da Najwa, kuma ta hango ƙamshin gaskiya a manganun su Zaidu, umma ta nisa tace.

Ina fatan duk kan abinda yake a rufe Allah ya bayyana shi, mu daina maimaita maganar dan ƙara ɓatawa mutane rai zai yi, Ikram in da ƙarfi a jikinki tashi ki dafa mana ko taliya ce tunda bamu ma ci abincin gidan bikin ba muka baro, kuma rana tayi hantsi ya duba ludayi.

Umma bari na dafa ni zan iya.
Chapter 71 · 0% Book details