← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 103

Sashe 66

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da yamma Ibrahim ya ɗauketa zuwa wani super market dan tayi siyayyan kayan abinci data duba babu wasu a cikin cefanen da aka yi mata, Ibrahim yasha ƙananun kaya yayi kyau ita kuma ta saka ash ɗin jallabiya tasha aiki ta yane kanta da gyalen abayar, suna isa suka yi parking Security suka fito suka buɗe musu motar dan dama suna biye da motarsu a baya, sannan suka take musu baya suka shiga ciki, wani sucurity ya kamawa Sameeha keke ita kuma tana zabar abinda take so tana sakawa a ciki. Aminu tun shigowarsu ya angeta sai yayi sauri ya tare yaran kar su ganta saboda tare dasu ya zo siyayyar kayan ciye ciye na makarantarsu, tunda ya ganta zuciyarsa ta shiga bugawa da sauri da sauri yaga ta sauya komai nata ya nuna hutu da jin daɗi, yadda yaga Ibrahim yana take mata baya yasan mijinta ne kuma dama ya waye shi tunda Senator Ibrahim dole mutane sun waye shi, ko ba a fili ba a hoto ko a tv, Allah Allah ya riƙa yi su fita dan kar yaran su ganta shiyasa yayi sauri ya jasu suka isa wajen biyan Kuɗi duk da basu gama sayayyar ba, ya biya kuɗi aka zuba musu a leda ma'aikata gurin suka kai musu mota, ya buɗe mota da sauri yaran suka shiga shima ya shiga mazaunin driver yana shirin tada mota, Sameeha ce ta fito da sauri zata ɗauki wayarta data bari mota akan zata kira iya mai aikinta ta tambayeta wasu abubuwan da babu a kitchen ɗinsu na abinci su saya musu, Abi shine ya fara ganinta yayi wani zullo yana cewa da ƙarfi.

Laaaa Abba ga Mamanmu wlh ita ce mamanmu ce, Amrah ga Mama.

Amrah ta shiga raba ido tana kallon inda Abi yake nuna mata, aiko tana tozali da Sameeha ta buɗe mota ta fita da gudun ta bi ta isa gurin Sameeha data buɗe mota ta miƙa hannu dan ɗaukar wayarta sai taji an faɗa mata ta baya an riƙe ta da ƙarfi ana haki ba tare da anyi magana ba, da sauri ta juyo dan taga waye sai kawai tayi tozali da Abi yanata yi mata dariya ga hawaye kwance aidonsa, Amrah kuwa taƙi sakinta dan ta ruƙunƙumeta tana kuka, dan ji take kamar zata ɓacewa ganinta, Sameeha cikin rawar murya tace.

Abi Amrah kune, in abbanku?

Yana mota har zamu tafi mun gama sayayya naga kin fito daga ciki ashe Mama kina cikin garin nan baki zo ba.

Mama wlh saina biki gida bazan koma gurin Abba ba.

Cewar Amrah data ɗago tana kallonta ido shaɓe shaɓe da hawaye, kallonsu kawai take yi yaran sun sauya mata dan sosai suka ƙara yi mata girma ga fresh da suka yi na hutu, ta tabbatar suna samun kulawa mai kyau a gurin mahaifinsu. Ibrahim ne ya fito ya dubata dan yaji shurun yayi yawa sai ya hangeta tare da yara suna magana, ya ƙaraso security na biye dashi su biyu, yana ganin yaran ya tabbatar da yaranta ne saboda Amrah tayi kama da ita sosai, cikin fara'a yace.

Ko ban faÉ—a ba yaranki ne ko? Big boy ya sunanka.?

Ya miƙawa Abi hannu sai dai mai miƙa mata ba ya tsaya yana kallonsa dan bai waye shi ba, Sameeha ta dan yi murmushin yaƙe tana cewa.

Abi shima babanku ne ka amsa masa magana mana.

Abi yace sunana Adam, wannan kuma Ƙanwata ce Amratu.

Masha Allah Allah ya muku albarka Amin. Hajiyata ya aka yi kika haÉ—u da yaran nan.

Suma siyayya suka zo yi sun gama zasu wuce shine suka hango fitowata.

Ayya to bari na jiraki ki gama da su kin san nan É—in ba tsaro sosai.

Cewar Ibrahim kana ya buɗe mota back seat ya zauna ya rufe ya shiga amsa waya, Aminu yana hango su amma yaƙi zuwa ganin yaran zasu bata masa lokaci ya fito yana kwala musu kira.

Kai Abi Amrah kuzo mu wuce.

Ni dai Mama ke zan bi.

Cewar Amrah tana maƙewa babansu kafaɗa, Abi da yake yaron yana da wayo ya fahimci wani abu dan haka ya isa gurin Amrah yace.

Kizo muje Abba zai kaimu gurinta kinji.

Ni dai ba zan je ba.

Haba Amrata Abban kike cewa ba zaki bi shi ba, kije zan zo har gida na ɗaukeku, karki ɓatawa Abba rai yayi fushi, ko kina so Allah ya saka ki a wuta ne kin ɓata masa rai.

Cewar Sameeha, Amra ta girgizata mata kai alamar bata so Allah ya sata a wuta sai Sameeha ta kama hannunta ta jata tana cewa.

Yauwa yarinyar kirki kije gurin Abba da kaina zan zo na É—auke ku.

Amrah bata ce komai ba sai ɓata fuska data yi a haka har suka isa gurin motarsu Sameeha ta buɗe back seat ta tura Amrah ciki kana ta rufe motar ta juya ta kalli Aminu tana cewa.

Nagode da ganin yarana cikin kyakkyawar kamala, amma ina so ka gane ka daina ɗaukar alhakinmu domin ni dasu muna buƙatar juna.

Tana gama faɗar haka ta juya ta wuto gurin mijinta ko waige bata yi ba, duk da zuciyarta a karye yake abu kaɗan zai iya saka ta fashe da kuka, dan sosai kewar yaranta suka taso masa har take jin wani damuwa a zuciyarta, Aminu kam bai ce mata komai ba ya buɗe mota ya shiga ya kunna ya rufe ta ciki dan kar Amra ta yi yunƙurin buɗewa, ya jasu suka wuce Amrah tana kwalawa Sameeha kira tana kuka.

Maama, maaamaaa mun tafi dan Allah ki zo ki É—auke mu.

Sameeha buÉ—e mota tayi ta shiga ta zauna gefen Ibrahim ta shiga matsalar kwalla, bai ce mata komai ba ya cigaba da hidimarsa domin kishi ya motsa, dan gani yake ganin Aminu ne ya sata kuka ba yaran ba.

Tofa...
[4/25, 6:59 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

40.

Sameeha tana kuka tana sharewa Ibrahim ya muskuta alamar zai fita daga motar yana cewa.

Da alama siyayyar nan ba zai yuwu yau ba tunda ganin tsohon mijinki ya tada miki hankali, ban zaci har yanzu kina son sa ba ai.

Da sauri Sameeha ta ɗago kai tana mamakin maganarsa sai a lokacin ne ma ta fahimci fuskarsa ta sauya bata wani ɓata lokaci ba ta matsa ta rungumeshi ta gefe tana share hawayenta.

Ni ba saboda shi nake kuka ba domin koda na ganshi babu abinda naji a raina saboda ka gama maye gurbin zuciyata, ni 'ya'yana ne suka bani tausayi saboda ya rabani da su, ƙiri ƙiri tun da muka rabu ban sake saka su a ido ba sai yau, haka suma yaƙi bari suzo inda nake, Amrah ce ta saka ni kuma da zasu wuce take maganar in zo in ɗauke su.

Sauke ajiyar zuciya yayi yana cireta daga jikinsa ya juyo da kyau suna kallon juna yana cewa.

Nafahimta amma me zaisa shi yin haka bayan ba rabuwar tashin hankali kuka yi ba, ai ba a raba uwa da 'ya'yanta dan sai mutum yaji kunya, idan kinsan inda suke gobe In Allah ya kaimu sai driver ya kaiki ki gansu, in ya baki yaran sai su zo su zauna damu ni ba ni da damuwar haka.

Nagode nagode Mahboob É—ina kuma ni ba zan je ba domin in ya kula ina son ganin yaran zai nima muzguna mini, idan sun dame shi da kanshi zai kawo su.

Hakane, yanzu ina gani ki zauna bari na saka security su ƙarasa siyayyan'r dan bazan so ki fito haka ba.

Ina ganin ma a haɗa kayan da muka siya in yaso sai a aiko a ƙarasa siyayyar zuwa gobe in Allah ya kaimu.

Cewar Sameeha, nan take Ibrahim ya kira ɗaya daga cikin security ɗinsa ya bashi umarnin ya amso kayan da suka ɗiba ya haɗa masa da ATM ɗinsa, ba jimawa ya dawo suka saka kayan a bayan boot kana ya saka wani security ya jasu shi kuma yana maƙale da Sameeha a baya ya rungumeta suna duba wani abu a yawarsa, suna yi suna hira ƙasa ƙasa tare ɗan murmushi kan fuskarsu a haka suka isa gida. Sameeha sam ganin Aminu bai wani dameta ba saboda tana da Ibrahim daya maye mata gurbinsa, sannan ma a wasu abubuwa na rayuwar aure Ibrahim yafi Aminu gogewa da wayewa sosai, shiyasa komai in yana yi mata take ganinsa a sabo dan bata saba da hakan ba, yanzu ne dai take kokarin sabarwa kanta, yaranta sune damuwarta kuma sune burin da ya rage mata ta gansu kusa da ita amma ta kula Aminu ya ɗauki lamarin da zafi, amma dole zata zuba masa ido taga iya gudun ruwansa dan dole wata rana zai nimeta akan yaran.

****

Aminu.

Koda suka isa gida rigimar da Amrah ta saka masa yayi matuƙar bashi haushi har sai da ya kai hannu ya bige ta abinda bai taɓa yi ba, wanda in za a bincika zuciyarsa cike yake da haushin ganin Sameeha da wani ya haifar da fushinsa, ganin yadda ya daki Amrah yasa Abi ya natsu suf-suf ya shige falo ya barsu a farfajiya, ya samu baaba a ɗakinta ya sanar da ita komai, sai ta fito falon ta samu Aminu a zaune ga Amrah can gefe tana kuka, wajenta ta isa ta fara rarrashinta kafin ta ce su wuce ɗakinsu su rage kayan jikin su tana zuwa, sai da ta tabbatar sun wuce kafin ta duba Aminu rai ɓace tana cewa.
Chapter 66 · 0% Book details