Sashe 30
Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A takaice Aminu sai da ya ɗauki sati baya cikin hayyacinsa, saboda ya samu internal injury saboda jini ta hanci ta baki ya riƙa fitarwa. Ga karaya a ƙafarsa ta hagu sannan ga wani ƙarfe daya cakan masa mararsa wanda sai da aka yi masa ɗinki a gun, abubuwa dai masara daɗi ya wakana a wannan hatsarin. Sameeha a lokacin da labari ya isheta kamar zata yi hauka dan saida tayi kwana biyu bata san inda mijinta yake ba, office ɗinsu Aminu ta je a nan ne suma suka san ba a ganshi ba, dan suma sunta ƙoƙarin kiransa bai shiga ba. 'Yan office ɗin sune suka tsananta bincike har aka gano inda yayi hatsari tare da sanin asibitin da aka kai shi. Sameeha ta kira gida ta faɗa musu suma sun yi matuƙar shiga tashin hankali sosai ga mutuwar Umma ga kuma Aminu da ake cikin zullumin rasa shi, dan gaskiya Allah ya mufeshi da tsawon rai bisa tarin raunukan daya samu. Sai da yayi jinyar kusan wata biyu a asibiti wanda Kamalu shine ya kula da shi har aka sallamoshi suka koma gida, 'yan uwansa sun so su bar garin ya koma gida ya cigaba da jinya amma yace kar su damu zai yi a nan gidansa, haka suka tattara suka tafi Sameeha ta cigaba da kulawa da shi har tsawon wata shida a lokacin ƙafa ta warke sarai ya dawo lafiya sai tabo ne ya rage. Sai dai kuma baya tantance wari da ƙamshi saboda buguwar da yayi akansa sannan kuma ko kaɗan baya jin sha'awa, hakan yasa yaje asibiti ya ga likita inda likita ya tabbatar masa da buguwar da yayi a kai ne yasa baya jin ƙamshi da wari amma a hankali zai dawo, sannan ɓangaren sha'awarsa kuma ya tabbatar masa da akwai wata jijiya data samu matsala daga mararsa, domin tun lokacin da yayi accident suka bincika suka san haka sai dai sun ɗaurashi akan magunguna wanda suka yi zaton ya samu lafiya sai kuma gashi ya dawo musu, anan likita ya turashi scanning koda ya dawo da result sakamakon ya nuna ba wata matsala a jikinsa hakan yasa likita ya ƙara bashi antibiotics ya tafi. Aminu tun yana ganin lamarin da wasa har sai da ya tabbatar da babban matsala ce tunda ya kasa sauke hakkin Sameeha, rabonsu da ita tun kafin ta haifi Amrah, tausayi take bashi sosai dan tana yawan fama da ciwon mara, hakan yasa dole yake mata wasu 'yan dabaru ta dan samu natsuwa, Aminu ya shiga niman magani bana hausa bana turawa ba, duk maganin daya ji ya shafi matsalarsa zuwa yake ya amsa, sai da aka shafe shekara biyu a haka ba wani sauyi, dalilin daya saka kenan ya nima shawarar Sameeha akan su haƙurcewa juna ya saketa taje ta auri wani dan zamansu haka ba zai yuwu ba tunda ita ke cutuwa, Sameeha tace ita bata yarda ba tunda yana mata 'yan dabaru hakan yayi mata, sannan tana ƙoƙarin kiyaye shan duk wani abu da zai riƙa taso mata da sha'awa, shiyasa ta yakicewa kanta shan wani maganin mata ko ƙarin ni'ima, ganin ta dage masa yasa ya barta suka cigaba da zamansu tunda shima yaga babu wani damuwa a tare da ita kuma yana son matarsa. Sai dai lokaci zuwa lokaci sai yaji kamar babu adalci a cikin zamansu, ko ya yi mata magana rubutawa take yi akan ita zata ita rayuwa da shi a haka kuma ko wani cuta da maganinsa, in sunyi hakuri watarana zasu dace. Hakan yasa suka haka rami suka binne wannan matsalar ba tare da sun faɗawa wani ba balle ya kawo musu shakku ko miskilar fahimta ga zamansu ba, dan ko wani mutum da irin tunaninsa, Sameeha ko mahaifiyarta bata taɓa kuskuren faɗa mata ba balle 'yar uwa o ƙawa, har suka shafe shekara shida a haka sai a wanda a lokacin ne Aminu ya samu transfer zuwa Abuja, shine suka dawo kaduna suka tadda taraliyar data kawo sanadin rabuwarsu.
Aminu daya kawo karshen tunaninsa sai ya kasa danne hawayensa dan yana matuƙar son Sameeha, ga tuna iyayensu da yayi, haka ya share hawayensa ya jingina bayansa ga mota ya rufe ido yana jin, duk abinda Hauwa tayi masa bai ga guda ɗaya daya nuna soyayya ce ba, tsabar son zuciya ce da ƙeta wanda yayi alwashin sai ya gwada mata shima, uwa ɗaya uba ɗaya suke amma sam kowa da irin halinsa.
*****
Sameeha.
Sai da ta tabbatar daya fita kafin ta miƙe da kyar ta fito falon dan duk taji yadda suka ƙare da Jamila, taso ta samu damar yiwa Jamila wasu tambayoyi dan sosai ta zargeta da saka mata wani abu a cikin abinci, sai dai bata samu dama ba tunda ya koreta, data fito falon kamar an ce ta kalla center table nan ta hango farar takarda, gabanta ya yanke ya faɗi dan tasan saki dai ya tabbata yanzu ta haramta ga Aminu, abu kamar wasa amma ta zama babba, ta isa gurin ta duka ta ɗauka sai ta samu kanta da zama a center table ɗin kafin ta buɗe ta karanta cewar ya saketa saki uku badan baya sonta ba sai dai hakan shine kaɗai mafita a garesu.
Kuka ta fashe dashi mai sauti tana ambaton sunan Allah, sai taji Aminun ya yi matuƙar bata haushi dan duk halaccin data yi masa take hange, bai dace ya yanke mata hukunci irin wannan ba, gani take yi kamar har lokacin bai yarsa bata aikata lesbian ɗin ba, ya kamata ace shine mutum na farko da zai shaideta tunda tsawon shekara shida suna cikin wannan matsalar bai taɓa ganin haka daga gareta ba, sannan wayarta yasha amsa yayi amfani da ita bai taɓa ganin wani abu mara daɗi a ciki ba, dan ko film ɗin batsa bata taɓa kallo ba balle tace zata iya biyawa kanta buƙata, sai duk taji ta tsane shi da komai na gidan, kamar an tsikareta ta miƙe ta koma ɗaki ta zauna bisa daddumarta sai ta cigaba da istigfari, wajen takwas saura ta ɗauki wayarta data ɗaura bisa gado ta lalubo number ɗin Zaidu ta danna kira, yana gani ya ɗaga dan yana shirin yin wanka ne ya fita.
Hallo hajiyar ƙanwata zinariyar danginmu, ya akayi kira da sassafe.
Guntun murmushi tayi daya fi kuka ciwo tace cikin dakiya murya a sanyaye.
Yaya Zaidu ina so ka zo gidana kaida Ikram yanzu, amma dan Allah karku faÉ—awa umma nan zaku zo, kayi kamar aikenta zaka yi.
Me ya faru kuma? Ko su Hauwan sun sake yi miki wani abu ne?
Yaya ba lokacin bayani a waya, sai dai in kun zo.
Ok yace mata kana ya kashe wayan yana tunanin to meke faruwa, Allah yasa lafiya yace kana ya cire jallabiyarsa ya saka rigar wandon daya ke jikinsa ya fito daga ɗakinsa yana kwalawa Ikram kira, da sauri ta buɗe labulen ɗakin umma ta leƙo.
Yaya Zaidu shirin makaranta nake yi fa, na kusa yin latti.
Aiko yau ba zaki islamiyar nan ba saboda aikenki zanyi, wani saƙo zaki amso mini yanzu a can kawo cikin sauri.
Yaya muna shirin jarabawa ne fa.
Tunda ba jarabawar bace ai da sauƙi jeki sauya kaya ki fito yanzu, in kuma da uniform ɗin zaki je to sai ki saka hijab ina jiranki a waje.
Zaidu bana son irin wannan fin ƙarfin fa, saboda me zaka hata zuwa islamiya iye? kai me zai hanaka kaje ka amso saƙon.
Cewar umma data fito daga wanka, Zaidu ya shafa kai yana 'yar dariya.
Umma wlh uzurine mai ƙarfi zanje yi shiyasa zan aiketa idan ta dawo da wuri sai taje makarantan tunda nan tashar kawo zata ba nisa. Dalla malama kije ki saka hijab kina ɓata lokaci.
Ya ƙare maganar akan Ikram data tsaya tana sauraren maganarsu da Umma, da sauri ta koma ciki ko uniform ɗin bata cire ba ta ɗauki hijab ɗin makaranta tana gungunai dan sam bata ƙaunar fashin islamiya, ta fito tana cewa umma ba zata zauna ba yanzu zata dawo ta wuce makaranta, Umma tace sai da dawo tana kwalawa Abi kira akan yazo yayi wanka ta fito daga bayi. Ikram ta samu Zaidu ya tare musu napep yace ta shiga, sosai ta sha mamaki ganin tare zasu, sai da suka fara tafiya a hanya yake ce mata Sameeha ce ta kirashi akan suje gidanta kuma bata so umma ta sani tukuna, jikin Ikram yayi sanyi tace .
Allah yasa dai Lafiya.
Zaidu yace Amin sai duk suka yi shuru ko wanne da irin sakon da yake karɓa a zuciyarsa. Suna isa gidan Zaidu ya tsaya biyan mai napep ɗin Ikram ta rigashi zuwa gate ta buga, mai gadi ya buɗe musu sai suka shiga tare da gaishe shi, ya amsa fuska sake dan sosai suke burgeshi da irin gaisuwar mutunci da suke yi masa saɓanin dangin Aminu da suke yi masa kallon uku saura kwata, ya shaida tarbiyyansu sosai kamar yadda Sameeha ta tarbiyyantar da yaranta dan suma akwai gaisuwa da girmama na gaba. Da suka shiga falo ba kowa sai Zaidu ya zauna a cushing Ikram ta wuce ɗakin Sameeha tana buɗe ƙofar ta ganta zaune a dadduma ta ɗaura kanta a gefen gado, da sassarfa Ikram ta ƙarasa gabanta ta tsuguna tana cewa.
Anty ba ki da lafiya ne?
Sameeha ta kalleta cikin murmushi a fuskarta ga idonta yana ciko da kwalla.
Ina yaya Zaidu?
Ta tambayeta ba tare da ta amsa mata nata tambayar ba.
Yana falo in kira shi ne.?
Eh Sameeha tace a takaice, sai ikram ta miƙe da sauri ta fita ba jimawa suka shigo tare da Zaidu wanda shima cikin mamakin kiransa cikin ɗakinta yake yi, tunda matsayinsa na yayanta baida hurumin zuwa ɗakin kwananta in ba babbar lalura ba kamar yadda yake hasashe ba tada lafiya ne, suna shiga ciki Zaidu ya tsaya a kanta yana cewa.
Sameeha me yake damunki kika zabge da rama haka lokaci guda? Ko gudawa da Amai kika yi jiya? Aminu bai dawo bane?
Ya dawo jiya da dare ga sakon daya bar mini da zai fita.