Sashe 65
Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Satinsu ɗaya da amarci Ibrahim ya koma Abuja a cewarsa sati na sama zai zo ya tafi da ita, to tunda ya tafi ta tare a sashin Hajiya barci ne kaɗai ke mayar da ita ɓangaren ta, ba karamin daɗi Hajiya taji ba saboda yadda Sameeha ta mayar da ita mahaifiyarta, in dai tana sashin bata bari ta kauda ko tsinke ita ke komai hatta abinci ita ke dafa musu bata bari masu aiki su girka, cikin ƙanƙanin lokaci ta shaƙu sosai da Hajiya tun tana kunyarta har ta ware suke shan hirarsu. Ikram ma tazo a kwanakin ya kai sau uku Shamsu ke kawota ya tafi aiki sai dare yake zuwa ya ɗauketa, Khairy itama tana jin labarin yadda Sameeha ke yini a gidan Hajiya hakan yasa itama koda yaushe tana hanya da ita ake komai, yanzu ne suka san sun samu surukai, saɓanin Nabila da take nuna musu ko in kula bata damu dasu ba balle su saba suyi jiki da juna. Lokacin da Ibrahim zai tafi ne ya ɗauki Sameeha ya kaita gidan Nabila, baa ta wani sake fuska ba sai wani fuska take a dole ga uwargida, sai dai duk yadda tayi zaton ganin amarya tafi ƙarfin tunaninta domin ta ganta babu raini matar fita anguwa ga kyau ga diri dan har ta fita cikar halitta, ganin bata amshe su yadda ya kamata ba basu jima ba suka bar gidan, shi dama Ibrahim ya haɗasu ne dan su saba koda baya nan Sameeha zata iya zuwa mata suyi zumunci, amma ga yadda ta nuna bata yi marhabun da hakan ba shiyasa Sameeha bata ƙara bi ta kanta ba, ta tsaya iya gidan Hajiya.
*
Ranar Juma'a ya kama kwana sha uku da aurensu ranar ne suka shirya zuwa gidan Umma suyi mata yini, dan washe gari Ibrahim zai zo lahadi kuma su wuce Abuja. Atamfa Sameeha ta saka green mai kyau ɗinkin riga da siket, sai ta saka hijab bata ɗaura ɗankwali ba ta ninke ta saka a jaka, a ranar ta fara fita da sabuwar motarta, kafin ta wuce sai da ta biya sashin Hajiya tayi mata sallama kana ta fito ta wuce gidan Ikram ta ɗauketa a mota dan dama haka suka shirya, kuma Ikram bata iya tuƙi ba tukunna sai an koya mata, itama Ikram atamfa tasha pink tayi kyau masha Allah duk kansu sunyi kumari ga hasken hutu daya fara ratsasu, duk da Ikram baƙa ce amma tayi haske kaɗan kuma ta murje sosai, haka suka wuce gidan umma suna hira a tsakaninsu wanda duk rabi na kewar gida ne da suka yi. Dama umma tasan da zuwansu dan haka ta rangaɗa musu waina da miya da kuma lafiyyyen farfesun naman rago wanda yaji kayan haɗi, koda suka isa sun samu ta gama komai su take jira, Zaidu da Anwar sun tafi Masallacin juma'a ita kaɗai suka samu. Suma saida suka gabatar da sallah kafin suka zauna a falo suka kara gaisheta sannan suka shiga hirar yaushe rabo, umma taji daɗi matuƙa da ganin yaranta cikin kyakkyawar kamala, hakan yasa ta ƙara samun natsuwar ruhi da kuma godiya ga Allah daya nuna mata wannan lokacin da kuma ni'imomin daya yi musu, su Zaidu da suka dawo nan chapter ta ƙaru suka shiga hira sosai cike da farin ciki da annashuwa, bayan sun gama ciye ciyensu suka fito tsakar gida kan babban tabarma da suka saba zama suka ci-gaba da hira, a cikin hirar ne Zaidu ya sako zancen yaran Sameeha yana cewa.
Yanzu Sameeha gashi zaki koma Abuja kinga kin ƙara kusa dasu Amrah, da Aminu shi mai mutunci ne da ya baki su su zauna a gunki in sunyi hutun makaranta suje masa.
Taf kaima kasan ba mai yuwuwa ba ne yadda Aminu ya ɗauka da zafi, tun rabuwarsu ƙiri ƙiri ya ki kawo su balle ya iya bar mata su, kawai dai dole zata nima inda suke tana zuwa ganinsu ko ya kawo su suna yi mata yini.
Cewar Ikram, Umma ta ce.
Gaskiya ba zai bada yaran nan ba, nima nafi yarda da su riƙa zuwa gaisheta su tafi dan kar a takurawa Ibrahima ko.
Sameeha ta yi guntun murmushi tana cewa.
Ni Allah ya saka mini dangana akan yaran, in yaso ya kawo su in ma yace bazai bada ba ya riƙe abinsa dole in su girma zasu nima in da nake.
Haka suka ci gaba da hirar, nan umma ta sako zancen bikin Najwa tana cewa.
Bikin Najwa saura wata É—aya da sati guda yau, Sameeha zaki samu damar zuwa kuwa?
Haba Umma dole na zo saboda Inna ba abin yadawa bace, anko ne ma ba muyi ba, zan barwa yaya Zaidu kuÉ—i ya saya mana Anwar ya kai mana wajen telenmu zan yi waya dashi, In an É—inka sai a kawo umma ki aje mana, biki saura kwana biyu zan zo In Sha Allah har sai an gama komai.
Aiko kin kyauta, ke Ikram tunda kina gari duk abinda ya taso in ya kama ki zo zan kiraki ayi komai dake, ina so ku shiga cikin dangi sosai a dama zumunci daku.
Ni umma wlh banda Najwa taci darajar Inna da babu abinda zai kawo ni bikinta.
Me kuma Najwan tayi miki dan nasan da walakin goro a miya, sam bakwa shiri kamar annabi da kafiri.
Cewar Zaidu, Ikram zata yi magana Sameeha ta kwaɓeta.
Amma nace bana son zancen nan Ikram, magana ta wuce miye amfanin taso da ita.
Ikram faÉ—a mana me tayi? dan na kula sam Sameeha bata so ana faÉ—ar laifin Najwa.
Cewar Zaidu, Ikram tsalam ta miƙe daga gefen Sameeha ta tsallaka gefen Umma da yaya Zaidu ta zauna tsakiya dan kar Sameeha ta kai mata hannu, nan ta shiga basu labarin duk abinda ya faru lokacin biki, Umma salati ta riƙa yi tana tafa hannu sosai suka yi mamakin Najwa, Zaidu yayi 'yar dariya yana cewa.
Ahaf sai dai ba Najwa ba, wlh zata aikata fiye da haka ma, na karanci yarinyar nan kamar yunwar cikina tana mugun son abin duniya da hangen na sama da ita, kunga kuwa daga haka sai Hasssada da kyashi ya samu gurbi a zuciyarta, Allah ya kyauta sai yanzu na ƙara godewa Allah daya rabani da ita, dan wlh ba zan jure wannan halin nata na son rai ba, taje can ta yiwa wani.
Wlh yaya ta bani mamaki ai kaga da kunya tazo inda muke, har yau bata san kalar É—akunanmu ba dan bata zo ba.
Cewar Ikram, Zaidu yace cikin taɓe baki.
Taya zata zo ta tafka abin kunya, ai wlh Najwa sai dai taci darajar Inna aje mata biki amma da dan halinta ne kare ba zata gani ba.
Allah ya kyauta ya shiryeta ni wlh lamarin ta ya fara bani tsoro.
Cewar Umma, Sameeha tace.
Ai sai dai addu'a dan kuwa in da tayi nadamar abinda ta yi to da ta tako ƙafarta tazo gidajenmu ta bamu hakuri, ke kuma Ikram kin kyauta da kika fasa maganar, sai dai dan Allah mu barshi a tsakaninmu kar wanda ya nuna mata.
Dama wa yake da lokacinta, darajar inna dai zata ci Allah yasa ta zauna a auren, dan wannan bakin hali gareta.
Zaidu bana son haka dan fata na gari lamiri, duk lalacewarta jininmu ce fatan shiriya za muyi mata.
Cewar umma, haka suka cigaba da hira har aka kira sallar La'asar suka tashi kowa yaje ya gabatar da nashi. Sai gabda Magrib su Sameeha suka bar gida, umma ce ma ta korasu da so suka yi sai bayan sallar isha'i su tafi tace bata amince ba su tafi ido na ganin ido, cikin farin ciki suka rabu da juna bayan sunyi guzurin sauran waina da farfesu, sannan Sameeha ta turawa Zaidu kuɗi masu kauri akan ya ƙara musu kayan abinci sannan Ikram ta bada dubu hamsin akan akaiwa Inna gudunmawarsu su duka, Zaidu kuma ya bawa umma dubu ashirin ta bada nata gudunmawar, wannan ahali suna cikin rufin asirin Allah da kuma kwanciyar hankali. Samedha sai da ta sauke Ikram a gida kafin ta wuce gidanta itama, a sashin Hakiya ta yada zango da tsarabar data soya a cewarta Umma ce ta ce a kawo musu tare da waina da farfesu, wanda Hajiya shi taci a abincin daranta, dan tana son waina sosai kuma taji dadin wannan, sai wajen ƙarfe goma saura Sameeha ta bar sashin Hajiya ta wuce ɓangaren ta.
Washe gari Ibrahim yazo tunda ya dawo bai zauna ba dan haka a gurin uwargida ya sauka ya kwana, washe gari ma ya ƙara kwana sai ranar monday suka bar Kaduna da Sameeha. Koda suka isa Abuja gida ne mai matukar girma da kyau shima gidan sama ne har yafi gidanta na Kaduna kyau da tsaruwa, haka ta fara sabuwar rayuwa a gidan, Allah yasa akwai maikata har da me aiki wata dattijuwa mai suna iya, cikin kwana biyu ta saba da ita har suke ɗan taɓa hira in ta sauko ƙasa, saboda Ibrahim In ya fita tun safe sai dare yake dawowa, Sameeha bata yarda ta zauna ba dan ita ke girma musu abinci, sai dai Iya ta girka nasu da masu aikin gidan. A rana na uku ne Ibrahim ya kaita gidan Anty Amina can ta wuni sai dare ya biya ya ɗauketa suka koma gida.
***
Ranar asabar.