Sashe 75
Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wajen takwas da wani abu Junaid ya samu Baba a É—akinsa suna magana da inna, Baban ma kunu yake sha da kosai yana karyawa, Junaid ya zauna yana gaishesu kana baba ya kalleshi yana cewa.
Junaidu ya aka yi ne, ka karya kuwa?
Ai baba bani a cikin abincin bikin nan waje zan je na karya. Dama nazo na sanar daku mijin Najwa yace in faÉ—a muku kuje gidansu Sameeha akwai maganar da yake so zaku tattauna a can.
Gidansa yake nufi ko? In kuma yana son magana damu ai nan ya kamata yazo in dai yana kallonmu da daraja.
Cewar Baba yana rufe kwanan kununsa, Junaid yace.
Nifa gidansu Zaidu yace kuje, wataƙila magana ce daya shafesu da yaransa, shiyasa nima nace zanje dan ayi komai a gabana.
To faɗuwa tazo daidai da zama dama na bari mutane su watse naje na samu Halima na bata haƙurin Najwa na auran Aminu, nayi mata bayanin muma ba mu san shi bane mijin ba sai jiya.
Hakane ta cancanta a bata haƙuri gaskiya dan zasu ga kamar mun munafurcesu, amma bari muje ɗin muji me shi Aminu zai ce, Junaid sai ka fita ka samo mana napep ko, ai kema Zulai a shirye kike.
Eh nayi wanka tun É—azu bari na É—auko mayafi a É—akina.
Cewar inna sai ta miƙe ta fito Junaid ma ya fita samo musu abin hawa. Tunda suka kama hanya ko wanne da irin tunanin da yake yi a zuciyarsa, Junaid kuma a hanya ya kira Aminu akan sun tafi gidansu Sameeha yace to kana ya kashe wayar.
Aminu da sauri ya miƙe ya zo ɗakin Najwa ya buɗe ya ce mata ta fito zasu fita ba musu ta biyo bayansa suka fito farfajiyar gidan, ya buɗe mota ya shiga mazaunin driver ita kuma ta tsaya tana jiran ya sanar da ita inda zata zauna, ya buɗe mata gefensa yace ta shiga, ba musu ta shiga ta zauna zuciyarta cike da fargaban ina zai kaita duk gani take wataƙila gidansu zai mayar da ita yace ya saketa, addu'a ta shiga jerawa a zuciya akan Allah ya ɗaurata akansa karya saketa, shi kuma yadda fuskarsa take a sake ba zaka taɓa cewa da damuwa ba, falalar ambaton sunan Allah shiya sanya masa natsuwa da takawakki akkan ƙaddarar data faɗa masa, ya rufe motar ya kunna suka kama hanya, Najwa kanta a sunkuye yake cike da damuwa, zaune take a takure ko hanya bata iya kallo dan fargaba take taga gida ya nufa da ita, a haka har suka shiga unguwar su Sameeha sai a lokacin ne ta ɗago kai, a razane ta kalle shi dan sosai ta firgita da inda zai kaina, cike da tsantsar tsoro tace.
Ina zamu je?
Gidansu tsohuwar matata domin in wanke mata zargi da damuwar ƙuncin da kuka sakata na sharrin da kuka yi mata.
Dan Allah da son Annabi s.a.w karka yi mini haka wlh na tuba bazan ƙara ba, karka tona mini asiri Allah da kansa yace duk wanda ya rufawa ɗan uwansa musulmi asiri shima Allah zai rufa masa.
Hmmm ga sani ga shagali ko, kuma Hadisi ne sahihi sannan ingantacce, amma ai ke baki yi aiki da Hadisin ba domin ke kika fara tona mana asirin da muka jima da birneshi ni da sameeha, yanzu dalilinki kowa sai ya san bani da lafiya. Dan haka dole ki je ki amsa laifinki ki kuma warware musu yadda kika haÉ—a makircinki.
Innalillahi wa inna ilaihir raji'un dan Allah Aminu ka yafe mini kayi mini rai bazan iya dubansu da wannan maganar ba, wlh duk abinda kake so zanyi maka amma banda wannan.
Hmmmm kina ɓata bakinki ne, kamar yadda baki yi tunanin zuwan irin wannan ranar ba kika aikata abinda kike so, dan haka banga abinda zai sa na fasa abinda nayi niyya ba nima.
Najwa ta fashe da matsanancin kuka dan sosai ta shiga tashin hankalin daya fi na jiya muni, Aminu so yake ya kaita ƙasa ya wulaƙantata ya tozarta ta a idon maƙiyanta, dan ta tabbatar suma sun ƙullaceta zasu so suga ta wulaƙanta, ita kuma ba zata yi fatan hakan ya faru ba dan kar suyi mata dariya, wanda tasan Ikram sai ta zuba ruwa a ƙasa ta sha dan farin ciki, da yayi mata wannan hukuncin gwara yace ya saketa ta tafi gidansu, ganin sun kusa isa gidan yasa ta kama wajen buɗewa ta danna dan gwara ace ta mutu da ta muzanta a idonsu Sameeha, tasan idan yaga ta mutu bazai ma ɓata lokacin tona mata asiri ba, in ma ya tona bata duniyar balle taga sunyi mata dariya, sai ta soma kokawa da ƙofar motar amma taƙi buɗewa, ganin fa saura ƙiris su isa yasa ta faɗawa Aminu ta kama sitiyarin mota akan duk su mutu, Aminu ya saka ƙarfi dan ya tureta amma ina itama ta saka nata ƙarfin, gashi a daidai lokacin wata motar tifa data ɗauko yashi ta doso su, salati kawai Aminu yake yi yana cewa.
Shikenan Najwa zaki kashe mu, innalillahi wa inna ilaihir raji'un.
Mu tara a pegi na gaba...
[5/3, 8:03 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*
45.
Aminu ganin da gaske fa Najwa kashesu zata yi, sai ya tattaro Æ™arfinsa ya bisgeta daga gabansa ya wasar da ita a gefe ya kifa mata mari mai kyau, sai ya kama sitiyarin motar yayi gefe da motarsa da mugun sauri dan saura Æ™iris suyi karo da wannan tifar har saida jikin motarsa ya gogi jikin tifar, mutane sai ihu suke suna salati dan sosai kowa ya sadakar da wannan mummunar hatsari daya kusa aukuwa, Ganin sun tsira yasa kowa yana musu sambarka Aminu ya isa gefen titi yayi parking yana mai sauke numfashi ga wani zufa da yake karyo masa saboda tsananin tashin hankali daya gani mararan, Najwa kuwa kuka kawai take dan itama ganin tifar tayo kansu ba Æ™aramin firgita tayi ba, saida taga sun kauce masa yasa ta dawo hayyacinta tana sauke ajiyar zuciya, ashe dai tana tsoron mutuwa ganinta ne kawai da bata yi ba take lissafin gwara ta mutu amma data ga da gaske ne sun kusa mutuwar ta shiga hankalinta, mutane suka dinga tsallakowa suna yiwa Aminu barka shikam hannu yake É—aga masu yana ya gode, saida ya daidaita natsuwarsa kafin ya kuma tada motar suka wuce. Æangaren su Inna kuwa har sun insa gidan, ita ta fara shiga kafin ta sanar da su umma tare take dasu ba kana ta fito tayi musu iso shi da Junaid, a nan tsakar gida suka zauna kan babbar tabarma da aka shimfida musu, Umma ta sako hijab ta fito suka gaisa kana su baba suka bata haÆ™uri akan abinda ya faru jiya da kuma nuna mata suma basu san da lamarin ba sai a jiyan, umma tace ba komai haka Allah ya Æ™addara, sai suka yi É—an jim kafin Junaid ya isar mata da saÆ™on da Aminu ya sanar musu wanda yasa suka zo, umma tayi shuru tana mamaki tare da tunanin mai zai kawo Aminu gidansu bayan tun da ya saki Sameeha bai sake waiwayarsu ba, sai ta nisa tace Allah ya kawo shi kana ta miÆ™e ta shiga cikin É—aki, ba jimawa su Sameeha suma suka fito suka gaishe su harda Zaidu dan duk suna a tare ne a É—akin Umma sun gama karyawa, nan umma ta saka Zaidu ya bawa inna haÆ™uri akan abinda yayi mata jiya tace ba komai ai ya wuce, sai ya matsa kusa da Junaid suka shiga yin hira su Umma ma suna nasu.
Aminu suna isa ƙofar gidansu Sameeha yayi parking ya kashe motar ya fito, Najwa ma fitowa tayi ya rufe motar ya tasa ƙeyarta suka shiga gidan, Najwa sai sunne kai take yi jiki a mace domin ruwa ya karewa ɗan kada, sun tadda har su inna sun iso suna zaune a tsakar gida bisa babban tabarma da alama zuwansa ake jira, ganin yana tare da Najwa yasa suka fahimci maganar ta shafesu duka ƙila kan batun aurensa. Su Abi suna jin muryan baban da yayi sallama suka fito daga ɗakin umma suka rungume shi ya kama su yana cewa.
Yaushe kuka zo kaduna.?
Shekaran jiya tare da mamanmu.
Abi ya bashi amsa, Aminu yayi guntun murmushi.
To yayi kyau ku koma É—aki in mun gama magana sai na kiraku mu yi magana kan na wuce.
To suka ce masa sai suka koma cikin ɗaki, shi kuma ya samu guri ya zauna kusa da inda Najwa take zaune, ta rufe fuskarta da mayafi bata buɗe ba balle tasan su waye zaune a tabarmar, zuciyarta ta gama tsinkewa sai bubawa take yi kamar zata faɗo ƙasa, Aminu daya zauna suka gaisa da su uma gabaɗaya sai a lokacin ne Najwa ta gane dasu innarta a gurin, take taji fitsari ya kamata jikinta ya ɗauki rawa, jin Baba ya soma magana yasa ta natsu tama rasa me zata yi.
Yauwa Aminu gamu mun zo sai ka faÉ—a mana dalilin taruwarmu a nan.
To baba maganace Nazo da shi akan abinda ya shafeni da kuma Sameeha sai kuma Najwa data shigo ciki, in ba damuwa a kira Sameeha tazo ayi maganar da ita.
Nan take Umma ta kwalawa Sameeha kira sai gata ta fito sanye da hijab ta ƙaraso ta zauna daga gefen tabarma, sai ga Ikram ma ta fito ta zauna daga bakin ƙofa dan so take taji meya kawo su. Aminu ya cigaba da magana ya fara basu labarin dalilin sakin Sameeha da yayi dama yadda ya kamata da waɗannan 'yan matan, su inna da basu san zancen ba suka shiga mamaki sosai, Sameeha kuwa kuka ta fara mara sauti dan ya tuno mata da mugun giɓi da kuma ƙoƙarin tona maganar da yayi gaban su inna, Aminu ya cigaba da cewa.