← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 103

Sashe 25

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ranar gidan kakanninta dake kawo ta kai ziyara, wato gidan iyayen ummansu, a can ma ta samu su umma dan sunyi dama zasu haɗu domin su sada zumunci. Ɓangaren su Binafa kuwa bayan sallar la'asar sun zo gidan Sameeha da shirinsu dan ƙaddamar da aikinsu da suka gama shirya masa, ko da suka zo mai gadi ya buɗe musu suka shiga ya saba da ganin sun zo ko da mai gidan bata nan hakan yasa bai damu ba, dan ya hango akwai alaƙa mai ƙarfi a tsakannsu da Sameeha ta 'yan uwanta taka. Jamila ta san da zuwansu dan komai Najwa ke faɗa mata, hakan yasa suna buga ƙofa ta zo ta buɗe musu suka wuce ɗakinta Jamila suka zauna a gefen gado bisa umarnin Najwa data ce ta basu damu su zauna a ɗakinta kuma zasu jira Saneeha ta dawo amma kar ta sanar da ita akwai baƙi, hakan yasa tayi gum da bakinta domin cike aikin sauran dubu goma daya rage zata bata, saboda tun ranar farko data samu sa'ar sakawa Sameeha maganin nan to Sameehan bata sake shan wani fruit ba sai juice ɗin roba take sha, kuma abinci da kanta take dafawa ta ɗiba nata kafin take kiran Jamila ta ɗauka nata, kamar tasan ana shirya mata wani abu kuma ita a bangaren ta gani tayi smoothy ɗin data sha rannan shine ya sakata sha'awa, shiyasa ta hakura da shan duk wani fruit dan kar ya tada mata zaune tsaye tunda ba miji a kusa, sai ta koma shan lemun gora kuma tunda ta daina shan fruit ɗin bata sake jin wani matsala irin da wancen ranar ba, shiyasa ta samu nutsuwa saboda tayi maganin matsalarta. Jamila kuwa sanar da Najwa tayi komai hakan yasa Najwan ta sanar da Binafa, sai Binafa tace kar ta damu akwai wani hanyar da zasu bi koda basu yi nasarar tada mata sha'awa ba, to akwai maganin da zasu bawa Jamila ta tabbatar ana gobe mijin zai dawo ta saka mata a abinci ko abin sha, abin maye ne mai zautar da mutum kuma baya saka barci sai dai mutum ya jishi a rikice kuma ba cikakken ƙarfi saboda yana kashe jiki, hakan yasa Najwa ta samu natsuwa tace zata haɗasu da Jamila wanda hakan ne ya faru a zuwan su yau gidan, kuma Jamila ta tabbatar musu da Aminu gobe Asabar zai dawo, saboda a gabanta Sameeha tayi waya dashi har tana tambayarsa abin da yake so a dafa masa saboda yace da sassafe zai fito dan zai je Kano akwai wani meeting da zasuyi mai muhimmanci, to zai biyo ta gida kafin ya wuce ta shirya tare zasu je, Jamila sai ta tsinci kanta cikin zullumi wanda yasa ta kasa zama a ɗakinta ta dawo falo ta zauna cike da tunani barkatai, wanda maganin da suka bata akan lallai ta saka wa Sameeha a abinci ko abin sha ya tsaya mata a zuciya, haka dai ta danne komai dan dole ta ƙarasa aikin da ta yi alkawari akai, kuma hange dubu goman yasa ta ƙara aro jarumta.

Sameeha sai bayan sallar magrib suka baro gidan kakanninsu a motarta ta kwaso su, sai da ta wuce gidan umma ta sauke su har da yaranta kafin ta juya akalar motarta ta dawo gida, bayan ta shiga falo ta samu Jamila a nan falo da ta samu a buɗe, da yake in tasan ta kusa dawowa takan buɗe ƙofar, ta kalleta da kyau.

Yau kuma me kike yi a falon ke kadai? kuma baki saka kayan kallo ba.

Zaman É—akin ne ya isheni shiyasa na dawo nan, kuma ina tsoron na kunna kayan kallo ki gani kiyi faÉ—a.

Babu faɗan da zan yi miki in dai ba zaki yi mini ɓarna ba, tashi kije ki yanka mini tattasai da albasa, ki ɗauki kaza ɗaya dake fridge ki tafasa mini, gani nan zan zo na dafa mana taliya shap shap.

To tace mata kana ta miƙe ta wuce kitchen Sameeha kuwa ɗaki ta shiga ta rage kayan jikinta ta fara gabatar da sallar magrib kafin ta fito daga ita sai vest da siket ta shiga kitchen ta samu ta yi mata duk abinda tace, sai da naman ya tafasa kafin ta daura mai ta soya su kafin ruwan tafashen ta ɗaura musu sanwar taliyar, bayan ta gama tace wa Jamila ta kula da girkin zata je tayi sallar isha'i da aka kira dan har an shiga masallaci an tayar da sallar, Jamila ta ce to, kamar tana jira ta fito ta ciro kwalbar maganin da suka bata ta zuba shi duka a cikin sanwar taliyar ta saka dulayi ta motsa kana ta rufe ta ɗaure kwalbar a cikin baƙar leda ta fito ta shiga ɗakinta da sauri, ta samesu a zaune ko wacce da waya tana charting, ta miƙa musu ledan data ɗaure kwalbar tana cewa.

Na zuba shi duka a cikin sanwar Taliyar data É—aura yanzu.

Aikinki na kyau 'yan mata, dan har na ƙara miki dubu biyar akan cikon dubu gomanki.

Cewar Binafa da take magana a hankali tana yi mata jinjina da babban yatsa, Jamila murmushi tayi ta juya da sauri ta fita zuwa kitchen.

.
Aminu.

Wajen ƙarfe shida kira na gaggawa ya shigo wayarsa akan meeting ɗinsu da za ayi a gobe asabar ƙarfe biyun rana an dawo da shi ƙarfe tara na safe bisa wani babban dalili, hakan yasa ba shiri ya taso driver sun wajen aikinsu ya bashi motarsa yace su kamo hanyar kaduna, daga shi sai briefcase ɗinsa sai wayoyinsa guda biyu, bai sanar da kowa zai zo ba hatta Sameeha bai faɗa mata ba, dan ya san in ta sani zata hana shi zuwa saboda halin da ƙasar yake ciki na rashin tsaro musamman a arewacin Nigeria, sannan kidnapers sun yi wa hanyar Abuja baƙin fanti wanda kowa yasan ba ƙaramin ta'asa suke yiba sai dai Allah yayi mana maganinsu, hakan yasa bai faɗa mata ba dan ya zame mata zuwan ba zata.

Sameeha da ta idar da sallah sai ta ce bari ta kira Aminu taji muryansa, koda ta kira ya É—auka amma bata jinsa saboda rashin network hakan yasa ta kashe kiran sai ga text É—insa ya shigo.

_Meehata karki damu zan kira ki anjima kaÉ—an._

Murmushi tayi ta aje wayar ta fito zuwa kitchen lokacin har ta sauya kayan barci dan so take tana cin abinci ta yi barci, dan gobe In Allah ya kaimu ta tashi da ƙarfinta saboda zuwa kano da za suyi, ɗoki take sosai dan rabonta da kano ta manta akwai ƙawayenta na WhatsApp group Sirrin 'ya mace da yawa a can da suka yi mugun sabo, ana zumunci da kuma abubuwan ƙaruwa da ake gudanarwa, sosai take ƙara samun ilimin rayuwa a wannan group ɗin, komai a tsari suke yinsa kamar yadda musulunci ya tanadar, sun zama tamkar 'yan uwa, hakan yasa ta fara lissafin inda zata je kai ziyara dan har ta yi magana da mata kusan uku ta pc akan in ta shigo zasu ganta. Ta samu Jamila a kitchen tana zaune.

Kin duba taliyar tayi kuwa.?

Ruwa ya rage ya tsotse.

Sameeha tace ok sai ta isa tukunyar ta buÉ—e taga tayi tace.

Ai ni haka nake sonta nasha da romo romo tafi mini daÉ—i, É—auko plate na saka miki nima ma saka nawa.

To Jamila tace ta dauko plate biyu ta bata, Sameeha ta amsa ta kashe gas ta soma zubawa Jamila ta saka mata yankan naman kaza ɗaya tace ta sallameta, kana ta zuba nata, saboda ta ƙosa ta ci a kitchen ɗin ta zauna tayi masa cin tsaf, sai da ta cika cikinta sosai kafin ta gama ta aje plate ɗin ta sha fanta da ruwa ta fito tana jin jikinta ya fara yi mata nauyi, zarginta barcin da take ji ne ya fara kawo jiki, taso ta zauna a falo abincin data ci tabi jikinta kafin ta kwanta, amma ina idanunta sunƙi bata haɗin kai sai ta wuce ta shiga ɗaki ta kwanta, dan har ji tayi ɗakin yana juya mata, sosai ta shiga mamakin yadda jikinta yayi sanyi kalau kamar dai ana jira taci abinci ne ganiyar data kwaso ya rufeta.

Nan muka kawo ƙarshen season 1 wato ƙarshen freepages..

Ko me zai faru? Ga Aminu yana hanyar dawo wa dan yana gabda shigowa gida...

Sameeha taci magani a cikin abincinta bata sani ba ta soma shiga wani yanayi na maye...

Binafa da Hanan suna cikin gidan wanda gabaÉ—aya shirinsu na safiyar asabar ne, sai kuma ga kuma Aminu yana hanyar dawowa. Me zai faru?

Shin burin Najwa yana cika? Ya ƙarshen ta zai zama?

Su Binafa suna cin sanara akan Sameeha kuwa?

Ya bikin Salma sai kazance da Su Hauwa suka ci burinsa.?

Burin Hauwa yana cika kuwa akan aurawa Aminu Najwa da kuma sakin Sameeha da take so yayi.?

Ya ko wanne yake karɓan sakamakon karshensa.? Sai mu tara a cigaban wannan labarin don samunsa kai tsaye har zuwa ƙarshe In Sha Allah.

_Bononza na kwana biyar akan N300 idan kwanaki biyar ya ƙare In Sha Allah zai koma asalin kuɗinsa N400, yau saura kwana biyu bononza ya ƙare._

Pay N300 to 0106956864
Ramatu Muhammad Kabir
Access bank (Diamond). Ko a tura MTN card N300 a 09034940106, masu so ta pc su tura N600. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.
[2/18, 3:35 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

18.

Jamila.

Data shiga É—akinta da plate É—in abincin da Sameeha ta zuba mata sai ta cewa su Binafa.

Kunga ta zuba mini abincin kuma da maganin da na zuba mata a ciki.

Ki samu leda baƙa ki saka a bola, idan maganin ya fara aiki a jikinta ko ɗaga ƙafa ba zata iya ba dan haka ki shiga kitchen ɗin ki dafa mana indomie muma za muci.
Chapter 25 · 0% Book details