← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 103

Sashe 6

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cewar Ikram, Najwa tace Ameen wa iyyaki tana kalkale dariya, motsa kofa da suka ji ne yasa suka mayar da hankalinsu ganin waye zai shigo, sai ga Aminu ya bayyana cikin tsadadden shadda da hula akansa yayi matukar kyau, wani irin sumar wucin gadi Najwa tayi numfashinta har ɗaukewa yayi ya dawo, nan take taji kirjinta yana wani bugawa da sauri da sauri ga kanta daya yi mata wani girr, tunda take bata taɓa ganin Namiji daya tafi da imaninta lokaci ɗaya ba kamar wannan da ya shigo, ana cewa so farad ɗaya a ganin farko to tabbas ta tabbatar da hakan yana faruwa dan kuwa nan da nan ta faɗa cikin wani kogon bege da mafarkin samunsa a matsayin miji, sai dai kalmar data ji yaran suna Abba oyoyo yasa ta farka daga kogon tunanin data faɗa ta tsaya sororo tana kallon ikon Allah jiki a matuƙar sanyaye.

Abban Amrah ashe baka yi nisa ba na É—auka ba yanzu zan ganka ba.

In koma kenan bakya buƙatar ganina a yanzu.

Ni É—in banza na nace ka koma.

Cewar Sameeha tana dungurin kanta, suka saka dariya ya karaso falon ya zauna a cushing yana cewa.

Kewarku yasa na taho yanzu dan wlh jiya nayi kwanan kaÉ—aici, gashi gobe da sassafe zan wuce Abuja ana nima na.

Wayyo daga dawowarmu ko hutawa baka yi ba, ni dai ina burin naga ranar da zaka aje aikin nan ka dawo ka zauna guri guda.

To ya za ayi Meeha ai duk wanda ya tara iyali dole ne ya fita nima.

Ina kwana yaya.

Lafiya lau Alhamdulillahi Ikram ya karatu ana ta taɓawa.

Ikram ta amsa da lafiya lau kama ta wuce kitchen dan É—aura girkin da Sameeha ta sakata, sai a lokacin ne Najwa ta sauke raunannen ajiyar zujiya ta ce.

Ina kwana.

Lafiya lau ya amsa sai ya miƙe yana duban Sameeha.

Baƙuwa muka yi ne?

Eh É—iyar Gaggo Zulai ce wanda nake faÉ—a maka ita kenan mata 'ya mace. Ai in gaya maka ma haÉ—in gida za muyi musu Zaidunmu ne zai aureta.

Kai masha Allah Allah ya sanya alkhairi yasa ayi damu, idan kin gama basu aikin ki zo ki tayani shirya kaya dan ina ganin sati biyu zuwa uku zanyi a Abujan nan dan wlh akwai ayyyuka rututu da suke niman shan kaina.

Wayyo ni Sameeha har sati Uku, ina tunanin sati guda zakai ka dawo gaskiya bazan yarda ba.

Ta faɗa tana fuskar shagwaba, Aminu yayi dariya ya wuce zuwa falonsa Sameeha ta bi shi tana yi mishi mitar kwanakin sunyi yawa, Najwa da kamar an daskarata a gurin ta bisu da ido tana jin wani irin damuwa da kuma haushin Sameeha daya ɗarsu mata a zuciya nan take, sosai taji haushin faɗa masa da tayi wai zata auri Zaidu, sai ta koma cushing ta zauna tana sauke ajiyar zuciya dan har ga Allah tunda take bata taɓa jin yanayi irin wannan ba akan wani ɗa namiji ba sai akan Aminu, wanda har numfashinta da zafi yake fita, jikinta ya ɗauki ɗumi da shiga tashin gankali, ga koshi ga kwanan yunwa ita taga samu taga rashi, dan tasan ko mutuwa zata yi Mijin Sameeha ya haramta a gareta dan tasan babu ta yadda zata yi ta mallakeshi a matsayin miji, dole ne ta lallashi zuciyarta ta samawa kanta lafiya, sai ta miƙe tana kokarin yaƙi da shaiɗan ta wuce kitchen wajen Ikram.

Sallamar Hauwa yasa Sameeha fitowa daga falon Aminu, cikin sakin fuska ta ƙarasa falon tana yi mata sannu da zuwa ta nuna mata gurin zama, Hauwa ta zauna suka shiga gaisawa sai bayan sun nisa ne Hauwa tace.

Ina Aminu ko yana babban gida ne?

Yana ciki yana haÉ—a kaya gobe zai tafi Abuja.

Ohh aikin kenan ba zama, dama nazo gurinki ne mu tattauna.

Ina jinki yaya Hauwa amma kafin nan bari na kawo miki abin motsa baki.

A'a yi zamanki ba na bukatar komai dan a koshe nake.

Sameeha ta koma ta zauna dan harta miƙe, Hauwa ta cigaba da cewa.

Dama na zo ina yi miki tunin abinda kika sani ne, akan sanin Aminu ɗan dangi ne, kuma rashin zamanku a nan kaduna yasa duk ba ayi saboda dake ba, dan haka ina so ki saki jikinki da mutane, ki shiga cikinmu a dama zumunci dake dan in kika ce zaki ware kanki wlh ba zaki ji daɗin mu'amala damu ba, dan na kula baki son mutane bakya so a raɓeki.

Hmmm yanzu Yaya Hauwa maganar kenan da ya kawo ki.

Eh itace ta kawo ni sannan in sanar dake gobe zan aiko miki da 'yar aiki wacce Laure ta samo miki, dan wannan gidan naki saida me tayaki aiki in ba haka ba kar ki zo ki fara tara datti gida ya lalace.

To ni nace muku ina buƙatar 'yar aiki ce? Sannan ma in zan nima 'yar aiki dole sai ku ne zaku kawo mini? wannan wani irin son kai ne da shiga hurumin da ba naku ba, to ki koma ki faɗawa Lauren bana son 'yar aikin dan baku isa ku ce zaku yi iko da abinda yake matsayin ikona ba.

Rashin kunya zaki mini Sameeha.

Hauwa ta faɗa da ƙarfi tana dukan kirjinta, Sameeha ta kalleta da kyau.

Idan haka kika ɗauka to shi na miki, wlh baku isa ku juyani ni da gidana ba ko wacce taje taji da matsalar gabanta, haba ni kaɗai ce wacce take auren ɗan uwanku da zaku sakani a gaba, tun ina Lagos baku barni da ƙananun munfurcinku ba gashi na dawo nan zaku dasa miki iko to wlh uban kuturu yayi kaɗan.

Ke Sameeha yaya Hauwan kike faÉ—awa haka?

Cewar Aminu daya fito falon wanda yayi daidai da lokacin da Sameeha take faÉ—a mata magana, sai Yaya Hauwa ta fashe da kukan munafurci tana faÉ—in.

Ni zaki zaga kici mituncina daga gyara ka yanka to ai bazai zama sauke mu raba ba.

Ta miƙe a fusace tana goge hawaye zata wuce Aminu ya dakatar da ita.

Dan Allah yaya Hauwa ki tsaya. Ke Sameeha ki bata hakuri ko na sassaɓa miki, baki isa ki wulaƙanta mini 'yar uwa ba kinyi kadan wlh, nace ki bata haƙuri!

Ya faɗa a tsawace, Sameeha da hawaye ya cika mata ido dan wlh Abin da ciwo matuƙa azo har gidanka anima takaka sannan ace ka bayar da haƙuri, tace cikin damuwa.

Kiyi haƙuri hakan ba zai sake faruwa ba In Sha Allah.

Ba shakka Sameeha daga abin arziki kin mayar da shi abin tsiya, ai wlh kinyi da 'yar halak dan zan baki mamaki, ba zan sake kawo miki magana irin wannan ba kuma zanje in isar da sakonki ga Laure cewar kince baki son 'yar aikin da ta samo miki.

A'a yaya Hauwa dan Allah kiyi haƙuri kuma na amince a kawo mana 'yar aikin, Sameeha ki kaɓeta tunda sunyi ne dan su kyautata miki, kuma dama dole zaki samu mai taya ki aiki ga kuma zaman gidan zai miki ba daɗi ke kaɗai in yasa sun tafi makaranta.

To Abban Amrah Allah ya kawota da alkhairi.

Daga haka ta juya tana share hawayen daya zubo mata a kuncinta ta shige ɗaki, Su Najwa kuwa da suka fito suka tsaya a kofar kitchen komai ya faru akan idonsu, dan haka suna ganin Sameeha ta shige ɗaki sai suka koma ciki, Ikram tana ƙananun surutai akan abinda Hauwa ta yiwa 'yar uwarta, Najwa dai tsaki take ta ja dan damuwarta daban ba wannan ne a gabanta ba, dan yadda ta ƙara tozali da Aminu wutar soyayyarsa ƙara ruruwa ta yi a zuciyarta.

Cakwakiya! To muje zuwa...

Ummu Sultan da Samha ce
[1/30, 8:49 PM] Rahma Kabir: *ABIN DA CIWO*

Na
©Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 5.

Aminu har gate ya raka Hauwa kafin ya dawo ya shiga É—akin Sameeha ya sameta a kwance tana kuka ya isa da sauri ya É—agota ya rungume yana cewa.

Dan Allah kiyi haƙuri Meeha wlh nasan ba kida laifi saboda nasan halin Hauwa, kawai bana so na goyi bayanki ne ta ce mun yi mata rashin mutunci taje tana yaɗawa 'yan uwa, sannan a kullun ina baki shawara ki daina biye musu duk abinda zasu yi miki, nasan wlh haushi kawai suke yi da ni'imar da kike ciki dan banga abinda kika taɓa yi musu ba.

Amma kasan abin da ciwo su tasani a gaba ni banyi musu komai ba, ƙiri ƙiri ni da gidana sai wasu ne zasu yi iko da shi ni ban isa inyi abinda nake so ba.

Ni dai ina ƙara baki haƙuri ki dai na wannan kukan komai zai wuce da yardan Allah, kuma in zamanki a nan zai zama damuwa ina ga zan sama mana wurin zama mai kyau a Abuja mu koma can gabaɗaya kinga ba mai saka miki ido ko takura.

Ni dai nafi son nan, sai dai mu riƙa zuwa maka hutu.

To ai shikenan kukan ya isa haka, tashi muje mu karasa haÉ—a kayan kin san da wuri zan fita, ina son komai ya kasance a haÉ—e guri guda kar sai na tafi na tuna da ban saka wani abu a jaka ba.

To tace masa ya kama mata hannu suka fito zuwa É—akinsa. Sai yamma lis Najwa ta wuce gida bayan Sameeha ta cikata da kayan arziki ta kaiwa inna sannan da sakon gaisuwa kuma ta bata kuÉ—in mota ta tafi, Ikram har titi ta rakata ta samu abin hawa suka wuce. Ita dai Najwa duk wannan mutunci da suka yi mata bai burgeta ba dan sosai zuciyarta take hasko mata dama ita ce ta dace da wannan gidan, gani take yi a komai tafi Sameeha wato kyau, fari da yarinta, duk da Sameeha itama ba baya ba wajen kyau ga diri da cikar zati, fara ce amma ba can ba kuma tana da idanu dan kallo É—aya za ayi mata a gane anyi mace a gurin, itace ta biyo Umma sak haske kawai Umma ta fita, Ikram tafi kama da su Anwar saboda babansu suka biyo, ana ganinsu anga kanuri ga hanci zar har baka duk da suna da duhu amma suma suna da nasu kyan, Ita Sameeha haÉ—a kyau biyu tayi saboda wushiryar baba ta gada da kuma dimple.
Chapter 6 · 0% Book details