← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 103

Sashe 7

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Najwa da tunani barkatai ta isa gida wanda gabaÉ—aya tunanin yadda zata zama matar Aminu take yi, sai dai har ta cimma gida bata samu matsayar shawara ba, dan ta hango babu wata hanya da zata samu haka sai dai ta lallashi kanta ta yakiceshi a rai. Yadda inna ta ganta sukuku yasa tace.

Lafiya na ganni sai kace wacce akayi wa duka ko duk gajiyar aikin ne.?

Inna kaina ke min ciwo kuma ba wani aikin wahala nayi ba kawai dai zuciyata take raya mini wani abun da ko mutuwa zanyi ba zan sameshi ba.

Uuu hum cutar kuÉ—in ne ya kamaki ko me?

Inna wlh gidan anty Sameeha shine mafarkina, shine burin dana daɗe ina saƙawa, wlh hango kaina kawai nake ace nine mamallakin wannan gidan, kuma Inna ashe haka mijinta ya haɗu kin san dama ban taɓa ganinsa ba, wlh yayi matuƙar kwanta mini a rai, zuciyata idan ba karya take yi mini ba na kamu da son sa.

Tas taji inna ta É—auke ta da kyakkyawar mari tana waro ido waje cike da takaicin abinda Najwan take faÉ—a.

Dan ubanki kin fara hauka ne, kina da hanki kuwa Najwa? kin san me kike faÉ—a?.

Wlh inna ina cikin hankalina kawai dai zuciyata ta kamu da son abinda ta san ba zata samu ba. Inna ina jin wani irin sabon yanayi a ƙirjina wanda ban taɓa jin irinsa ba akan wani namiji ba, ki taɓa zuciyata kiji yadda take buga mini wlh bani da lafiya.

Najwa tayi maganar tana kuka da taɓa gefen zuciyarta, inna sakin baki tayi tana kallonta cike da tsantsar mamakinta.

Gaskiya ne Najwa wlh ba ki da lafiya dan da alama kwakwalwarki ta taɓu. To wlh ki sakawa ranki har gaban abada ba zaki taɓa samunsa ba dan ya haramta a gareki, ko kin mance Babansu Sameeha shine ya saki nono na kama uwa ɗaya uba ɗaya nake da shi, dan haka kar naji kin bawa wani labarin wannan shashancin naki.

Nima inna nasan dole ana barin halak dan kunya, In Sha Allah ba zaki sake jin wannan maganar ba.

Tana gama faɗar haka ta miƙe ta shige ɗakinta ba dan ta hakura ba sai dan rashin samun goyon bayan inna yasa ta faɗa mata haka, sai dai wani ɓangare na zuciyata yana sanar da ita ta haƙura shine mafita amma wani sashi kuma yana ƙara hasko mata daular gidan Sameeha da kuma kyawun Aminu daya firgita zuciyarta lokaci guda ya sakata cikin wani yanayin da ba zata iya misaltashi ba. A wannan ranar barci ɓarawo ne ya sace Najwa dan harga Allah tunani yaƙi barin zuciyarta, ɗan barcin da ta samu ma cike yake da hargitsin mafarkin gidan Sameeha da kuma Aminu.

Gari da ya waye Najwa ta tashi wasai tamkar wani abu bai damunta, ta koma walwalarta dan sosai take son nunawa Inna tabar maganar Aminu, amma kuma ta gama yanke shawarar zuwa gidan ƙawarta Nafeesa ta bata shawara akan ƙudurinta. Abokiyar cin mushenta ce duk wani abu na sirri wa junansu suke tattaunawa, Nafeesa wayayyar 'yar boko ce dan ta samu yin Diploma a masscom, da ta gama ne ta shiga makarantar hadda suka haɗu da Najwa wanda tasu ta zo ɗaya kuma iyayenta suna da rufin asiri, a sanadin haɗuwarsu ne Najwa take ɗan sanin abubuwan more rayuwa har take kokarin kwaikwayanta, yanayin shiga ne kaɗai bata yarda ta sauya ba, dan Nafeesa tayi tayi ta koya mata saka gyale amma Najwa bata yarda ba, sai dai a fagen burin auren mai kuɗi halinsu guda amma ita Nafeeaa ba tada kwaɗayi tunda ta taso cikin jin daɗi. Najwa da ta gama aikinta ta shiga ɗakin inna ta gaida baba ta tambaye shi zata gidan ƙawarta Nafeesa amso assignment da aka bayar jiya Lahadi da bata samu zuwa Hadda ba, Baba yace to kana ya bata ɗari biyu na mota ta amsa tana godiya sai ta fito, sai inna ta biyo bayanta tana cewa.

Da fatan maganar da kika yi mini jiya kin barta har abada dan bana so ki sanar da wani.

Haba inna ai tuni na ƙaryata zuciyata na mance komai, kuma In Sha Allah ba zaki sake jin magana irin wannan ba.

Yauwa Auta Allah ya miki albarka, ina ganin zan yiwa Babanku magana akan Zaidu ya turo a yi maganar aurenku kawai a huta.

Inna ai na taɓa yin magana da Zaidu yace a bashi lokaci, kin san yanzu ne yake kan buɗe shagonsa.

Hakane fa to Allah yasa jinkirin ya zama alkhairi, ki dawo da wuri karki daÉ—e dan zan je barka a can unguwarmu kawo anjima.

To ta ce mata ta wuce zuwa gidan su Nafeesa dake malali. Wajen ƙarfe goma ta isa ta buga gate aka buɗe mata ta shiga, a farfajiyar gidan ta samu Nafeesa tana buga kwallo, tana ganin Najwa ta taho gareta da sauri tana yi mata oyoyo, Najwa tayi dariya tana cewa.

Yaushe zaki girma ne Nafeesa da kike buga kallo sai kace wata yarinya.

Wlh exercise nake yi kin san sai ana yi ana motsa jiki, ya jiya ban ganki ba a makaranta kuma na kira wayarki bata shiga.

A gida na barta saboda naje gidan cursin sister É—ita da suka dawo gada Lagos.

Ayya ko wannan antynki da kike faɗa mini ƙanwar Zaidu.

Eh ita fa yanzu ma akanta na zo ki ba ni shawara.

Nafeesa ta ce to kana ta kama hannun Najwa suka shiga cikin gida har zuwa falonsu, basu samu kowa a ciki ba dan haka ta jata zuwa É—akinta, bayan sun zauna a kan gado Nafeesa tace.

Kawata naga damuwa a fuskarki, ki bani labari ko wulaƙanci tayi miki ne dan naji kin ce suna da kuɗi ko.

Eh, ai da wulaƙanci kaɗai tayi mini wlh dana ji daɗi, na faɗa so ne, ina nufin soyayyar mijinta.

Nan Najwa ta kwashe labarin komai ta faÉ—a mata har da yadda suka yi da inna.

Kut amma wlh kin ɗibo da zafi, zuciyarki bata faɗa miki gaskiya ba Najwa. Mijin ƙanwar Zaidunki fa kike so.

Nafisa ta faɗa tana riƙe haɓa, Idon Najwa yayi rau-rau kamar zata yi kuka.

Ya zanyi Feena a ganin farko na kamu da sonsa, ya haÉ—a duk wani abu da nake mafarkin samu a gurin namijin da nake so, ga kyau ka kuÉ—i ga asali komai ya haÉ—a, irin dai mazan nan da ake kira first class wanda ake kwatance a cikin labaren littafan hausa.

Ke ki faÉ—a mini a takaice mijin novel.

Cewar Nafeesa tana 'yar dariya. Najwa ta dafa hannunta tana cewa.

Yauwa shi fa. Ki gaya min yadda zanyi dan na faɗawa inna na bar maganar, amma har ga Allah ban haƙura ba ina son samunta ko ta halin ƙaƙa tunda ba haramci in ya aureni.

To ke meya kai ki faɗawa inna, kin san ko mutuwa zaki yi ba zata taɓa yarda ba saboda kar zumuncinsu ya lalace, amma ni tambaya ɗaya zan miki, dagaske kina son aurensa ko so kike kawai ki dan taɓa soyayya da shi kici kuɗinsa.?

Soyayyar aure nake masa, gidan da Anty Sameeha take ciki irinsa nake son gani kaina a ciki, dan gaskiya burina kenan.

To ki saka aranki kamar kin samu, amma dole sai mun kauce hanya fa.

A'a Feena wlh ba zan bi malamai akan wannan ba, idana imani da kuma tsoron Allah, duk da ina da shagala amma ba zan yi shirka ba.

Nafeesa ta kwashe da dariya tana tafa hannu sai da tayi mai isarta kafin tace.

Na manta fa ashe da mahaddaciya nake magana, to nima ba wannan nake nufi ba, tunanina in har kina so ki zama matarsa to dole sai Anty Sameeha ta bar gidan.

To ta ya hakan zai faru?

Ba kin ce basa shiri da 'yan uwansa ba, to ta hannunsu zaki fara bi wato ki haÉ—a kai ya yayarsa Hauwa kika ce ma sunanta ko?

Eh.

To hakan shine zai fara baki Ƙofar fara samun shiga gidan Aminu.

Najwa tayi shuru tana tunani, can ta nisa tana cewa.

To ta ya zan haÉ—a kai dasu?

Shiga cikinsu za kiyi ki tayasu kushe Sameeha da nuna kyamar abinda take yi musu, da karin sharri ke duk ki haÉ—a ki faÉ—a in dai zai sa ki samu shiga a gunsu.

Anya zan iya kuwa? Anty Sameeha bata taɓa yi mini wani abu ba wlh.

To zauna karki yi sai ki fasa cikar burin naki. Kije kiyi tunani sauran plan É—inmu zan kara nazari akansa.

Haka Nafeesa ta dinga iza Najwa tare da hasko mata in har tana son samun cikar burinta to sai tabi shawarar da ta bata.

***

Sameeha.

Aminu da wuri ya tafi dan jirgin ƙasa ma yabi, kafin ya tafi saida ya gabatarwa Sameeha da sabon driver Mai suna Hamza da zai riƙa kaisu anguwa ko kai yara makaranta da aike kasuwa, duk da yace sai in ya dawo zai yiwa su Abi register makaranta, wajen ƙarfe tara da rabi na safe sai ga Hauwa ta zo da mai aiki suka gaisa kamar komai bai faru jiya ba sai ta ɗaura da cewa.

Sameeha ga mai aikin nan sunanta Jamila, sai ki bata ɗakin da zata zauna dan na kwana ne saboda daga ƙauye aka ɗaukota.

To shikenan an gode,

Abin da Sameeha tace kenan dan bata so tayi magana mai tsayi ya jawo rikici, sai Hauwa tace.

Ya batun walimar da zaku yi? Ko kun fasa saboda Aminu baya nan.

Bamu fasa ba za ayi asabar mai zuwa In Sha Allah dan mun gama tsara komai.

To madallah, in akwai taimakon da kike buƙata sai kiyi magana tunda taro ne na mutane da yawa yana buƙatar shawara.

Idan da yuwuwar hakan zan kiraki In Sha Allah.

Daga haka Hauwa ta miƙe tayi mata sallama ta wuce, Sameeha sai da ta tabbatar da ta tafi kafin ta ƙarewa mai aikin kallo, yarinya ce da ba zata wuce shekara sha biyar ba zuwa sha shida, duk da ƙauyenci ya nuna a tare da ita amma a feƙe take, Sameeha ta gyara zama tana cewa.
Chapter 7 · 0% Book details