← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 103

Sashe 92

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suka cigaba da shirin biki musamman Mujaheed daya ɗauko gyaran gida, dan so yake ko ya ya ne ya burge Najwa duk da yasan ba irin gidan yake cewa zai kaita ba, amma kuma yasan da ƙaryar ne kaɗai zai samu zuciyarta kamar yadda yake hasashe, kuma faɗuwa tazo dai dai da zama dan irin haka Najwa take so, dan da ace yazo mata a yadda yake baida komai to kallo ma bai ishe ta ba. Wannan lokacin Mujaheed ya rage zuwa zance saboda yana so yayi komai cikin lokaci, haka yaje ya zauna gaban Hajiya ya zayyano mata auren da zai ƙara da dalilinsa na ƙarawan, itama ta goyi bayan ya ƙara dan zama da mace ƙazamiya sai haƙuri nan ta ce zata sanar da Alhaji duk abinda ya bayar zata bashi. Haka kuwa aka yi ta sanar da Alhaji ya bashi gudun mawar dubu ɗari biyu, Hajiya ta bashi dubu hamsin, yaran gidan kuma daga mai dubu goma, ashirin, talatin ya haɗa kuɗi ya kai dubu ɗari huɗu da wani abu hakan yasa ya ƙara samun kuɗin haɗa akwati, dama yaje Gombe ya sayar da gonar babansu wanda ya kawo aka cirewa ƙannensa dana mamansu nashi ne ya soma gyaran gida, Mama ma ta ƙara masa da nata akan ya ƙara ga kuma tallafi daya samu gurin 'yan uwan baba da mama duk ya haɗa Allah ya rufa masa asiri ya rufu. Da kyar ya haɗa akwati biyu da kit ya cika su da kaya dai dai ƙarfinsa ya adana a ɗakin mama, yace amarya tace su danginsu ba a kai akwati sai dai yarinya ta gani a ɗakinta, mama ta yaba da aladarsu tace hakan ma shine dai dai. Ita kuma Najwa ce mata yayi su family ɗinsu ba a kai akwati sai an kai amarya ta gani a ɗakinta bayan kwana biyu, saboda kar a yi ɓarna a cikin akwatin dan kaya ne masu yawa sosai. Najwa ta yarda ta kuma ji daɗi dan har take tuna labarin da Nafeesa ta bata na ganin akwati a ranar da aka kaita kuma kaya sosai ya zuba, hakan yasa tace kaya ne ma da yawa ƙila bazai ɗauki gidansu ba tunda tasan Mujaheed masu mugun kuɗi ne. Haka dai akaita shirin biki inna duk ta sanar da dangi, wannan karan ma umma da ita ake yin komai, hatta lokacin da za a kai kayan ɗakin Najwa ango yace a badasu kawai suna da masu yin gyara kamar na farko dai, umma tace wa inna gwara dai aje a gani dan kar a ƙara yin irin na farko, Najwa fa ta dage akan kar aje, gwara ayi yadda ango yace bata son a samu matsala, to tunda uwar gayya tace ga yadda take so hakan aka yi mata aka bar zuwa, ita kuma a ganinta kar aje ayi mata sata ne dan yadda yake faɗar gidanta wane nasu Sameeha, tafi son kowa yaje a ranar da za a kaita dan asha mamaki da ganin suturar da Allah yayi mata, ƙannen Mujaheed sune suka yi gyaran ɗakin Najwa suka jera komai a muhallinsa, kayan ma sunyi yawa dan ɗakin ya cike, dole wasu sai da suka zuba su a extra ɗakin dake kusa da nata.

Ana gobe biki umma ta matsawa su Sameeha akan lallai sai ta zo dan tana so su nuna komai ya wuce tunda Najwa wani zata aura ba Aminu ba, Ikram dai lafewa tayi akan ba tada lafiya, Sameeha kuwa Ibrahim ne ya tasota a gaba saboda cika umarnin umma, a ranar suka zo garin ya barta a gida. Washe gari da wuri suka tafi gidan inna ita da umma, nan fa kowa yayi mamakin ganin Sameeha ita da aka yiwa cin amana amma ta dage ta zo, umma ta nuna zumunci ya fi ƙarfin komai sannan su komai ya wuce. A tsakanin Najwa da Sameeha sai dai suka yi kallon kallo amma ba wanda ya yiwa ɗan uwansa magana dan Sameeha tace in dai Najwa tayi mata magana zata kulata amma in taba yi ba zata saka mata ido, albarkacin inna kawai taci tazo bikin bisa matsawar umma, dan Abin da ciwo in ta tuna abinda tayi musu kawai dai taci darajar iyaye ne. Najwa dai sai rawar kai da take zubawa domin duk kayan akwatinta na Aminu su ta dinga sakawa tunda babu abinda aka cire mata a ciki komai yana nan a sabo, hakan yasa ta samu damar ɗaga kai domin tasan kayan da zata samu sunfi waɗan nan, shiyasa ma bata damu a kawo na akwatinta ba tunda tana da waɗannan. Bayan an idar da sallar azahar aka ɗaura auren Najwa da Mujaheed bisa sadaki dubu ɗari biyu, wanda ɗumbin mutane sun shaida, Najwa an kuma ɗaura aurenta a karo na biyu. Yaran 'yan uwa sune ƙawayenta bata gayyaci kowa ba dan tai ta niman Nafeesa a waya baya shiga daga ƙarshe ta gane ko ta sauya layi ko kuma tayi blocking ɗinta, hakan bai wani dameta ba domin tasan ta samu mijin nunawa sa'a, a hankali zata samu sabbin ƙawaye masu aji da kuɗi ba irin Nafeesa ba, haka suka dinga ɗaukar hotuna ba laifi biki yayi armashi ba irin wancen na farko ba.

**
Bayan sallar magrib aka zo da motocin ɗaukar amarya masu yawa, ciki har da Hajiya dan ita Mujaheed ya wakilta a ɗauko masa amarya tsabar yana girmamata, kuma yayi hakan ne dan kankarowa kansa mutunci mutane su gane shi ɗin wani ne, Hajiya da farko kamar ba zata je ba Alhaji ne ya ƙarfafa mata guiwa akan yadda Mujaheed ɗin ya ɗaukesu da muhimmanci, shiyasa tazo a motarta cikin shiga ta alfarma tare da ɗiyarta wacce take zawarci a gida, itace sawun gaba wajen karɓan amarya dan 'yan uwansa sai dai suka koma gefe, a motar Hajiya aka saka Najwa sai 'yan uwa mata biyu suka shiga baya suka sanya Najwa a tsakiya Hajiya da 'yarta suna gaba. Mujaheed ba ƙaramin gayyar abokai yayi ba kuma sunyi masa kara a gurin ɗaukar amarya, nan fa aka kwashi amarya da tawagarta zuwa gidan Mujaheed. Sameeha bata so zuwa ba amma umma tace dole sai sun je daga can sai su wuce gida dan a motarta suka je bikin saboda driver ya ɗauko motar a gidanta ya kawo mata, hakan yasa ta dauki umma da wasu 'yan uwansu a motarta sai tabi bayan 'yan ɗaukar amarya suka nufi gidan Najwa dake unguwar Abakwa.
[5/16, 8:24 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

55.

Motocin ɗaukar amarya ne suka yi jerin gwano akan babban titi, da yake dare ne ababan hawa sunyi ƙaranci aka hanya, tafiya suke a tsane ba hayaniya ko hargowar 'yan ɗaukar amarya, a haka har suka isa hanyar da zasu yi ratse su shiga Abakwa, Hajiya dake tuƙi ta kalli 'yarta kana ta mayar da kallonta hanya tana cewa.

Daɗina da unguwannin nan ba su da kyawun hanya, ga babu wadataccen titi a cushe yake, in ba dalili ba babu abin da zaisa na shigo hanyar nan in gwaggwaɓe motata.

Sai haƙuri kam kuma Mujaheed namu ne dole muyi masa kara, ina ganin ma in mun shiga unguwar dole sai dai mu fito ta ribas dan babu wadataccen wajen da za a juya mota. Sai dai in kin fito ki wuce mu bi ta junction ɗin unguwar shanu mu fita babbar titi ba dole sai mun koma ta nan ba.

Dole haka zanyi dan kwanaki dana zo barkan matarsa ta haka ya mayar dani gida.

Cewar Hajiya, Najwa dake cikin mayafi ta riƙa maimaita sunan unguwar da suka zo wai abakwa, ita da Mujaheed ya ce mata can cikin unguwar rimi ne wajen masallacin Almannar ne gidan yake, taya kuma zata ji suna maganar Abakwa, amma sai ta danne tambayarta dan ba halin tayi magana, har motarsu ta shiga cikin layi dan haka Hajiya parking tayi a gefen hanya har sauran motocin suka yi gaba suka shiga layin ita ce ƙarshen shiga, dan so take su wuce da wuri suna shiga su fito sai gida. Motoci duk sun tsaya ba batun a buga hon mai gadi ya buɗe, haka duk mutane suka fito 'yan uwan ango suka yi jagora zuwa cikin gida, Hajiya ma ta juya tana cewa su Najwa.

To amarya gamu mun zo gidanki sai mu fita mu shiga ciki.

Ƙirjin Najwa dai bugawa yake yi domin tunani ne ya cika mata zuciya dan hayaniyar mutanen layi ma ya tsaida mata geto area aka kawota, dan motaci suna dira maƙota yara da manya suka firfito tuna kallon motocin 'yan ɗaukar amarya, 'yan uwan baba suka fito ɗayar ta kama hannun Najwa ta fito sai suka wuce zuwa gidan Hajiya suna take musu baya, sun zo daidai ƙofar gidan Gaggo yar baban Najwa tace.

Hankali dai karki faÉ—a kwata dan gata nan sai mun tsallaka kafin mu shiga gidan, ki buÉ—e ido kiga hanya kar amarya tayi wanka da kwata ki kafa tarihi.
Chapter 92 · 0% Book details