← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 103

Sashe 43

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abin ya zana ba dan Allah ba kenan, haba Ikram da imilinki zaki daÉ—i haka ai Kuluwa kuwa tana da kyau da ta samu hutu sosai zata yi fresh dan tana kama damu, ki ma bar wannan tunanin dan hali ake dubawa, ba ga Najwa ba tana da kyan ba hali sai son duniya ta sa a gaba, kinga imata aurenta zata yi dan haka in dai duk suna so ina goyon bayan haÉ—in.

Hakane kuma to Allah yasa yaya Zaidu ya yarda dan naga yafi son classy beb.

Sameeha tace Amin sai wayarta ta shiga ringing tana dubawa taga number ne kamar ba zata É—aga ba sai ta É—auka da sallama, jin muryan matar É—azu yasa ta É—an É—aure fuska suka gaisa sai Khairy take cewa.

Na yi miki magana online naga baki kai shine na ce bari na kira ki in kina free ki hau muyi hira.

Allah sarki ya kika isa gida É—azun? nafa gode. Yanzu kam barci nake ji dan har na kwanta kan gado.

Nima na kwanta kafin barcin ya kamani ne nace ki hau muyi hira, yaran duk suna gidanmu na kai su suyi hutu, Abbansu kuma baya gari ko yana nan ma yana gun amaryansa.

Allah sarki ashe kina da abokiyar zama.

Eh shekara É—aya da wata shida kenan da auren tana goyon yaronta Sadiq.

To Allah ya haÉ—a kanku.

Ameen. Kema Allah ya baki miji nagari.

Ya aka yi kika san bani da aure?

Sameeha ta faÉ—a tana waro ido waje, Ikram ko ta baza kunne tana jin hirarsu.

ÆŠazun naji kina magana da 'yar uwar ki a haka na fahimci kamar ba kida aure, ashe na cinka daidai.

Hmmm aiko dai.

To Allah ya zaɓa miki miji nagari ya baki wanda zai share miki hawaye ya Ƙaunaceki tsakani da Allah.

Ameen, amma aure kam baya gabana dan gaskiya komai ya fice min a rai.

Haba 'yar uwa da ƙuruciyarki fa, kuma duk macen data saba da namiji ai ba zata iya jure zama haka ba.

Tun da na iya jure tsawon shekara shida aiko zan iya rayuwa ko ba aure.

Sameeha ta faɗa cikin suɓucewar baki, Khairy kuwa gyara kwanciya tayi saboda an taɓo mata inda ke yi mata ƙaiƙayi.

Ban fahimci me kika ce ba?

Hmmm a bar maganar, kin ga yanzu ma mun cinye lokacin charting É—in a waya nagode da zumunci.

Ameen kina son dai kice kin gaji da hira da ni ne kawai.

Murmushi Sameeha tayi tana cewa.

Barci dai nake ji kuma na tabbata da oga na kusa ba zaki yi wayar nan dani haka ba.

Taf ko zanyi, wlh banƙi na bawa amarya sati guda ba. Nifa na saka shi ka ƙara aure wlh.

Ikon Allah ban taɓa jin macen da ta sa mijinta ya ƙara aure ba a zahiri sai ke.

Ina da dalili, idan kin samu lokaci zan baki labari kota chart ne yanzu bari na barki sai da safe ki gaida du Umma.

Zasu ji nagode.

Tace mata sai suka aje wayar Sameeha tana mamakin sakewar da Khairy ta yi mata, Ikram da duk ta ji hirarsu tace.

Anty wacece wannan naga kuna ta hira haka?

Murmushi Sameeha tayi ta shiga bata labarin Khairy, sosai tayi mamakin yadda ta shigewa Sameeha.

Anty ki dai bi a hankali nifa matan masu kuɗin nan da yawansu ba su da kamun kai, daga haɗuwarku ji yadda ta kiraki ta ɓata lokaci kuna magana, anya kuwa?

In Sha Allah sai Alkhairi da Allah na dogara, kuma nima dole nayi taka tsantsan in naga abin nata yayi yawa blocking É—inta zanyi wlh.

Ki dai tsaya kiga gudun ruwanta, Allah yasa mu dace.

Ta amsa da amin kana Ikram ta miƙe akan zata je bayi, Sameeha ta koma ta kwanta ta saka wayarta a silent ta yi addu'ar barci ta rufe idonta.

Da safe ne Umma ke faÉ—a mata zancen su Zaidu kuma tayi magana dashi ya amince itama Kuluwa ta yarda, amma sai bayan azumi za a tada maganar aure, Sameeha tayi musu fatan alkhairi, umma ta amsa da amin kana tace.

Kema da zaki bari ku daidaita da wannan yaron Idrisa da sai ayi bikin lokaci guda a huta, tunda kinga ansan shi ansan halinsa ba sai an yi wahalar bincike ba.

Umma wlh sam abin bai kwanta mini ba, da zaki magana da inna ta bashi haƙuri kawai.

Sameehaa bafa zaki zauna haka ba dole kiyi wani auren tunda ba halin komawa Aminu, ko da hali ma bai da lafiyar da zaki cigaba da zama dashi.

Umma ki mini addu'a kawai amma Iddrisa bai kwanta mini ba gaskiya.

Hmmm umma ta sauke ajiyar zuwa tana cewa.

Shikenan zanyi magana da Rukayya a bashi haƙuri dan ba za mu yi miki dole ba. Anjima zan mu je babban gida a can zasu kwana gobe In Allah ya kwimu zasu wuce ki fito ki zo ki kama aikin gidan Ikram ta tafi makaranta.

To Sameeha tace mata kana ta miƙe ta fito tsakar gida ta soma aiki. Data gama ta ɗaura abincin rana su Umma sai da suka ci kafin suka wuce gidan kakansu. Wajen ƙarfe biyu da rabi Sameeha tana zaune a tsakar gida tana katanta wani littafin Rahma Kabir Gashin Ƙuma a wayarta, sai taji sallamar Khairy ta shigo gidan da fara'arta. Da sauri ta ɗago tana kallonta cike da mamakin ganinta wanda ya bayyana ƙarara a fuskarta da kuma tunanin meya kawota gidansu.
[3/1, 7:28 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

28.

Sameeha tana kallonta har ta ƙaraso tabarmar da take zaune ta cire takalmi ta hau ta zauna tana cewa.

Sannu da hutawa? Ke kaÉ—ai ce a gidan?

Yauwa sannu da zuwa. Lafiya kika zo?

Sameeha ta bata amsa da tambaya fuskarta a dan ɗaure, Khairy sai da taji wani iri amma ta san dama dole za ayi haka tunda ba saninta tayi ba take shige mata, bata yi magana ba wayarta ta yi ƙara ko da ta duba Anty Amina ce dama sun haɗa plan idan ta zo zata yi mata text, to kafin ta shigo ta faɗa mata ta iso gidan shiyasa ta kira yadda zasu yi amfani da damar wajen Sameeha ta yarda da Khairy. Tana ɗaga kiran tace.

Anty ina yini.

Lafiya lau, kina gina kuwa.

Aiko na je gurin mai kama da Mubeena dana ce miki jiya mun haɗu, wlh na kasa haƙuri na je gidansu, gata ma ku gaisa.

Ta ƙare magana tana miƙawa Sameeha wayar tace.

Yayata ce ku gaisa.

Ba yadda taso dole ta amsa ta kara wayar a kunne ta gaisheta, Anty Amina ta amsa tana cewa.

Kiyi hakuri da Khairy nasan ta takura mini haka take da shegen naci, kuma dalilin wai kina mata kama da wata ƙanwarmu ce da Allah yayi wa rasuwa, rana guda aka yi musu aure ita Khairy amma Allah yayi mata rasuwa gurin haihuwa, tun jiya ta kirani take cewa taga mai kama da Mubeena.

Allah sarki Allah ya jikanta da Rahma yasa mu cika da imani.

Ameen, ina ƙara baki hakurin takura miki da take niman yi.

Bakomai ai, nagode.

Cewar Sameeha kana tayi mata sallama ta miƙa wayar ga Khairy, tana amsa Amina ta rufe ta da faɗa kuma Sameeha tana ji saboda vulume ɗin wayarta ana ji sosai.

Haba Khairy daga haÉ—uwa da mace zaki nima takurata me yasa kike haka, idan ke kin yarda da ita ita ta yarda dake ne da zaki nima shige mata, ba a haka gaskiya yadda rayuwar nan ta zama abin tsoro mutum ma abin tsiro ne, wai ma da kika fito kin faÉ—awa Ahmad ina zaki.

Wlh da izininsa na fito, na faÉ—a masa zanje gun mai kama da Mubeenarmu.

Wato shima kin faɗa masa kenan, kuma da yake shima sai a hankali ya biye miki ya barki kika fito, Allah ya kyauta amma bana so ki takurawa 'yar mutane ta ɗauka da wata manufa a ranki, tunda yanzu ɓata gari sunyi yawa, da mutuncinki da komai ki zubar da ƙimar gidanmu.

Haba Anty ki daina yi mini wannan faɗar daga naje gunta, amma tunda hakane zan rabu da ita ni dai nasan wlh bazan taɓa cutar da ita ba balle nayi abinda zai ɓata sunan gidanmu.

Tana kaiwa nan ta kashe wayar ta miƙe tsaye idonta cike da kwalla tana cewa.

Dan Allah kiyi haƙuri ni ban zo gareki da nufin cutarwa ba, ban san da wani fuska ma kike mini kallo ba, amma ni tsakani da Allah nake nazo gareki kuma ganinki yana tuna mini 'yar uwata Mubeena ne. Sai anjima.

Jikin Sameeha yayi sanyi sosai kuma ta fahimci lallai ba cutarwa a tare da ita musamman maganganun data ji yayarta tana faÉ—a, hakan sai ya saka ta samu natsuwa a ranta dan dama tana ta addu'a idan matar nan sharri ce a gareta Allah karya bata dama cutar da ita ya kuma rabata da ita. Da sauri ta dakatar da Khairy dan har ta kusa fita daga gidan.

Dan Allah ki dawo Hajiya muyi magana.

Tace cikin daga murya, Khairy data saki wani shu'umin murmushi sai ta gimtse fuska tayi na tausayi kana ta juya ta dawo ta zo ta zauna, kenan plan É—insu ya tafi kamar yadda Anty Amina ta tsara musu É—azun da safe. Sai da ta zauna kafin Sameeha tace cikin kulawa.
Chapter 43 · 0% Book details