← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 103

Sashe 63

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cewar Shamsu, nan take Sameeha ta buɗe wayarta ta karanto masa number ɗin Najwa ya saka a wayarsa ya soma kira, Najwa a cikin barci taji karar waya hakan yasa ta farka ta duba wayar taga number ne har ya katse bata iya ɗauka ba ta mayar da wayar ta aje, sai ga wani kiran ya sake shigowa cikin gajiyawa da ƙarar tayi saurin ɗaukar wayar ta kara a kunne ba tare da tayi magana ba.

Hajiya Najwa halan kina barci na tashe ki, kiyi haƙuri kamawa tayi da fatan kin gane me magana.

Shamsu yace bayan ya saka kiran a handsfree yadda zasu ji komai, Najwa ta tashi zaune dan ta gane Shamsu ne amma saboda tayi masa wasa da hankali tace.

Ban gane me magana ba.

To Shamsu ne mijin Ikram, na kira ki ne na baki haƙuri akan hukuncin da kika shirya ɗauka a kaina, saboda kin turawa Ikram saƙo gashi ta rufe mini ɗaki tana ta cin mutumci na akan haka, a takaice gani zan kwana a mota dan ta fusata sosai ina tsoron kar dare yayi tayi mini wani illa in barci ya ɗauke ni.

Hmmm ni ban fahimci inda ka dosa ba.

Najwa ki nasan fa kin san komai ba sai mun tsaya muna wasa da hankulan juna ba, na tabbatar sai yau ne kika san nine mijin da Ikram ta aura, domin É—azun na ganki a gidansu kuma tsakani da Allah bansan Ikram 'yar uwarku bace sai da aka gama zancen aurenmu da ita, lokacin take faÉ—a mini kema an saka bikinki to a cikin hira take faÉ—a mini inda kike har na gano ke ce, kuma in zaki yi mini adalci kece kika koreni dan haka bai dace ki hukunta ni ba.

Hmmmm amma ka rasa wacce zaka aura sai 'yar uwata saboda kaci mini fuska ko, meyasa daka gano nice Najwa 'yar uwarsu baka fasa auren ba.

Amma kin san an saka ranar aurenki hakan ya ƙara mini ƙarfin guiwan dana cigaba da niman Ikram, Najwa kinsan ina sonki kuma bazan taɓa son wata mace sama da ke ba amma kika koreni, na rasa me ye makusa a jikina kika yi mini haka.

Meyasa zaka ɓoye mini asalinka? Meyasa ka ɓoye mini komai naka ka muna mini kai talaka ne.

Saboda na gwadaki ne na gane zaki so ni domin Allah, sai kuma baki kaiga cin jarabawata ba kika ma koreni, ni dai yanzu ki faÉ—a mini me kike so a gareni domin ki wanke ni a gun Ikram, dan sosai kika haddasa husuma a tsakaninmu.

Yanzu kana mufin Ikram ta kulle maka É—aki a mota zaka kwana?

Allah kuwa, yanzu ina tunanin kona je na kama hotel ne, ni ina so ki faɗa mini me kike buƙata da zai wanke laifina a gunki ki wankeni a gurin Ikram dan Allah.

Ko meye nace ina so zaka yi mini shi?

Najwa ta faɗa cikin jin daɗin hakkarta ta cimma ruwa, Shamsu yace cikin sanyin murya dan ya ƙara karya mata zuciya.

Eh in dai baifi ƙarfina ba.

To ina so nima ka aureni.

What?

Ya faɗa da ƙarfi su Sameeha ma mamaki yasa suka zazzaro ido waje domin tun sadda suka fara magana zuke mamakin Najwa, Najwa ta ce cikin 'yar dariya.

Eh ko ba zaka iya aure na ba ne? to hakan shine zai wanke laifinka a guna kuma shine zai sa na numa ma Ikram cewar bakin rijiya ba wajen wasan yaro bane.

Taya hakan zai yuwu? Keda ake shirin yin aurenki, sannan me Ikram tayi miki da ta cancanci haka a gunki.

Hmmmm saboda ta aureka shine laifinta, sannan kuma idan ka yarda da aurena ni nasan yadda zan saka a fasa aurena da wancen.

To shikenan zanyi tunani akai amma kinsan dole zancen aurenmu zai É—auki lokaci saboda yanzu ne nayi aure.

In dai ka amince to ko nan da shekara É—aya ne zan jiraka, sannan ka aje batun zaka yi tunani idan ba haka ba wlh sai na cigaba da kunna maka abubuwan da sai kayi dana sanin auren Ikram. Sannan ko kaje ka faÉ—a mata nice nayi mata sako ba zata yarda ba saboda sun yarda dani kuma ina da hanyar wanke kaina.

To hajiya Najwa nagode Allah ya saka da alkhairi da kika warware mana zare da abawa, ga yaya Ibrahim da Anty Sameeha dama Ikram duk suna jinki kuma suna gaisheki da jan aiki.

Shamsu ya ƙare maganar yana 'yar dariya, a zabure Najwa ta tashi ta zauna tana jin wani gumi yana damunta, bata taɓa zaton gadar zare ya saka mata ba, tace cikin ƙara ji.

Me kake nufi da zancenka Shamsu?

Hanyar da kika bi nima shi nabi na gano gaskiyar abinda kika haÉ—a, Ikram ga 'yar uwarki kuyi magana.

Ya kare maganar yana miƙawa Ikram wayar, Ikram tace cikin sanyin murya.

Ni babu abinda zan iya ce mata taje ita da Allah.

Najwa kin kyauta Allah ya shiryeki.

Muryan Sameeha kenan data yi magana cikin damuwa, Najwa kashe wayarta tayi ta aje ta a kan gado tana jin wani baƙin ciki yana ruruwa a zuciyarta, wannan shine karo na farko data haɗa plan ya rushe bata kawo Shamsu daɗin baki yayi mata ba, aiko yaci bashi dan ta ɗauki alwakarin yin maganinsa sai ya san wacce yaci amana, haka ta miƙe ta manna bayanta a bango tana huci zuciyarta tana tafarfasa, dakar ta tausa kanta ta koma ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya, yanzu kenan yasa taji kunya a idon su Sameeha, da wani ido ma zata kallesu? tana ganin ba zata sake taka ƙafarta ba zuwa inda suke dan abin da kunya, ba zata yarda ma inna ta san da wannan abin da tayi ba saboda tasan zasu kwashi rikici, addu'a take Allah yasa su rufa mata asiri su bar maganar a haka.

Su Sameeha kam Ibrahim sosai ya yi musu nasiha yace kuma su bar zancen a tsakaninsu dan kar wasu suji suyi dariya tunda naka naka ne komin lalacewa Najwa jininsu ce, dan haka su barta da halinta kuma su rufe maganar kar ma su nuna mata ko a fuska, daga bisani suka yi sallama da juna wajen ƙarfe sha ɗaya da minti sha shida suka fito Ikram da Shamsu har mota suka rakasu kana suka wuce, sai suka dawo ciki Ikram sai ɓoye fuska take yi cike da jin kunyar abinda tayi wa Shamsu, da taji maganar Sameeha da bata riski kanta a haka ba, shiko Shamsu nuna wa yayi ko kaɗan bai damu ba kuma komai ya wuce.

Duk da wannan abin ya faru bai hana gidaje biyu amare da angwaye sun more amarcinsu ba, dan kuwa ko wanne ya baza komar soyayyar sa ya kwashi roman so da ƙauna. Washe gari ne da yamma aka shirya kayataccen walima a cikin farfajiyar gidan Hajiya nan second gate, 'yan gidansu Ikram ma sun zo dan dama wasu sai a ranar ne suka samu damar zuwa ganin ɗakin amare, Ikram ma Shamsu ya kawota ta sauka a sashin Sameeha sai da lokacin walima yayi kafin suka tattara zuwa sashin hajiya, kota wani ɓangare soyayya ake nuna musu Masha Allah abun dai sai wanda ya gani, sun san sunyi dace da dangin miji saura musu kyautatawa da kuma kama mazajensu hannu bibbiyu. Duk waɗanda suka zo wannan walimar sai da suka tafi da kyautar zanin atamfa da kuma kayan ciye ciye, ga wa'azin da aka gabatar ya kayatar wanda mutane sun tafi da malama Haajara a baki saboda iya sarrafa harshe da kuma ilimin zaman aure da ta baje musu suka kwashi garaɓasa. Bayan sallar magrib kowa ya watse gida ya rage sai dangi na jiki, Ikram a sashin Sameeha ta zauna, sosai Sameeha ta kuma yi mata faɗa akan abinda ta yiwa Shamsu jiya, ta kuma nusar da ita yadda ake zaman rayuwa sosai, domin ita tana da wayewa da sani akan zaman aure dan jiya ba yau ba ne, Ikram ta yi mata godiya ta ɗaura da cewa.

Nayi mamakin abinda Najwa ta aika jiya hakan yana nuna tana bakin ciki da aurena, kin ga kenan ashe bada zuciya É—aya ta shigo jikinmu ba aketa hidimar biki da ita tunda kinga yauma bata zo ba sai Inna, wai harda cewa inna ta faÉ—a mana ba tada lafiya ne, banda kunce a rufe maganar da sai na faÉ—awa Inna abinda ta mini.

Ikram ki bar komai ya wuce kin fita har a gurin Allah, sannan ki cire damuwarki akanka ki fuskanci aurenki, idan ta zo ta nima sulhu shikenan mu cigaba da zumuncinmu tunda son zuciya ya sa tayi haka, kuma ma da kunya tace zata ƙara aikata aikin rashin gaskiya a garemu.

Anty wlh yadda na karanci Najwa sam baki gane halinta ba, na tabbatar ba zata sake zuwa inda muke ba tana da riƙo sannan kuma baƙin cikin nasarar da muka samu bazai barta ta cigaba da zumunci damu ba, ni kam ko ta dawo bazan sakar mata fuska ba dan nasan ta da mugun son zuciya.

Ni dai nace ki bar wannan maganar kuma ga sakonki nan Khairy ta ce na baki tsumi ne da kuma gumba da kayan ciye ciye dai na mata, ki riƙa amfani dasu a hankali, in kuma baki gane ba ki kirani nayi miki bayani.

Hmmm Anty khairy bata gajiya, ni dai wlh bazan sha wani abu yanzu ba dan hmmm.

Sai tayi shuru tana sunne kai, Sameeha ta yi murmushi tana cewa.

Yarinya da haka zaki saba Allah dai ya kawo 'yan dugui dugui masu albarka dan ke yanzu zaki fara aje garke nikam ba yanzu ba.

Allah anty ina fatan ki haifa mana twins, nasan yaya Ibrahim sai yayi yayyafin kuÉ—i ga mutane dan murna.

Ki fara faÉ—a a akanki kafin ni dan ina da Abi da Amrah.

Sameeha ta faɗa tana miƙewa zata ɗauko wayarta a chrgy, Ikram tayi murmushi.

Su can gidansu daban nan gidan kuma suma nasu zaki haifo musu.

Ikram yaushe muka fara irin wannan maganar dake, wato aure daÉ—i ko.

Laaa anty ni kin ma koreni, bari naje falo na jira yazo mu tafi.

Kima kirashi yazo ya É—auke ki kawai kin ji.
Chapter 63 · 0% Book details