Sashe 8
Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ina so na sanar dake bana son ƙazanta ki riƙa wanka, kuma duk lokacin da mijina yake gari kar ki sake na ganki kin fito falo, aikinki daga shara sai mofin shima iya falo da ɗakin yara, ɗakina da ɓangaren babansu ni zan gyara, sai wanke wanke, sannan ko bana nan ban yarda kiyi girki ba, kar in ganki a gurin injin wankinmu ki wanke kayanki a waje ba ruwanki da namu wankin. Idan na kamaki da munafurci ko rashin gaskiya wlh zan koreki dan bazan ɗauki rashin arziki ba.
To anty In Sha Allah zanyi duk yadda kika ce.
Yauwa kuma zan riƙa baki dubu goma duk wata.
Su kuma cewa suka yi dubu sha biyar zaki biyani.
To su daban ni daban, sai yadda naga kamun ludayin aikinki tukuna ki samu haka.
To jamila tace tana cuno baki dan gaskiya ba haka suka yi dasu ba, sai da ta tabbatar da za a biyata sha biyar kafin ma ta yarda da zata yi musu aikin da suka saka ta, saboda sun gama jera mata duk rahoton da suke so ta kawo musu akan Sameeha da duk abinda ke wakana a gidan. Sameeha ta miƙe ta ce ta bita a baya, suka isa wani ɗaki dake kusa da kitchen ta buɗe, akwai gado a ciki da komai dan ɗakin an yi shi ne saboda baƙi, tace nan ne ɗakinta kuma ta kula da tsaftarsa dan bata yarda da ƙazanta ba, Jamila gyaɗa kai tayi ta shiga ta zauna a gefen gado, Sameeha ta fita zuwa ɗakinta da su Abi suke ciki tare da Ikram suna kallo dan akwai tv a ciki. Jamila da harara ta bita tana yatsine fuska taja tsaki ta ɗauko wayarta a jaka ta danna number ɗin Hauwa, bugu ɗaya ta ɗauka ta ce cikin make murya.
Wlh Hajiya matar nan ba tada kirki sai É—aure fuska take kamar dai bata son ganina a gidan, kuma wai dubu goma zata biya ni bayan ba haka muka yi da ku ba, gaskiya ni dai ku cikasa mini dan wlh aikin da kuka sakani yana da wahala fa.
Karki damu Jamila ni zan cikasa miki ai ke tamu ce duk abinda kike so shi za a yi, kin ga dai yadda take ko, to ina so ki riƙa bani labarin duk abinda ke faruwa a gidan.
Karki ji komai ai ni nayi miki alƙawari.
Daga haka suka yi sallama Jamila ta ajye wayar ta kwanta rigingine cike da nutsuwa tana sauke ajiyar zuciya tare da latsa laushin katifar kamar gidan ubanta.
[1/31, 6:39 PM] Rahma Kabir: *ABIN DA CIWO*
Na
©Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 6.
Sameeha tana shiga É—akinta ta zauna a gefen gado tana cewa.
Ikram ku tashi ku koma falo da kallonku ina so na É—an samu barci.
To anty amma har Yaya Hauwa ta tafi ne?
Eh 'yar aiki ta kawo mini gata can na bata É—akin kusa da kitchen sam hankalina bai kwanta da yarinyar ba, gata dai 'yar kauye ce a yanayin shigarta amma alamu ya nuna idonta a buÉ—e yake.
Ai Wlh anty ke kika kyalesu amma da nice banga 'yar iskan da ta isa tayi mini haka ba, kuma umma sam bata bin bayanki É—azun ina ji da kuna waya sai faÉ—a take yi miki. Allah shawarar da zan baki tana yin wata guda ki sallameta, in sunyi magana kice bata yi miki aiki mai kyau, kinga sai ki sa umma ta nima miki wata.
Hmmm umma cewa tayi wai ko marina Hauwa tayi karna rama na rabu da ita saboda sharri suke kokarin bina dashi, ni kam bazan É—auka ba wlh, shiyasa ma ba zan sake faÉ—awa umma matsalata da su ba tunda ba bin bayana take yi ba. Ni ina ganin É—iyar Inna Rukayya zan É—auko kawai in sakata a makaranta tunda kinga su can ba wani karatu suke samu ba.
Shikenan ma ba ruwanki da wata 'yar aiki tunda aikin gidan ba wahala, na tsakar gida kyasa mai gadi da driver suna gyara miki.
Allah dai yasa mu dace.
Cewar Sameeha, Ikram ta amsa da amin kana ta tasa ƙeyar yaran suka fice daga ɗakin.
****
Najwa.
Har ta isa gida tana tunanin shawarar da Nafeesa ta bata akan ta haɗa kai da su Hauwa, sai dai ita tana ganin kamar ba zasu karɓeta ba ƙila suyi zargin ko Sameeha ce ta sakata, amma zata yi iya kokarinta ganin ta tusa kanta in dai zata samu cikar burinta, dan sai da Nafeesa ta ƙara hasko mata auren Aminu kafin ta ƙara jin kwarin guiwa, a yadda take jin zuciyarta tana bugawa so take ta ƙara tozali da shi taji muryansa ko hakan zai saka ta samu sukuni, sai dai ko taje gidan ba zata ganshi ba dan ta san zai yi tafiya kuma sai ya jima bai dawo ba kamar yadda Ikram ke fadya mata, koda ta isa gida ta samu inna ta tafi barkan da ta ce mata, dan haka ta kwanta a ɗaki tare da danna wayarta da take rakani kashi, taja guntun tsaki tana cewa.
'Yar wayar zamanin nan ma ta gaga in riƙe saboda duk samarin nawa talauci yayi musu kanta, haba wlh dole in sauya sheƙa nima in faso gari a dama dani, dan na gaji da wannan rayuwar maneji, yanzu da ace ina da babban waya ƙila in lalubashi a facebook in ga hotonsa ko ɗan chart in fara da shi.
Ta ƙare maganar tana jan guntun tsaki, sai ga kiran Zaidu ya shigo kamar ba zata ɗauka ba ta ɗaga kiran ta saka a kunne tana sallama, Zaidu ya amsa mata yana cewa.
Amaryata ya gajiyarki na jiya da fatan Sameeha bata gajiyar min dake sosai ba.
Hmmm ai gajiya tabi lafiya, kyawun gidanta ma ba zai sa naji na gaji ba dan Wlh Anty Sameeha ta dace da gidan duniya.
Gaskiya kam gidanta yayi kyau Allah ya bamu kuÉ—i masu albarka na gina miki kamar sa ko wanda ya fishi.
Ameen ya rabbi, dama ina shirin kiranka sai naka ya shigo.
Ok ina jinki me ya faru.?
Waya nake so Android wacce ake yayi na gaji da riƙe rakani kashin nan. Kaga ko da baka samu zuwa ba sai mu riƙa yin charting ko.
Hakane amma yanzu ina cikin uzuri sai in na gama da shagona In Sha Allah zan siya miki mai kyau, dama tuntuni nake tunanin yin haka.
Ai dama na san ba zaka siya mini ba sai dai kayita mini hanya hanya, in ba ta ƙuƙe mini ba ai da bazan tambayeka ba.
Sai kit ta kashe wayarta dan ta nuna masa taji haushi kuma da gaske haushin ta ji dan gabaɗaya ji tayi ta tsaneshi bata son ganinsa, Zaidu ya ƙara kiranta amma taƙi ɗauka har sai da yayi mata kira sama da uku tayi banza da shi, ya tura mata da sakon.
_Kiyi haƙuri zan shiga kasuwa yanzu in siyo miki koda second hand ne sai ki fara amfani da shi kan na samu kuɗi na siya miki sabuwa._
Data karanta ta ɗan saki murmushi sai ta ki bashi amsa akan bata sauko ba dan ta ƙara tunzurashi ya siyo mata ɗin, ta yatwine fuska.
Dama tuntuni haka nake maka da yanzu na dan samu abinda na sama a jikinka, Nafeesa tasha bani shawarar haka sai naƙi yarda ganin kar in fito da kwaɗayi ga samarina su raina mini wayo kuma suna yi mini kallon ustaziya mai hankali kar na zubar da kimata, amma yanzu ma duk zan yi maganinku na zubar daku gabaɗaya a kwandon shara, Saboda nayi mijin da ya kere sa'a zai fito mini da ajina sosai.
Tana gama faɗar haka ta miƙe ta fito dan ɗaura abincin rana tunda Inna tabar mata sallahu a gurin Yaya Sadik da ta samu a gidan.
***
Zaidu.
Yana zaune a É—akin umma suka yi waya da Najwa, bayan ya gama tura mata sako ya duba umma yana cewa.
Wani lokacin yarinyar nan ina rasa inda tunaninta yake zuwa, gata da ilimi amma wani lokacin bata aiki da shi.
Meya faru kuma?
Ummu tace tana dubansa, sai ya bata labarin yadda suka yi yanzu, umma ta ce cikin faÉ—a.
Haba Zaidu ai tayi maka kawaici tunda sai yanzu take nuna maka tana son babbar waya, kuma ai ya kamata ka siya mata tunda ita ce ake yayi, ko Ikram baka ga wacce Saurayinta ya siya mata bane, in har kana so ka samu zuciyar Najwa dole sai kana kyautata mata, tunda 'yar uwarka ce ko ba soyayya kayi mata dan zumunci.
Amma umma nace mata ta bari na samu kuÉ—i yanzu ina fama da shagona ne.
Ka ɗauka cikin kuɗin ka siya mata mai saukin kuɗi itama ta shiga zamani a dama da ita, na tabbatar in kai ka fara siya mata waya a samarinta ka ciri tuta kuma zaka samu matsayi mai kyau, sannnan gidansu ma ba zasu hana ta riƙe wayar ba tunda kai na gidane ka bata wayar.
To shikenan umma zan duba na gani, amma naga tun yanzu kina goyon bayanta kar nan gaba tayi mini laifi na kawo kararta ki shigar mata.
Aiko kasan ko kaine da gaskiya ba zanbi bayanka ba dan yana da kyau in nuna kawaici, ba zan soka ba in ƙita dan na haifeka.
Amma ai wasu iyayen ko nasu keda laifi goyon bayansa suke yi.
To ni ba irin wannan iyayen bane ai kaso naka duniya ta ƙishi, kaƙi naka duniya ta soshi.
Wannan zancen haka yake ummanmu bari na fita na fara niman mata wayar kafin ta fashe dan fushi.
Ya faÉ—a yana 'yar dariya, umma dariyar tqyi tana a dawo lafiya Allah ya tsare ya amsa da amin ya wuce kasuwa.
Kamar yadda yayi mata alƙawari da yamma bayan sallar la'asar ya isa ƙofar gidansu ya aika mata yaro da wayar a cikin leda da karamar takada a ciki ya wuce. Najwa ce a tsakar gida yaron ya samu ya bata sakon yace inji Zaidu, ta amsa da sauri sai yaron ya fita, inna ta fito daga bayi tana cewa.
Me Zaidun ya aiko miki da shi?
Yanzu zan duba in gani.