Sashe 17
Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A'a Ikram bana son irin wannan maganar ko ba soyayya a tsakaninta da Zaidu, ita 'yar uwarmu ce da bamu isa mu yakiceta ba, sannan ni ba zata taɓa gundurata ba tunda abinci kashi ne, tazo ta ci ta tafi ina ce shine dai damuwarki?.
Ikram kwafa tayi ta miƙe tana magana ƙasa ƙasa dan gabaɗaya takaici ya cika mata zuciya, gana su Hauwa ga kuma Najwa da ta kara mata, Sameeha da guntun murmushi ta bita, sam Ikram ba tada haƙuri ana mata abu take nunawa har ma tayi faɗa akai, saɓanin ita da take danne damuwa a zuciyarta sai dai yayi ta cinta bata iya ramawa, sai dai zuwa yanzu dole zata koyi fitar da damuwa dan taga in tana yiwa su Hauwa shuru shuru to zasu kaita su baro ne, ta san su ba irin wanda za ana yiwa kawaici bane. Tana cikin cin taliyar data dafa musu jelof ɗin man gyaɗa da kifi, Najwa ta shigo da sallama fuska sake Sameeha ta tarbeta har ta ƙaraso ciki ta zauna suka gaisa, Sameeha tace.
Tashi ki shiga kitchen ki É—ibo abinci dan naga daga makaranta kike, hala ko gida baki isa ba.?
Hmmm maganar da Ikram ta faÉ—a mini yasa na fasa zuwa gida na tawo nan, amma na sanar da inna a waya na wuto gidanki. Anty Allah ya shiga tsakaninki da mutanen nan amma sam basa sonki da alkhairi.
Aniyar kowa zata bishi.
Amm yaya Aminu bai ƙaraso ba?
Tukuna dan sai ya kai la'asar tunda jirgin ƙarfe biyu ne kuma atleast sai sunyi awa biyu da mintuna a hanya.
Najwa tace Allah ya kawo shi lafiya sai ta miƙe ta wuce kitchen dan ta ɗiba abinci, Sameeha tace amin ta cigaba da cin abincinta dan bata yarda damuwa yana hanata cin abinci ba. Najwa ta zuba abinci mai mata ta fito ta zauna tana ci ba jimawa sai ga tikram ta fito daga ɗaki tare da su Abi tana kallon Najwa ta kawar da kai taƙi yi mata magana, Najwa kuwa ta taɓe baki taki kulata haka suka cigaba da zaman falon ko wanne da abin da yake saƙawa har suka kammala cin abincin suka cigaba da kallo. Wajen ƙarfe uku saura sai ga Zaidu ya zo gidan saboda Ikram ta kirashi ta faɗa masa sakon Najwa ta kuma sanar da shi ta zo gidan, shiyasa yace bari yazo suyi magana ta faɗa masa baki da baki ba zata aure shi ba. Najwa tana ganinsa tasha jinin jikinta domin har ga Allah bata shiryawa haɗuwa da shi ba sai komai ya koranye, amma ta san duk shirin Ikram ne ta kirashi yazo, haka ta haɗe fuska kamar an kashe mata wani dan dole zata kwaci kanta ba zata yarda su liƙa mata shi dole ba dan an wuce auren tilas yanzu, sai da ya gama gaisawa da Sameeha yayi mata jajen abin da ya faru kana ya kalli inda Najwa take zaune tana cika tana batsewa, yace cikin danne zuciyarsa.
Hajiya Najwa ba magana ne ko dai sakon da kika bawa Ikram da gaske ne, dan ban gamsu ba shiyasa na zo da kaina naji laifin me nayi dana cancanci haka.
Ai ba se kayi laifi ba zan ce bana yin auren, kawai dai na hanga na duba naga baka cika sharuÉ—É—an mijin daya dace na aura bane, tunda har yanzu baka shiryawa aurena ba, ni kuma aure nake son yi kuma da wanda ya dace.
Yanzu nine ban shirya aure ba haka muka yi dake? Meye aibi na kuma? Ina ce ke kika tsaidani kan batun turowa.
Eh saboda baka samu aiki ba kuma bana tunanin shagon daka buɗe zai riƙe mu.
Najwa duk me ya kawo wannan maganar? kin mance komai yin Allah ne, tunda ni naji nace zan iya sai ki zuba ido kiga na kasa É—in kafin ki yanke mini hukunci.
Hmmmm ai wlh yaya Zaidu dama Najwa can ba sonka take yi ba yaudararka take yi tunda ba tun yanzu ba nasanta da shegen buri, ka rabu da ita kawai ga matanan da yawa a gari masu tarbiyya sai ka zaɓa zaka aura.
Cewar Ikram data ƙara kuluwa da maganganun Najwa, Sameeha ce ta nuna ta da yatse ta ce ta wuce su tafi cikin bedroom karta sake jin bakinta, itama ta miƙe ta tasa keyar su Abi dan ba zata saka baki ba tunda ta kula Najwan ba mutunci ne da ita ba kar tace ma sunyi mata taron dangi, ba su kai ga shiga ciki ba suka tsinkayi maganar ta tana cewa da ƙarfi.
Ai da kin rabu da ita ina daidai da zamaninta, kuma aurensa É—in ne bazan yi ba dan ba aji na bane idan kinji haushi ki rufe ido ki aureshi, 'yar rainin wayo kawai, ina da dalilin da zan rabu dashi tunda bai cika sharuÉ—É—an mijin daya dace na aura ba, shiyasa tun wuri na fito na faÉ—a dan kar abu yayi nisa ace nayi yaudara.
Tana gama faÉ—ar haka ta wuce fuuu kamar guguwa cike da borin kunya dan dama da hauka ake nadeta. Zaidu da ido ya bita dan ya kasa magana haka suma su Sameeha da ido suka rakata har ta fice daga falon, sai duka dawo suka zauna Ikram sai zuba masifa take yi Sameeba tace.
Dan Allah ya isa haka tunda wacce kike yi dominta ta tafi, kai kuma yaya Zaidu dan Allah ka rabu da ita a cigaba da mutunci, nasan dai abin da ciwo amma haka zaka danne dan tazo da yaudara amma kanta ta cuta.
Ai Sameeha kamar yadda ɗa yake barin cikin uwarsa to na rabu da ita har abada, ban taɓa tunanin Najwa zata yi mini haka ba ashe ba tada mutunci a gabanku take faɗa mini magana ko kimata bata gani ba, da in aure ta ina dana sani gwara na haƙura kuma zata haɗu da daidai ita duniya ce.
Kayi hakuri yaya kuma Allah ya baka ta gari.
Cewar Sameeha.
Ameen amma bani ba ƙara niman 'yar danginmu, ke na aje niman aure har zuwa nan gaba na nima kuɗi dan 'yan matan yanzu ido a kuɗi ne in ba kada Naira ba a yi da kai.
Ba duka aka zama ɗaya ba wlh yaya akwai nagari suna nan suna jiran mazan aure, dan nima kaga ba ruwana da buri da son duniya ko anty Sameeha Allah ne ya kawo mata Aminu ta aureshi kuma suna tare ne har dukiyarsa ta bunƙasa.
Cewar Ikram, nan suka cigaba da tattaunawa har aka kira sallar la'asar Zaidu yayi musu sallama ya wuce gida zuciyarsa a jagule saboda ya rasa Najwa duk da yana yiwa Allah godiya data bayyana masa zahirin yadda ta ɗauke shi. Koda ya isa gida ya faɗawa Umma komai, cewa tayi Alkhairi ne rabuwarsu kuma Allah ya zaɓa masa nagari dama tana ta addu'a akai to rabuwan shine mafita dan itama tayi mamakin kalaman Najwa zata yi kokari tayi magana da inna su tsawatar mata inda miji ma ta fito dashi su aurar da ita dan alamunta ya nuna ta fara sauka daga tarbiyyar da suka bata, wataƙila ta samu sabbin kawaye masu hure mata kunne ko kuma saurayin da yake kokarin sauya mara tarbiyyarta.
Wajen biyar saura Aminu ya shigo gidan, ruwa kawai yasha yace Sameeha ta miƙe ta ɗauko mayafi su tafi babban gida dan sun gama haɗuwa su suke jira, Sameeha hijab ta ɗauko ta zumbula ta fito suka wuce a motarta dan nashi motar ya saka driver ya wanke masa ita, suka bar yaran a gida tare da Ikram.
*Yau gidan biki har biyu naje ban samu zama ba kuyi hakuri da wannan In Sha Allah zaku samu mai yawa gobe In Allah ya kai mu*
[2/12, 8:42 PM] Rahma Kabir: *ABIN DA CIWO*
Na
©Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 13.
Babban Gida.
Su Aminu suna isa suka tadda mutanen gidan a asalin part ɗin iyayensu, wanda suke rufe shi sai in wani abu muhimmi ko kuma sha'ani suke buɗewa, bayan sun zauna a katon kafet daya malale ɗakin dan babu kujeru, suka gaggaisa tare da ɗan taɓa hira kafin Alhasan ya koro bayanin musabbabin haɗuwarsu, yayi dogon sharhi tare da jan kunne da kuma nasiha akan muhimmancin zumunci da kuma haɗin kan junansu, daya ja fasali sai Kamalu shima ya ɗauka yayi nashi bayanin daga bisani suka bawa Laure damar magana buɗar bakinta sai cewa tayi.
Duk wannan dogon bayanin banji kun yiwa Sameeha faÉ—a ba, domin duk ita ce musabbabin faruwan waÉ—annan abubuwan, kuma naji kuna ta zancen mune muka saka aka É—auki video dan mu tozarta ta, haba haba ai da hankakinmu zamu yi mata haka ba, sai kace dama muna shirye da faÉ—an data kawo da kanta, gaskiya ba kuyi mana adalci ba dan bamu san komai akan maganar video ba.
Laure ba mun taru bane dan mayar da magana, ko ku amsa laifinku ko karku amsa kune ba kuda gaskiya, kuma mun taru ne a nan domin mu kawo sulhu a tsakaninku, ku yafi juna komai ya wuce.
Cewar Alhasan, a lokacin Aminu yayi gyaran murya ya soma magana.
Ba tun yau ba suka ɗauki karan tsana suka ɗaurawa Sameeha ina sane da haka amma nake kawar da kai, sai dai gaskiya haƙuri na ya fara ƙarewa, ace duk rikicinku bai tsaya a nan har sai kunyi shela da matata a duniya tare da zagi da Kasafi, wannan dalilin yasa na baro duk abinda nake yi nazo gareku domin a kawo karshen rikicin nan, gaku ga Sameeha ku faɗi abinda take yi muku da kuka sakata a gaba.
To ance maka wani abu tayi mana, me ko zata mana tunda ka zama sallamamme a gunta, sai abinda ta kitsama zaka zo kana yiwa mutane ɓaɓatu, iye Aminu gaka mai mata, da fatan ka tambayeta rashi mutuncin data yi mana a gidanku, har da cewa ba zata buɗe mana ɗakuna mu gani ba saboda gamu ɓarayi kar muyi muku sata, to kusha kuruminku ni dai in taka ƙafata inje gidanka sai in Sameeha bata nan dan kar in je tace nayi mata wani abin.