← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 103

Sashe 62

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya miƙe yana gyara mazaunin babbar rigarsa, Sameeha ma miƙewa tayi dan da mayafi a jikinta suka fito tsakar gidansu ga motar daya sauka yanzu, ya buɗe mata mazaunin kusa dashi ta shiga ya rufe kana ya zagaya ya shiga mazaunin driver ya kunna mota tare da hon mai gadin sashin ya buɗe masa gate kana ya fice da motar.

****

Najwa.

Tunda ta koma gida ta ƙasa komai sai saƙa da warwara, gani take in tabar Ikram da Shamsu sun ci bilis, shiyasa ta kashe wayarta gabaɗaya dan kar a dameta da kira, tana buƙatar zurfafa tunaninta akan hukuncin da zata ɗauka akansu, har wajen sallar azahar tana a kwance, da kyar ta miƙe ta gabatar da salla tana zaune bisa dadduma, dabarar turawa Ikram text ya faɗo mata, sai ta miƙe da sauri ɗan har wani kuzari ta samu saboda a yau tana so Ikram da Shamsu kar suyi kwanan farin ciki, dadduma ta naɗe ta zari jakarta ta fice zuwa bakin titin layinsu shagon mai sayar da layin waya, ta sayi layin MTN sabo mai register kana ta dawo gida ta saka layin a ƙaramar wayarta sai ta soma rubuta tex ɗin, data gama tayi saving ta aje har sai da aka yi sallar La'asar kafin ta turawa Ikram tana dariyar mugunta.

Yau za a ci amarci da tashin hankali dan nasan Ikram ba tada sauƙi sai ta ɗaga masa hankali, Ni kuma haka nake so, kuma zan cigaba da tura mata saƙo yadda rikici zai cigaba da wanzuwa har sai Shamsu ya nima wacce ke tura sako, idan ya nima mu haɗu na bashi dama daga nan na shigar da nawa buƙatar, Wlh zan iya fasa auren Aminu In dai ya amince da aurena.

Cewar Najwa a zahiri kamar mai taɓin hankali, ɗan sosai shaiɗan ya ƙara samun gurbi a zuciyarta yana haska mata Shamsu yafi Aminu shine ya dace da ita a yanzu. Haka ta dinga saƙa da warwara har aka yi sallar magrib, tayi zaton Ikram zata kira layin amma shuru hakan yasa ta kashe wayar da layin ke ciki ta kunna asalin babbar wayarta data kashe ɗazun, ita kaɗai a gida kamar mayya, dan inna can zata kwana kamar yadda itama take kwana akan, tasan mazan gidansu sai dare yayi zasu shigo tunda ba abinci zasu samu ba a gidan, har aka yi isha'i tana a haka, data idar ne ta fita zuwa waje ta siyo biredi da ruwan bunu ta dawo ta haɗa tea mai kyauri ta sha ta kwanta, a haka har barci ya ɗauketa da tunani barkatai.

Shamsu da Ikram.

*Duk wacce ta karanta mini littafi bata biya ba, ta sani ta karanta da hakkina kuma In Sha Allah sai Allah ya saka mini.*
[4/22, 7:44 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

38.

Ikram da Shamsu.

Ya shigo da abokansa su uku falon yace su jirashi, sai ya isa bedroom ɗin Ikram akan ya kirata su gaisa amma sai ya samu ɗakin a rufe, ya buga bata buɗe ba sai ya shiga kiranta a waya yana ringing amma ba a ɗauka ba, ya shiga yi mata magana akan tayi haƙuri ta buɗe amma ta nuna tamkar bata cikin ɗakin, cikin sanyin jiki ya dawo gurin abokansa yana basu hakuri akan amarya ta ɓoye kanta, basu wani damu ba sun san ko wace amarya da kalan na ta salon dan haka suka yi masa sallama suka wuce, har mota yayi musu rakiya da suka wuce ya dawo ciki ya isa ɗakinsa ya watsa ruwa ya saka jallabiya kana ya ɗauki extra key a drower ya fito ya isa ɗakin Ikram yayi sa'a ta cire key a jikin ƙofa, yana sakawa ya buɗe ya shiga, Ikram tana ganinsa ta zabura ta miƙe tana cewa.

Karka kuskura ka matso kusa dani in ba haka ba zanyi maka abinda baka taɓa tsammani ba, Shamsu nayi dana sanin aurenka kuma kasa a ranka ba zaka taɓa samun abinda kake so a gareni ba, ka fita bana son ganinka.

Ta ƙare maganar a tsawace tana kuka ganin yana matsowa kusa da ita, tsananin mamaki yasa Shamsu kasa magana dan ya rasa ina maganarta ya dosa balle ya iya hasko inda matsalar take, cikin dakiya da danne damuwa ya soma cewa.

Haba amaryata ki kwantar da hankalinki ni babu abinda zan yi miki, yanzu ki zauna muyi magana.

Babu maganar da zan ɓata lokaci nayi maka domin ka gama ɓata rawanka da tsalle, na dai gaya maka baka isa ka samu abinda kake nima a guna ba, da zaka fita dana fi jin daɗi dan bana ƙaunar ganinka.

Shamsu yana shirin yin magana sai wayarsa da ya saka a haljihun gaba ta soma ƙara, sai ya ciro yaga Ibrahim ne ya ɗauka da sauri har suka yi magana kana ya kashe wayar yana duban Ikram.

Yaya Ibrahim da Anty Sameeha suna hanyar zuwa nan, duk da ban san dalilin zuwansu ba amma hakan yana da yanada alaƙa da wannan rikicin da kike yi mini, dan haka ki daina kuka koma miye gaskiya zata yi halinta In Sha Allah.

Yana gama faɗar haka ya fito daga ɗakin ya zauna a falo tare da dafe kansa da duk hannunsa biyu, damuwa sosai ya shiga kan yadda ranarsu ta farko a gidan aurensu ya kasance, yadda yasan Ikram tana sonsa ya tabbatar ba ƙaramin abu bane yasa ta yi masa haka, kuma yasan tana da tarbiyya musu bai taɓa shiga tsakaninsu ba, haka ya zauna zaman jiran isowar su Ibrahim. Itama Ikram zama tayi a bakin gado tana matsar kwalla dan ta rasa yadda zata danne halin da take ciki ta ɓoyewa Shamsu, shiyasa ta kasa controlling kanta kamar yadda Sameeha tace karta nuna masa komai ta bar komai a hannunta, haka kowannensu ya zauna cikin damuwa har zuwa sadda suka ji hon ɗin motar Ibrahim a gate, hakan yasa Shamsu yayi saurin fita lokacin mai gadi ya buɗe musu sun shigo, Ibrahim yayi parking suka fito Shamsu ya ƙaraso yana yi musu sannu da zuwa cikin ladabi, suka amsa kana suka shiga cikin falo suka samu wajen zama Sameeha da Ibrahim a kujera mai zaman mutum uku suka zauna, sai Ikram da fitowar ta kenan ta samawa kanta guri a kujera mai zaman mutum ɗaya, Shamsu shi kuma ya zauna a kujera mai zaman mutum biyu, nan Ibrahim ya soma magana yana cewa.

Shamsu ba ɓata lokaci za muyi ba saboda dare, ina so ka duba wannan saƙon kayi nazari akan waye ko wacece zata yi maka irin haka.

Yayi maganar yana miƙa masa wayar Ikram daya amsa a hannun Sameeha, Shamsu ya taso ya amsa ya koma ya zauna ya soma karanta saƙon cike da tsantsar mamaki a fuskarsa, ya ɗago ya kallesu bayan ya gama karantawa ya ɗaura da cewa.

Yaya ni ba ni da wani maƙiyi dana sani a zahiri da zai yi mini irin haka, ashe shine dalilin da ya sa Ikram ta rikice mini, Innalillahi wa inna ilaihir raji'un.

Ya ambata yana mai dafe kansa da hannu bibbiyu domin saƙon ya kaɗa shi sosai kuma bai ga laifin Ikram ba domin saƙone da yake da tashin hankali a ciki, musamman ita da take a matsayin matarsa da aka ɗaura aure yau yau, Ibrahim yace.

Shamsu kadai zurfafa tunaninka akai ƙila ka taɓa samun sabani da wani ko wata yace bari ya biyo ta wannan hanyar domin ya rama, abokin aiki ko budurwa, duk da ni ban yarda ka aikata ba saboda nasan tarbiyyarmu wlh ba zaka taɓa ɓata sunan ahalinmu ba wannan shirri ne dai.

A zabure Shamsu ya muskuta ya É—ago kai yana cewa.

Tabbas mace ɗaya ce nasan ƙila ta iya aikata haka saboda zafin da taji na auren Ikram da nayi, saboda budurwa ɗaya nayi a nan Kaduna sai Ikram dana aura yanzu, sannan ita wancen da kanta ta koreni tace ba zata iya aurena ba saboda banda kuɗi.

Nan ya kwashe yadda suka rabu da Najwa ya basu labari tas kana ya cigaba da cewa.

A zahiri na ɓoye mata asalina ne domin nasan zata soni saboda Allah sai kuma ta faɗi jarabawar ta nuna kuɗi take so, ta kuma sallameni da kanta akan karna sake zuwa gidansu. Dalilin da zai saka tayi mini wannan sharri saboda Ikram na aura, zata ga kamar nayi hakan ne domin na ƙuntata mata, kuma na soma soyayya da Ikram bansan alaƙarsu ba daga baya ne na fahimci kuna da alaka a Najwa.

Najwa!

Cewar Ikram da ƙarfi, Sameeha ma tace.

Najwa kuma! Najwa Tamu dana sani ko wata daban.

Ita dai cousin ɗinku wacce take a badarawa, na tabbatar bata san nine na Auri Ikram ba sai yau shiyasa ta biyo ta wannan hanyar dan ta ƙuntata mini, ƙila a ganinta na auri Ikram da gangan ne dan na bata haushi, wannan hasashena ne kuma bincike shine zai tabbatar da gaskiya, ita kaɗai nake zargi a yanzu.

Ikram yau tunyaushe ne baki ƙara ganin Najwa a gidanmu ba, saboda na tuna ban ganta ba tun yamma dan bada ita aka kawo mu gidajenmu ba.

Ai ni rabona da ita tun lokacin da aka fito É—aukar hoto dasu Shamsu suka shigo gaisuwar iyaye bayan É—aura aure.

Cewar Ikram tana yawo da idanunta kamar mai tunani, Ibrahim yayi murmushi domin shima zarginsa ya faÉ—a akan Najwa sai yace.

Da alama ita ce dan na tabbatar a wannan lokacin da muka shiga gida ta ga kaine mijin Ikram yasa ta bar gidan, kuma ta yi amfani da wannan damar dan ta lalata tsakaninka da Ikram, dan haka yanzu ta ina zamu tabbatar mu gano da ita É—in ce ta aikata haka.

Murmushi Shamsu yayi yana cewa.

Ku bani number É—inta yanzu na kirata da dayan layina da ba tada shi, yanzu gaskiga zata yi halinta.
Chapter 62 · 0% Book details