← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 103

Sashe 54

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda su Hajiya suka shiga yake cike da fargaba da addu'ar Allah yasa su bashi aurenta, bai taɓa sanin ya kamu da tsananin son Sameeha ba sai yau da yake fargabar rasata, Shamsu ma addu'a ya dage da yi akan Allah yasa su bashi Ikram duk da yasan har lokacin ba wani samun gurbi yayi a zuciyarta ba. Lokacin da su Hajiya suka fito duk suka shiga mota suka wuce, Ibrahim kamar ya tambayi ya suka yi amma sai ya kasa ya danne gani su Hajiyar ma shuru suka yi ba wani hira da suke yi har suka isa gida, suka zauna a falo Ibrahim da Shamsu ko wanne ya ƙosa yaji sakamakonsa sai zullumi suke yi, nan dai Hajiya Fati ta fara koro musu bayanin tun shigarsu har zuwa sadda aka tambayi su Sameeha, sai tayi shuru Hajiya ta ɗaura da bayani daga ƙarshe dai suka tabbatar musu da anbasu auransu sati mai zuwa za aje nima musu aurensu In Sha Allah, ba ƙaramin farin ciki suka yi ba kamma Ibrahim da keta jero hamdala har ya miƙe ya bar falon hamdala dake ambata, su Hajiya sosai suka yi mamakinsa sai kace bai taɓa aure ba Sameeha ce ta fari, Shamsu ma da farin ciki yabar falon ya wuce sashinsa dan ya sanar da Mahaifiyarsa da tun haɗuwarsu da Ikram ya bata labari, ko yau ma ya sanar da ita za aje tambaya ta taya shi da addu'a. Koda ya sanar da ita tayi murna tace zata fara faɗawa babanshi kafin su Hajiya su faɗa masa. A wannan dare duk gidaje biyun nan a cikin farin ciki suka kwana duk da Sameeha tana jin damuwa in ta tuna da Aminu da kuma kewar yaranta.

Zuwa Safiya su khairy sun samu labarin komai, farin cikin kamar zata yi hauka ashe yayansu kallonsu kawai yake shima ya hango dacewarsa da Sameeha amma ya basar kamar ba komai a ransa, a ranar da yamma saida taje gidansu Sameeha ta dinga farin ciki da zumudi, sai da Sameeha ta koreta gidanta dan ta isheta da surutun yayanta.

...

Tun ana gobe Asabar da iyayen su Ibrahim zasu zo aka sanar da su Umma, dan khairy ce ta bawa Hajiyarsu number ɗin umma, Hajiya da kanta ta kira umma suka yi maganar. Washe gari Asabar umma ta kira innar Najwa tazo da kuma 'yan uwanta dake nan kawo wanda suke 'yan uba suma ayi dasu su ta yata murna. Mutanen Zaria sun iso gidan umma wanda dama tuni ta sanar da dangin babansu Ikram, suma sun zo dan a gidan mutanen Zaria suka same su bayan sallar la'asar, Khairy dan ɗaurawa lamarin ita ta aikewa su Sameeha da snacks ɗin da zasu amsa baƙi, yaya Zaidu ya siya musu drinks, dan dashi ma aka zauna yin maganar. A takaice an bada aurensu tare da saka rana nan da wata biyu mai zuwa, Sameeha dubu ɗari biyu sadakinta Ikram kuma dubu dari uku saboda ita budurwa ce an bambanta, sannan dukiyar aure an bada dubu ɗari biyar duka su biyun wato milion ɗaya aka aje musu, anyi komai cikin mutunci da karamci ba wata matsala, mutanen unguwa an zagaye motocinsu dan harda dogawaran sarki aka zo dama su rawani, kuma a cikin manyan motoci suka zo abu dai sai wanda ya gani, sai shida suka bar gidan su Baffa har mota suka yi musu rakiya suka tafi kafin suka dawo cikin gida suna yaba karamci da taddako irin nasu, Nan suka kira umma ta fito da sauran 'yan uwa aka yi mata murna da addu'a kana suka danƙa kuɗin a hannun Zaidu yaje ya aje su a banki domin sun san shine jagoran kayan da za a siya musu. Sai bayan magrib kowa ya watse aka bar su umma da farin ciki, zuwa yanzu Sameeha ma ta saduda ta karɓi zabin da Allah yayi mata. Ikram sai yanzu ta ƙara yarda Shamsu ne zabin da Allah yayi mata, ashe babansa shine wazirin zazzau Bai faɗa mata ba, kuma Khairy ma bata faɗa musu ba sai yau suka san da haka, umma kuwa a ranar saida ta yi sadakar abinci mai yawa da suka dafa dan sosai take nunawa Allah godiya daya nuna mata wannan ranar.

****

Najwa.

Inna tana isa gida ta tare ta da zancen.

Inna wi ina kika je? ko maganar auren Sameeha ne ya taso dana ji kina maganar É—azu da baba.

Ai bama Sameeha ce kaɗai ba harda Ikram. Ai yau naga matanen masarauta naga inda arziki ke dukan dukiya. Sadakin Ikram dubu ɗari uku, Sameeha kuwa dubu ɗari biyu saboda bazawara ce, dukiyar aure da gaisuwa dubu ɗari biyar su duka, million guda aka danƙa musu.

Wani irin zabura Najwa tayi ta miƙe tsaye tana kallon inna tare da dafe kirji.

Inna kodai baki ji daidai bane, wai Sameeha dana sani da Ikram ne aka bada kuÉ—in aurwnsu har haka. Su waye zasu aura haka?

Ita dai Ikram ance É—an wazirin Zazzau ne, Sameeha kuma É—an uwan mijin Ikram ne dai, bamu san waye shi ba amma ance mai kuÉ—i ne, biki ma nan da wata biyu za ayi.

Innalillahi wa inn ilaihir raji'un, taya za a saka bikin haka? kenan sai an yi masu da kusan wata biyu kafin ayi nawa. A ina Ikram ta haÉ—u da É—an wazirin Zazzau? me yasa komai sai sun fini.

Najwa kina da hamkali kuwa kike wannan maganar? ai arzikin ko wani bawa yana goshinsa kuma matar mutum kabarinsa, kema ai ba ƙaramin mutum zaki aura ba tunda yana da rufin asiri.

Amma umma Ikram fa dana fita kyau ce zata auri É—an wazirin Zazzau, itama anty Sameeha da take bazawara kuÉ—in aurenta har ya fi nawa.

Saboda haka Allah ya tsara karma ki saka wannan a ranki shaidan ya samu girbi a zuciyarki ya saka miki hassada, bana son sake jin irin wannan maganar, kije ku duba abibcin can naji kamar ya fara kauri.

Najwa bata ƙara yin magana ba, dan ji tayi ƙirjinta yayi mata nauyi zuciyarta yana yi mata wani irin zafi, baƙin cikin da hassada ya rufe mata ido dan sosai ta kaɗu da wanda Ikram zata aura, na Sameeha bai wani dameta ba amma Ikram da zata auri ɗan waziri ta shiga gidan sarauta shine ya tsaya mata a ƙoƙon zuciyartw, sai take ganin Ikram ta danne ta tayi mata nisa dan bata isa ta kama ƙafarta ba ita da zata auri Aminu mijin yayarta daya saka, kuma yaushe tayi mata gorin aure gashi Allah ya nuna mata har zata rigata auren ma, kuma da dan gidan sarauta saurayi mai jini a jika, jikinta ne ya ɗauki rawa zazzaɓi kawai taji ya kamata, bata san kuka take yi ba sai da ta shafa kuncinta, abincin da bata duba ba kenan ta wuce ɗaki ta kwanta tana rawar sanyi, sai ta fashe da kuka tana ganin ita sam ba tada sa'a a duniya.
[4/16, 7:51 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

34.

Ƙaurin da inna taji na abincin dake wuta yasa tayi saurin fitowa daga ɗaki tana sababi, ta isa da sauri ta sauke ta mayar da tukunyar holoƙo ta saka ruwan wanka kana ta nufo ɗakin Najwa dan tayi mata faɗa akan ƙin sauke abincin da bata yi ba, Najwa tana jin motsin zuwan Inna yasa ta danne kukanta ta bawa ƙofa baya, Inna ta ce cikin faɗa.

Wani irin shirme ne Najwa kike yi, nace ki sauke abinci amma kin samu guri kin kwanta, kin ma yi sallar magriba kuwa?

Kaina ke min ciwo tun ɗazu da rana, da yamman nan kuma zazzaɓi nake ji da kyar ma na ɗaura girki, ɗazun mantawa nayi ban faɗa miki ba.

Assha yanzu haka maleria ce, Allah ya sauke, bari Junaidu ko Sadiq su shigo sai a samo miki magani kisha, amma ki tashi kiyi sallah in baki yi ba.

To Najwa tace mata, inna kuma ta juya zuwa ɗakinta sam bata gane halin da Najwan ke ciki ba, har zuciyarta ta yarda da ba tada lafiya ne tunda gashi ya nuna ma a muryarta da yayi sanyi. Najwa miƙewa tayi ta zauna tana jin wani tuƙuƙin baƙin bakin ciki yana ratsa illahirin zuciyarta da gabbai, sai ta miƙa hannunta gefen gado data aje wayarta ta dubo number ɗinki Hauwa ta danna mata kira, bugu ɗaya ta ɗauka Hauwa tana cewa.

Amarya kinƙi ambato muna zancen ki sai ga shi kin kira, muna nan muna ta hada hadan haɗa akwatinki, kin san ke twmu ce komai muna su muyi shi waja wajaba laranta.

Hauwa ta kai aya a maganarta tana saurare me Najwa zata ce mata, Najwa sai da ta lumshe ido kafin ta ja fasali tace cikin sanyin murya.

Anty Hauwa kin samu labarin auren Sameeha da ƙanwarta Ikram da za ayi, ta samu miji ɗazun nan aka kawo kuɗin aurensu, sadakin Sameeha dubu ɗari biyu Ikram kuma dubu ɗari uku, abu kamar a film.

Kutumelesi au Sameehan har ta samu miji? Ashe duk son da takewa Aminu ƙarya ce tunda gashi ko shekara bata yi da fita ba zata yi aure, to su waye zasu auresu haka? naji kin ambaci kuɗi masu yawa na sadaki.

Ikram dai ɗan wazirin Zazzau zata aura Sameeha ce dai bamu sani ba amma ance mai kuɗi ne kuma ɗan uwan mijin Ikram ne, abu dai wlh kamar almara, nima nayi mamakin wannan daraja da suka yi musamman Ikram da take baƙa ba ta da fasali.
Chapter 54 · 0% Book details