← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 103

Sashe 79

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Najwa tunda taji Anty Saleema tace zata je da ita kano sai taji ɗan sanyi a ranta, dan yanzu abinda tafi so shine tayi nesa da inda take da kowa ma ƙila hakan zai saka ta samu sassauci daga halin da take ciki, sai kawai ta miƙe cikin zafin nama duk da tsamin da jikinta yayi na dukan jiya da yau, amma haka ta soma haɗa kayanta dan ko kayan akwatinta a yanzu bata buƙatarsu, kuma kayanta na gida ba a riga an kai mata ba dan haka cikin ƙanƙanin lokaci ta gama komai ta zura babban hijab ɗinta ta saka safa da niƙaf dan so take tayi ɓadda kama yadda babu wanda zai ganeta saboda tana kunyar mutane su ganta kar suyi mata dariya, a dalilin aurenta ta wulaƙanta mutane da yawa ta rabu da ƙawayenta na kan layinsu da yawa a ganinta ta wuce hulɗa da ƙananun mutane, ta jawo trolley ɗin kayanta tsakar gida ta tsaya tare da ɗaga niƙaf ɗinta ta rungume hannu tana jiran fitowar Saleema dan tasan ba zata ƙara kwana a gidan ba saboda itama akwai zuciya, ilai fitowarta da minti goma sai gata ta fito da jakar kayanta tana kwalawa inna kira akan ita zata wuce, ganin Najwa a tsaye da shirin tafiya yasa ta saki murmushi.

Kunga 'yar halak harta kimtsa, aiko dama yanzu nake shirin yi miki magana ki shirya ashe harma kin fini zaƙuwar mu tafi, to In Sha Allah alkhairinki yana Kano sai mutane sunga irin wanda zaki aura, yadda kike da kyau da hasken fata mazan Kano ba ƙaramar ƙaunar farar mace suke yi ba.

Hmmm ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta, ni sai dai nayi muku fatan ku sauka lafiya amma in har Najwa bata sauya halinta ba to wlh kema sai ta gundureki. Najwa ina miki faran shiriya kuma In Sha Allah addu'ata kenan kullun dan hannu bai taɓa ruɓewa ka yanke ka yar, Saleema ki gaida maigidanki da abokan zamanki.

Cewar inna data fito daga ɗaki cike da ƙarfin guiwa dan ba ƙaramar farin cikin tafiya da Najwa tayi ba, Saleema ta taɓe baki tana cewa.

Ai dama nasan bakinki É—aya da yaya, ko min abinku Najwa dai In Sha Allah sai ta zama zakaran gwajin dafi.

To saleema ai banyi miki musu ba Allah ya sauke ku lafiya.

Inna ta faɗa tana wucewa gurin kitchen dan ta ɗauki kofin Baba da aka wanke. Saleema bata ce komai ba ta gyara mazaunin gyalenta ta yi gaba Najwa ta sauke niƙaf ɗinta ta bi bayanta da trolley suka fice daga gidan, suna fita sauran 'yan uwa suka shiga zancen tafiyarsu Inna tana ji bata saka baki ba dan fatanta ma kowa ya watse ya bar mata gida ko zata shaƙi iska mai daɗi saboda abinda ya faru har yanzu baisa ta samu natsuwa mai kyau ba.

Najwa suna fita suka samu napep ya wuce dasu tasha ba ɓata lokaci suka samu motar Kano suka shiga, Saleema ta biya kuɗin, mota tana cika suka kama hanya, sai a lokacin ne Najwa ta soma fidda zafafan hawaye taji duniyar ta yi mata kamun kazar kuku, tana gani ta rasa komai duk wani burinta ya ƙare a lokaci guda, dana sanin yadda ta kamu da son Aminu ta soma yi, ba wai dan tayi nadama ba sai dan dana sanin akan baida lafiyar da zai iya ɗauke nauyin duk Sha'awarta data jima tana yi akansa, ashe duk wani tanadi data yi masa aikin banza tayi, ji take duk abinda ya sameta Sameeha ce sila da bata dawo taje gidanta ba da duk haka bai faru ba, shiyasa take jin itace babbar maƙiyiyarta sai Ikram sannan Aminu da kuma Nafeesa data faɗo mata a rai, nan take ma ta tuna da tona mata asirin da tace zata yi domin tana so yadda ta rasa komai ta muzanta to itama Nafeesa ta shiga halin ƙunci, domin itama ta taka muhimmiyar rawa wajen sata yin wasu abubuwan, sai kuma su Binafa da suma ta yi alwashin tona musu asiri kowa kwaɓarsa sai tayi ruwa, a sannan ne ta saki murmushi wanda yake cike da tarin mugunta, ta ciro wayarta dake jaka sai ta tuna da ta ci screen, sai ta kalli Saleema tana cewa.

Anty dan Allah ara mini wayarki akwai abinda nake son tura wa yanzu.

Ba musu ta ciro wayar a jaka ta bata, Najwa ta saka sabon sim ɗin data yiwa Ikram text lokacin bikinta a wayar Saleema, sai ta kunna data ta sauya WhatsApp ɗin Saleema ta mayar da nata Number ɗin, dama duk numbers ɗin da take so tayi savimg a nan, dan haka cikin kankanin lokaci ta rubuta saƙo kamar haka ta turawa number ɗin yayan Nafeesa da take cewa.

Ɗan uwa ina son in sanar da kai wani lamari wanda nake fatan mu samu masalaha a cikinta, nine Saurayin Nafeesa wanda muka samu matsala da ita muka rabu, dalilin akwai wani sirri da muka rufe wanda ya dameni sosai shiyasa na buƙaci na sanar da kai ko hakan zai sa mu samu maslaha. A lokacin da take zuwa Poly wani tsautsayi ya faɗa a tsakaninmu har na kusanceta sai kuma ciki ya samu, to gaskiya na shiga damuwa sosai wanda yasa nace dole sai an zubar saboda mu rufawa kanmu asiri, to shine ta samu cousin ɗinku Binafa suka san yadda suka yi aka zubar da ciki sai asirinmu ya rufu, daga nan kuma muka cigaba da mu'amalarmu amma tana yin planning yadda ciki bai sake samuwa ba. Ita Binafa ta rufa mana asiri muma mun rufa mata saboda munyi ban gishiri ne in baka manda, domin itama cikakkiyar 'yar lesbian ce wacce har aure tayi da wata ƙawarta Hanan a ɓoye, abubuwa dai da yawa sun faru kuma suna kan faruwa, to gaskiya wannan dalilin yasa naji bazan iya auren Nafeesa ba saboda zargi da ya shiga tsakanimu, amma bayan 'yan kwana biyu naji sam banyi mata adalci ba dana rabu da ita sai dai bazan iya cigaba da ɓoye wannan sirrin ba dole sai na fito na faɗa, wataƙila zamu samu maslaha ku yafe mini.

Ta tura masa dan dama a ranar da aka kaita kafin ta yiwa Nafeesa magana lokacin da zata cire sim ɗinta ta ɗauki number ɗinsa a wayar Nafeesa tayi saving a ƙaramar wayarta. Najwa nan take taga yayi marking sai ta kashe data ta shiga hotunan Saleema tana kallo tana jin farin ciki a zuciyarta na tona musu asiri.

Bayan awa guda ta ƙara kunna data sai ga sakon yayan Nafeesa kamar haka.

Innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Amma Hamisu kaci amana bamu zaci haka daga gareka ba, ai ko tunda abinda ya faru kenan dole ma ka aureta dan baka isa ka ɓatatq ba kace zaka rabu da ita, yanzu ina hanyar zuwa gida za ayi duk wacce za a yi ma.

Najwa tana gama karanta haka ta saki shu'umin murmushi kana ta kuma kashe data ta kwantar da bayanta a jikin mota ta lumshe ido tare da jin wani farin ciki yana ratsata akan abinda ta aikata, tace a ranta.

Yadda na muzanta na rasa farin ciki kuma sai kun rasa shi wlh, saboda tare daku muka aikata komai, dole ko wanne ya amsa nashi rabon baƙin cikin.

A haka ta dinga tunani har barci ya É—auketa, sai da Saleema ta tasheta tana cewa.

Yadda kika samu barcin nan ya nuna alamar zaki samu natsuwa a garinmu, na tashe ki ne saboda mun kusa sauka tun É—azu muka shigo Kano.

Wlh da yake banyi barci mai daÉ—i ba shiyasa ga gajiyar biki dana duka.

Ta faÉ—a cikin sanyin murya.

Allah sai ya saka miki In Sha Allah.

Saleema ta faɗa tare da yin shuru tana duba agogon hannunta. A takaice sun isa gida gurin ƙarfe uku na rana suna shiga yaran Saleema suka rugo suna yi musu oyoyo da uniform ɗin makaranta a jikinsu, suka amsa trolley Najwa suka wuce part ɗinsu, sai da suka sha ruwa suka zauna a cushing tana tambayar babbar 'yarta Ikilima me suka dafa? tace taliya ce dafadukan manja kuma ya ƙare, sai tace ta shiga kitchen ta dafa musu indimie guda Huɗu dan da yunwa suka shigo, tace to kana ta wuce kitchen, a lokacin ne ɗan kishiyarta ya shigo yana ce mata babansu yana kiranta a ɓangarensa, tace to kana ta miƙe ta mayar da mayafinta tabi bayan yaron. Babban gida ne da yake da part huɗu nata ɗaya sai na kishiyarta uwar gidan malam sai kuma na amaryarsa da bai jima da aurenta ba sannan nashi ɓangaren da yake ganawa da mutanensa, sannan kuma turakarsa ne duk me girki can take samunsa. Saleema tana shiga ta sameshi zaune a dadduma ya jingina da jikin cushing da fara'arta ta ƙarasa ta zauna a carpet tana gaishe shi ya amsa fuska a haɗe tare da cewa.

An sanar dani kin dawo tare da baƙuwa shine na kira naji dalilin zuwa da ita ba tare da kin sanar dani ba.

Wlh zuwan bana shiri bane shiyasa na tawo da ita, dama nace in muka ƙaraso sai na sanar da kai.

Ke bana son shashanci taya zaki yi gaban kanki saboda baki ɗaukeni a bakin komai ba, Saleema na fa gaji da halinki duk cikin matana ke ce mai taurin kai kike bani matsala, banda ina duba darajar yaranmu da tuni na rabu dake wlh, to ina so ki tattarata ta bar mini gidana tun kafin dare yayi, dan kinsan bana karɓan baƙon da ba a sanar dani ba.

Subhanallahi haba malam, meyasa zaka yanke mini hukunci irin wannan ba tare da kaji uzuri na ba kuma...

Ki tashi ki bar mini falo tun kan ki harzuƙani, na kula ke zuma ce dole sai da wuta, in ba raini ba taya zaki yanke hukunci baki sanar dani ba, to na baki umarni ta bar mini gidana yanzu yanzu.

Yayi maganar a tsawace jikin Saleema yana rawa ta miƙe saboda tana mugun jin tsoronsa dan ba haka ya barta ba, da tashin hankali ta baro sashinsa da tunanin ina zata kai Najwa ta zauna kafin ta shawo kan malam ya haƙura.

*****

Nafeesa.
Chapter 79 · 0% Book details