Sashe 45
Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wacece ke magana?
Dam ƙirjinta ya buga dan ta gano yanayin muryansa fuskarsa a ɗaure yake, kuma kenan baiyi saving number ɗinta ba da Hauwa tace ta tura masa tun kwanaki.
Idan ba ki da abin cewa zaki iya kashe wayar dan ba ni da lokacin ɓatawa.
Ya faÉ—a a hasale, Najwa ta daure tace.
Kayi hakuri na kiraka ne mu gaisa nice Najwa, Anty tace mini baka da lafiya shiyasa na kira nayi maka ya jiki.
Murmushi yayi har hakoransa suka fito, wato Hauwa ta nan ta hudo kuma? tunda yaƙi kiran Najwan ya kuma daina ɗaukar wayarta shine zata saka ta kirashi.
Ayya nagode, da yake data tura mini number É—inki ban samu damar saving ba saboda busy, ya mutanen gidanku.
Lafiya lau.
To madallah, da akwai wata matsala ce?
Babu amma dan Allah ina so ka riƙa kirana dan mu saba.
Karki damu zan kira, ki tura mini account number ɗinki, sannan ki zauna kiyi lissafin abinda kike buƙata na shirye shiryenmu nan da kwana biyu sai ki faɗa mini in san abinda zan tura miki.
To tace masa tana godiya, daga haka yace shi zai kwanta suka yi sallama ta kashe wayar tare da tura masa account number ɗinta, yana gani ya tura mata dubu talatin na kati, sai ya gyara kwanciya ya kashe wayar yana tunanin yadda zaman wannan auren zai kasance a tsakaninsu, shi baya sonta bayi da lafiya amma anya bazai cutar da yarinyar mutane ba? Wani ɓangare na zuciyarsa ya faɗi haka, yana gudun kar son ɗaukar fansa ga Hauwa ya jefa rayuwar yarinya ƙarama a gagari ya mayar da ita ƙaramar bazawara tunda yasan zaman ba zai ɗaure ba, sai yake ji kamar yace ya fasa kawai dan baya son ya cutar da kowa, amma in ya yuna matsalolin da Hauwa ta kunna masa Abin da ciwo kuma baya jin zai iya yafewa ba tare daya rama ba, kuma wannan auren ne kaɗai hanyar da zai ƙunsa mata baƙin ciki, da wannan tunanin barci ya ɗauke shi.
Washe gari suka hau jirgi suka dawo Abuja, da yamma lis Aminu ya bar Baba Saude da yara ya kamo hanyar Kaduna dan yin magana da Hauwa.
****
Najwa da Hauwa.
Tun da Hauwa ta sanar da ita ta bashi number ɗinta zai kira take ta zuba ido har aka shafe sati ba labari, hakan ya fara damun Najwa take ganin wannan auren anya ba zai zame mata damuwa ba tunda alamu ya nuna Aminy baya sonta, sai yanzu take tunanin kila in ya ganta yace ma ya fasa tunda yasan ita 'yar uwar Sameeha ce, sai duk ta fara jin ta sare da alama rijiya ta bada ruwa amma gugu ya hana. Shiyasa ta shirya musamman taje gidan Hauwa tana yi mata ƙorafin Aminu bai kirata ba ta ɗaura da cewa.
Yaya koda bai zo ba ya kamata ya riƙa kirana a waya dan mu saba, amma shuru fa har yau bai kiraba da sunan kuma ina matar da zai aura, anya zan iya kuwa?
Haba Najwa sai da aski yazo gaban goshi zaki nima sarewa, ya sanar dani bayi da lafiya shiyasa bai kira ba, yanzu ga number É—insa ke ki kirashi kiyi masa ya jiki na tabbatar daga nan zaku cigaba da yin waya.
Hauwa ta ƙare maganar tana miƙa mata wayarta akan ta ɗauki number ɗin Aminu, Najwa ta karɓa ta saka number ɗin a wayarta, nan dai Hauwa ta cigaba da rarrashinta a haka suka rabu ta bar gidan. Ita kuma Hauwa tunda Najwan ta zo tayi mata korafi taketa kiran Aminu yaƙi ɗagawa, hakan yasa ta yi fushi tare da kiransa da wayar yaronta koda ya ɗauka ta rufeshi da faɗa shine ya bata haƙuri akan da sun dawo daga Ilori zai zo Kaduna ya sameta.
Najwa sai da ta kwana biyu tana taraddadin kiransa gudun kar ya wulaƙantata, Nafeesa ce ta ƙara mata ƙarfin guiwa akan ta ɗaure ta kira dan yanzu fa sun kusa zama ɗaya, ita ta sauke nata girman kan ta kira shi su daidaita, sai gashi ta kira shi kuma bai yi mata wulaƙanci ba sunyi magana, duk ba wa wani hira mai daɗi suka yi ba amma Najwa taji farin ciki, ƙarin murnanta yadda ya turo mata dubu talatin wai na kati, nan ta shiga hango ashe ba ƙaramin kuɗi yake sakarwa Sameeha ba, lallai in ta aureshi zata tara kuɗin da har sai ta siya gida dan ba zata kashe su a banza ba dole ne ta mayar da hankali ta kwashi rabonta, a ranar tayi barcin farin ciki. Da safe saida ta faɗawa inna kuɗin daya tura mata, dan koda yaushe cikin yi mata ƙaryan suna yin waya ne, wanda sai jiya ne ta samu damar yin magana da shi, sai da ta turawa Nafeesa duby biyu a cikun kuɗin dan ta shaida, nan suka dinga murna akan tayi miji wanda hannunsa a buɗe yake ba ikin na 'yan dembe ba.
Aminu bayan sallar Isha'i ya sauka a Kaduna, da yake gidansa ya wuce sai da yayi wanka ya huta, wajen tare da rabi na dare ya bar gidansa ya wuce wani restaurant yaci abinci kana ya biya babban gida, ba karamin farin ciki suka yi ba da suka ganshi, sai dai ramar da yayi ya É—aga musu hankali nan suka rufeshi da faÉ—a akan meyasa bai sanar dasu ba bayi da lafiya, ya basu hakuri akan ma ya samu lafiya yanzu sosai, nan suka cigaba da bashi shawara akan ya kula da kansa sannan suka É—aura da maganar aurensa, yayi musu godiya akan ja gaba da suka yi kan maganar. Sai wajen sha É—aya suka rabu ya wuce gida.
Da safe wajen tara ya isa gidan Hauwa tana ganinsa ta saki fuska tana murna da ganinsa, dan tasan kuɗi yazo, dama tana cikin talaucinsu yadda rayuwa tayi tsada hannu baka hannu kwarya ake, ya zauna a falonta suka gaisa sai suka ɗaura da zancen bikin, yace ta yi lissafin kayan da za a siya sai ya tura mata kuɗin, har yake faɗa mata Najwa ta kirashi, ba ƙaramin daɗi taji ba, ba dan kar kwaɓarta tayi ruwa ba da tace taje gidansu Najwan suyi hira, amma tsoron abinda zai je ya dawo yasa ta yi shuru, ya jima suna hira daga bisani yace a ranar zai koma Abuja dan jirgin ƙarfe biyu zai bi, kuma bavdan yana cikin uzuri ba daya je yaga matar fata zaɓa masa, da sauri tace.
Karka damu ko wayar dai in kunayi ya wadatar, in kazo nan gaba kwa gana dan kar a katse maka hanzari.
Yaji daɗin yadda ta faɗa dan shima bawai dan yana so yaje ba ne yace mata haka, sai dan taga ya bada kulawarsa akan zaɓinta, daga bisani suka yi sallama ya tafi. Ƙarfe biyu yana yi da mintuna jirginsu ya tashi zuwa Abuja, driver ɗinsa shima ya tafi da motar zuwa Abujan.
Sameeha..
[3/2, 9:18 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*
29.
Sameeha.
A hankali Khairy ta cigaba da shiga jikinta wanda a cikin wata guda da haɗuwarsu ta zo gidan ya kai sau biyar, tun su umma suna ɗari-ɗari da ita har suka sake suna ganin so gamon jini ne dalilin 'yar uwarta data rasu take yiwa Sameeha ƙauna, zuwanta na ƙarshe data yi shi ne tazo tare da yaranta sun dawo hutu dan har sun koma makaranta, tun rana suka zo tare da kayan ciye ciye data yi musu samosa da cake da kuma kunun zaki wannan musamman ne na umma, sai da suka kai dare wato suka ci tuwon dare a gidan bayan sallar isha'i suka tafi, wanda a lokacin saura sati guda walimar ƙaninsu da take ta mitan Sameeha taje mata, ita dai da to ta bita dan ta san ba zata wani je ba tunda ita taji zata iya jela zuwa nan gidansu ita ko ba zata wani shige mata ba dan wutsiyar raƙumi yayi nesa da ƙasa wato rayuwa ake na kwarya tabi kwaya, tana tunanin zuwa ayi mata wulaƙanci tunda da yawan masu kuɗi basa so ana rabar su, sannan ba dukansu bane masu sauƙin hali da sauƙin kai irin Khairy, shiyasa tace ba zata ba kowa ya zauna a mazauninsa ta dai amsa mata kawai zata ne. Duk da a 'yan kwanakin nan data zo ta haɗata da Hajiyarsu sun gaisa sannan ta haɗata da yayarta Aisha da take Yobe, da kuma mijinta shima ta haɗasu sun gaisa wanda har wautar ta ta gani da tace zata gaisa da mijinta, tana mamakin yadda Khairy ta ɗauketa a zuciyarta yadda ta saki kanta da kuɗinta ta nuna sun zama ɗaya, sam bata kyamarsu komai ta samu a gidan ci take yi, tun suna ɗari ɗari har sun sake mata, umma ta ɗauketa 'ya kamar yadda take kiranta da umma. Sameeha ta fito daga ɗaki riƙe da plate ɗin shinkafa da wake da ta yi musu mai da yaji, ta aje akan tabarma tana cewa.
Umma gashi bari na dauko latas dana yanka mana Allah yasa baiyi sanyi ba a fridge.
To Allah yasa, kin san dai ina fama da haƙori in yayi sanyi ba zai taunu mini ba.
To umma bari na watsa masa ruwan É—umi na san zai rage zanyi.
Ta faÉ—a tana koma ciki ba jimawa ta fito da shi ta isa kichen ta zuba masa ruwan É—umi ta juye a matsami ta kawo ta ajiye, ta zauna ta fara juya gefenta da hannu dan tare da umman zasu ci.
Hannu kuma zaki saka?
Yau so nake nayi mata cin ƙet umma, kin san ina son mai da yaji.
Kice kawai kin mini wayo zaki fini ci.