← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 103

Sashe 51

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Afwan yau aiki nasha kunsan ana ta shirin tarban Ramadan Allah yasa muga farko da ƙarshensa lafiya. Yasa mu kasance cikin 'yantattun bayi*
_Mun kusa tafiya hutu sai bayan sallar In Allah ya kaimu zamu cigaba. Naso na gama kafin azumi amma bazai yiwu na guntule labarin ba, dan akwai abubuwan daya kamata a bisu daki daki._
[3/10, 8:45 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

32.

Su Najwa sai da suka zauna a kan tabarma dake shinfiÉ—e a tsakar gida kafin suka gaishe da Sameeha ta amsa fuska sake kana ta É—aura da cewa.

Amarya ce a gidanmu, yasu inna.

Lafiya lau, dama na zo ne muyi shawarar ankon da zamu fitar.

Allah sarki ai da kin fitar mana da ko wani iri ne Najwa. Ga atamfofi nan masu kyau.

Duk da haka anty ai mai shawara aikinsa baya ɓaci.

Cewar Najwa tana 'yar dariya, Sameeha tace hakane kana ta miƙe daga haɗa wutar gawayin da take yi ta ƙaraso ta zauna a tabarman, Najwa tana tambayar umma Sameeha tace tana barci, kana ta ɗaura da cewa.

To ke wanne kika ga ya dace a fitar? sai a fidda mai sauƙi saboda yadda rayuwar nan ta zama, Ikram ko ya kika ce.?

Anty kunfi kusa duk wacce aka fitar iyaka namu yi ne.

Ikram ta faɗa tana cigaba da wanke wanke. Najwa ta taɓe baki.

Rabu da ita Anty Sameeha ita wannan bama ta cikin sahun mutanen da suke yi mini murna, tunda na shigo take wani shan ƙamshi kamar na kashe mata wani.

Hmmm ke dai da Ikram zanga ran da zaku daina wannan rigimar.

Sameeha ta faɗa tana murmushi sai Najwa ta miƙa mata wayarta akan ta ga wacce ta fitar dan tuni suka maga zaɓar wacce zasu fidda ankonta ita da Nafeesa, koda Sameeha ta gani ba wani kyau tayi mata ba amma sai tace tayi kyau a fidda ita ɗin kawai, nan dai suka ɗaura da hira daga bisani Najwa tace zasu tafi dama maganar ya kawo su, Sameeha tace su tsaya a ɗaura abinci suci, suka ce sauri suke yi zasu biya wani guri, sai suka miƙe Sameeha ta koma gurin haɗa wutarta tana cewa su gaida Inna, Najwa tace.

Zata ji, dan Allah anty ki bani aron wannan silifas É—in kafarki nawa gurin sauka a napep ya tsinke.

Ayya to Allah ya kyauta, Ikram ta baki nata dan wannan kamar zai miki yawa.

A'a naki nake so dan wlh Ikram ba bani zata yi ba yadda take kullace dani. Banma son nata.

Ta faÉ—a da sauri tana ya mutse fuska, Ikram ta dalla mata harara.

Dama ba baki zanyi ba sai dai ki taka naman ƙafarki mara mutunci.

Sannu mai mutunci duk baƙin cikinki sai dai na rigaki aure, dan naga alama ke sai an haɗa da addu'a kafin zaki samu mashinshini.

Ikram ta miƙe a fusace zata zo ta bata Amsa Sameeha ta dakatar da ita.

Koma ki cigaba da aikinki, Najwa bana son irin wannan rashin jituwar dake tsakaninku, kufa 'yan uwa ne meyasa kuke haka? In Sha Allah zan haɗaku da yaya Junaid da kuma Zaidu su haɗaku bana son sakarci, zoki amsa takalmin ku wuce tun kafin raina ya gama ɓaci.

Kiyi hakuri anty, Ikram ce take jan rigima dani dan nace bazan auri Zaidu ba duk ta bi ta tsangwame ni, bayan shi tuni ya bar komai ya wuce.

Magana dai ta ƙare bana son rikicin nan.

To Anty nagode idan na samu lokaci zan kawo miki takalmin.

In dai silafas ne Najwa ki barshi kawai kin ƙara na aikin gida.

Cewar Sameeha ta cire mata takalmin ta koma ta ɗauki na umma ta saka sai ta wuce ta ɗaura ruwa akan gawayin data haɗa, Najwa ta ƙara yi mata godiya ta saka kana ta ɗauki takalmanta a hannu suka wuce suna cewa in umma ta tashi a gaisheta, Sameeha tace to, bayan sun fita ta rufe Ikram da faɗa akan ta daina biyewa Najwa tunda ta girme mata.

Amma anty kina ji tana jifana da gorin aure, wlh maganar ta ƙona mini rai banso kika hana ni bata amsa ba.

Eh duk da maganar ba daÉ—i saiki rabu da ita, kuma yanzu lokacin ta ne dole zata rika sakin magana tunda ba hankali ne da ita ba, Allah yasa in anyi auren ma ta natsu.

Cewar Sameeha, Ikram dan takaici bata ƙara magana ba ta cigaba da aikinta. Ana kiran sallah azahar Umma ta farka daga barci tare da wani irin rikitaccen mafarki, ta yi addu'a kana ta sauko daga gado ta fito waje ta hango Sameeha tana jajjage a turmi ga Ikram data gama wanke wanke zaune a tabarma suna hira, Umma ta ce.

Sameeha zo nan na aike ki. Ikram jeki karɓeta jajjagen.

Sameeha ta saki jajjagen ta iso gaban umma da fuskarta ke ɗauke da alamar barci. Ta miƙa mata ɗari biyu.

Jeki gidan Tani mai kuli ki siya kuli na É—ari biyu, sai ki biya makaranta Malam Madu mai almajirai ki bayar sadaka.

To umma amma da Ikram taje da kanta ni sai na ƙarasa girkin.

Kinsan halinta in na aiketa sai ta biya gidan ƙawarta Zainab kafin da dawo sai anta kiranta a waya. Ki je kawai ki siya ki kai nasan ba zaki ɗauki lokaci ba

To Sameeha tace sai ta shiga ɗaki ta ɗauko hijan da wani takalmi plat shoe ta saka ta wuce aiken umma. Ita kuma Ikram ta cigaba da jajjage dan taliya za suyi da moyar manja na jajjage, umma ta dauki buta ta shiga bayi kana ta fito ta zauna a kuejra ta fara alwala, nan Ikram ta bata labarin zuwan du Najwa da kuma baƙar maganar data gaya mata, ta ɗaura da cewa.

Allah umma ni ko aurenta ba zani ba.

To ke banda abinki Ikram meye abin fushi, kisan Najwa da shirme dan ba a yiwa mace gorin aure domun komai lokaci ne, ina ce yanzu saura wata iyar to ba abin mamaki bane a wurin aure kafin nata auren ki rigata. Ni bama wannan ba lamarin Sameeha ne ke damuna É—azun mafarki da ita nayi mara daÉ—i shiyasa nace taje ta yi sadaka da hannunta ina fatan duk masifar dake bibiyarta Allah ya kareta, albarkacin wannan sadaka data bayar da hannunta domin sadaka tana maganin musifa.

Allah ya kyauta ya karemu daga dukkan sharri, In Sha Allah ba abinda zai faru sai alkhairi, mafarkin bazai taɓa zama gaskiya ba da yardan Allah.

Allah yasa haka, sannan karki ƙara biyewa Najwa, na faɗa miki ba tun yau ba kin girme mata kamata yayi ki fita hankali.

To umma zan kiyaye, daga haka umma ta miƙe dan ta kammala alwalar ta wuce ɗaki Ikram kuma ta ɗaura sanwar miya. Sameeha ba jimawa ta dawo gida tace tayi sadakar kana tayi alwala ta wuce ɗaki dan ta gabatar da sallar azahar.

*****

Najwa.

Suna fita ta sheƙe da dariya kana ta zame takalmin ta mayar da nata tana jan ƙafa har suka samu abin hawa suka kira Binafa akan sun samu sa'ar ɗauko takamin dama dabarar da ta yi gurin samu, tace su wuce gidan malamin zata biyo su haɗu a can. Koda suka isa bokan ya amsa warin talamin ƙafar hagu ya miƙawa Najwa wani turara akan duk ranar juma'a in zata kwanta ta shafe jikinra dashi ta kwana ba kaya, har ya ƙare sauran aikin shi zai yi a gunsa kafin zuwan bikinsu Aminu sai fara rawar ƙafa a kanta, sannan kuɗin aikinsa dubu ɗari da hamsin, a nan ne idon Najwa ya raina fata tayi tsuru tsuru dan bata san inda zata samu ciko ba, kafin ta tawo daga tunanin ina zata samu kuɗin taji Najwa tana cewa.

Bani account number in tura maka.

Nan boka ta faɗa mata nan take ta biya kuɗin tana kallon Najwa. Idan buƙatarki zata biya to tamkar namu ne ta biya. Allah dai yasa ki samu Aminu a tafin hannunki.

Najwa ta washe baki tana zambaɗa mata godiya sosai ta yaba da kirkin Binafa banda tana lesbian halinta mai kyau ne wannan ne naƙasunta, sai da suka fito tukuna kafin Najwa ta bata dubu ashirin daga kuɗin da Aminu ya bata, tace ba zata amsa ba ta rike tayi wasu buƙatunta, a haka suka wuce gidansu Nafeesa.

****

Ikram

Da dafe Shamsu ya zo hira dan haka cikin gida Ikram ta shigo dashi ta aje musu kujera ƙanana guda biyu a nan bakin gate suka zauna, dan dama bata hira a waje, nan suka gaisa kana ya tambayeta gajiyarsu tace yabi lafiya, daga nan ya fara da cewa.

Sunana Shamsuddeen kuma ni yaron yayan mamansu anty Khairy ne, a gidan nake zaune ina kula da wasu harkokin yaya Ibrahim.

Allah ya taimaka.

Ameen amma nan gidanku ne ko gidan yayarki?

Gidanmu ne ita aurenta ya mutu.

Allah sarki Allah ya bata na gari.

Ta amsa da amin kana suka cigaba da hirar duniya, da kuma tambayar ta makarantar da take zuwa, sai ta faɗa masa, daga bisani Shamsu ya ƙara da cewa.

Yadda kuke da natsuwa da hankali ga kyau masha Allah nayi mamakin abinda zaisa mijin yayarki ya saketa, dan a tsakanin jiya da yau dana wayeku na hango tsantsar tarbiyya a tare dake kuma nasan itama haka take.

Wlh kasan aure raine dashi kuma mutum bai taɓa gujewa kaddararsa, amma yana sonta sosai ya hakura da zama da ita kuma itama har gobe tana sonshi shiyasa taƙi kula kowa ma.

Ikon Allah, to mai zai hana su koma airensu kawai tunda suna son juna.

Ai saki uku ne ya yi mata banda haka da tuni sun koma, ƙaddara dai ta riga fata.
Chapter 51 · 0% Book details