← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 103

Sashe 11

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ashe haka take? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun gaskiya Allah ya wadaran halinta wannan ba matar aure ba.

Allah yaya Hauwa ku saka shi ya ƙara aure kawai domin kuma a dama daku a gidan ɗan uwanku in kun zo ba ruwanku da ita. Jiya ina ji tana magana da Ikram akan irin tanadin rashin mutunci data yi muku idan kuka nima shigo gonarta.

Hmmmmm Hauwa tace tana cije gefen lebenta tare da ƙanƙance ido ɗaya tana girgiza kai.

*Zaku jini shuru a kwana biyu saboda muna da biki sai mun kammala da yardan Allah zaku jini. Ina godiya da addu'arku da kuma soyayyar ku gareni Allah ya saka da alkhairi ya bar kauna. Rahmarku ce*
[2/5, 6:12 PM] Rahma Kabir: *ABIN DA CIWO*

Na
©Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 8.

Hauwa tsabar bacin rai ji tayi kamar taje ta rufe Sameeha da duka amma dole ta bawa zuciyarta hakuri sai ta ce.

Jeki abinki Allah yayi miki albarka ya baki miji nagari, dan da baki faÉ—a mini ba to ba zamu san meke faruwa ba.

Ameen yaya kuma idan na samo wani labarin zan zo in faÉ—a miki.

Hauwa jin Najwa ta faɗi haka ta ɗan washe baki dan dama burinta ta riƙa jin komai dake faruwa a gidan shiyasa ma ta kawo mai aikin da suka nimo da kansu, gashi lokaci guda Najwa ta faɗa mata labari sama da na Jamila, dan haka ta rage murna tana cewa.

Yauwa 'yar gari ai dama irin haka nake buƙata, dan haka ga wayata saka mini number ɗinki domin abubuwan dake wakana a gidan nan nake so a riƙa faɗa mini yadda zan ji daɗin ɗaukar mataki akan Sameeha.

Tayi maganar tana miƙawa Najwa wayarta, Najwa ta amsa da sauri ta saka mata number wayarta ta danna kira ya shiga ta kashe tana cewa.

Wani suna zan saka miki?

Saka mini sunanki tunda na riƙe kuma zan riƙa ganewa tunda 'yar bokon nan munyi na san hausa.

Ta faɗa tana ɗan murmushi, Najwa tayi mata saving sunanta kana ta miƙa mata wayar tace.

Har gida zaki riƙa jin labarin komai dan babban burina Anty Sameeha ta girbi duk abinda takewa mutane.

Hauwa gyaɗa kai tayi tana murmushi dan sosai Najwa ta faranta mata rai ta gusar mata da ɓacin ran da Sameeha ta kunsa mata, sai Najwa ta wuce tana 'yar dariyar samun nasara cikin ƙanƙanin lokaci, sosai take jin farin ciki da hango haƙƙarta tana gab da cimma ruwa, ashe shawarar da Nafeesa ta bata ba ƙaramin aiki zai yi mata ba gashi ba aje ko ina ba ta samu shiga a gurin Hauwa, abinda bata sani ba itama Hauwa abinda take so kenan shiyasa tafiyarsu ta zo ɗaya, ko wannan da mugun nufin dake cikin zuciyarsa akan Sameeha da bata yi musu laifin komai ba sai tsabar son zuciya da hassada da yake damunsu. Hauwa da ta fito daga kitchen ɗiyarta Adama mai aure ta ƙaraso da sauri tana cewa.

Mama muna ta nimanki ashe kina kitchen gasu yaya Laure can a farfajiya sun zo.

Mu je na samesu, ungo riyke mini wannan ledar ki saka a cikin buhun dana baki a jiya, kuma wlh ki adana min shi kar a sace.

To Adama tace ta amsa ledar ta saka a cikin hijab dan dama ta san da shirin Hauwa da ta zo taron, tace zata samar musu abincin da zasu ci a gida da dare ba sai sunyi girki ba, itama saboda ɗaurawa ƙarya cewa mijinta tayi biki suke da shi a family house ɗinsu dan haka kwana zata yi, da ya barta sai ta je gidansu da shirin kwana. Hauwa tana fita ta isa wajen 'yan uwa da suke a cikin rumfar, nan suka gaisa kana ta kama hannun Laure ta jata suka koma can gefe ta shiga labarta mata abinda Sameeha tayi mata akan rufe ɗakuna da tayi dan kar ayi mata sata da labarin da Najwa ta bata kaf babu abinda ta rage, Laure ta riƙe haɓa tana cewa.

Amma anyi mara mutunci mu zata wulaƙanta to wlh ko taƙi ko taso sai ta buɗe ɗakunan mun bawa idonmu abinci. Kuma kika ce yarinyar data baki labari 'yar uwarta ce? karfa ace Sameeha ce ta saka ta dan tayi mana zagon ƙasa fa, ta riƙa sanin duk shirinmu akanta.

Haba Laure wlh ba dai ni Hauwa za ayi wa haka ba, kuma ƙiri ƙiri na hango tsanar Sameeha a cikin idon Najwa a takure take da zaman gidan, ke koma aikota tayi ta bugi ruwan cikina ne ina daidai da ita kuma kifi na ganinka mai jar ƙoma, bata isa ta yi mini wani abu ba dan na gaba yayi gaba wlh shekaru ba ɗaya ba akwai tazara.

Haka suka cigaba da tattaunawa, a hankali kuma gida yana ta cika da 'yan uwa. Sameeha tana can tana hidima da amsar baƙi da gaisuwarsu. Wajen sha ɗaya da rabi masu abinci suka kawo su Hauwa suka zo gurin suka tsaya suna cewa a d'ɗibar musu nasu, masu abinci basu kula su ba suka shiga jera kayan aikinsu dan sune zasu yi savin mutane ka faɗi abinda kake so a zuba maka, Sameeha ta buƙaci haka dan bata so ayi rigima ko ace ta nuna wariya ba a bawa wasu abinci ba, masu rabon abincin suka aika Sameeha ta zo suka nuna mata su Hauwa da maganar da suka yi musu, Sameeha ta kalli Hauwa da Laure tana cewa.

Yaya wannan masu rabon abincin ne duk abinda mutum ke so shi za a bashi, nayi hakane domin a hutar da kowa.

Hmmm amma ɗazun dana zo baki yi mini bayanin haka ba, yanzu kinsa zasu yi mana kallon mayunwata, sannan wannan duk salon ɓata kuɗi ne meye na wani kiran masu rabon abinci gamu, mu miye amfaninmu matsayinmu na manya.

Ba haka nake mufi ba Yaya, naga walima muka yi gayya shiyasa bana so na wahalar da kowa. Iyaka mu haÉ—u muyi zumunci na murna da ganin juna.

Allah ya kyauta, Hauwa muje mu zauna kafin anjima mu kuma jin wani salon wulaƙancin.

Cewar Laure da ta yi gaba Hauwa tayi ƙofa tabi bayanta, Sameeha ta girgiza kai ta juya gurin masu abincin tana yi musu bayanin duk wanda za a zubawa abinci a saka masa naman kaza sannan a yankawa mutum naman rago da aka gasashi, suka ce mata to kana ta wuce cikin falo ranta a ɓace, Ikram tana ganinta tace.

Su Hauwa ne ko? Wlh Anty da kinji shawarata da baku haÉ—a walimar nan ba, da kin bi kowa zuwa gidansa ki gaisa dasu ki yi musu alkhairi, amma na kula sam mutanen nan basa sonki.

Allah yasa mu dace, nasan ko meye zan musu bazan fita ba tunda basu na bawa ragamar komai ba suyi yadda suke so ba. Su damuwarsu dani kome zanyi na faÉ—a musu na wakiltasu suyi mini jagora a cikin lamarin gidana, ni kam wlh uban kuturu yayi kaÉ—an banga wacce zan yiwa wannan biyayyar ba tunda ba haifata suka yi ba, ko mahaifiyar Aminu da tana raye bata yi mini irin wannan ikon ba. Kin ga mu je can waje gabaÉ—aya.

Cewar Sameeha sai ta miƙe suka fita tare da Ikram dama Najwa tana wajen. Dangin Umma sosai suka zo musu amma dangin babansu basu zo ba saboda sunan da ake yi a family house ɗinsu na matar ƙanin su Gaggo Zulai wanda suke 'yan uba, ɓangaren dangin Aminu sune suka cika gida dan sosai suka zo wannan walima. Zuwa ƙarfe uku gida ya tunbatsa DJ yanata sakar musu sauti masu rawa nayi abu dai gwanin sha'awa, kuma har lokacin abinci bai ƙare ba duk wanda ya zo sai an zuba masa, su Hauwa kuwa sai aika yara suke yi suna karɓo musu suna juyewa a kular data ɗauko tana tarawa, Sameeha har cikinsu taje ta zauna aka yi hira da ita ana raha, abin dai gwanin ban sha'awa da burgewa kamar ba wani abu a cikin ransu. Ana kiran sallar la'asar DJ ya kashe kayan kiɗansa sameeha ta sallame shi dan a lokacin suka yi zai tafi. Aka fara shiga cikin falo dan yin sallah, waɗanda suka fara shiga suka fito da gudu suna faɗin wuta wuta a kitchen dan sosai kitchen ɗin ya turniƙe da hayaki, ƙirjin Sameeha yayi wani irin mugun bugawa har yasa ta kasa tsayuwa ta samu kujera ta zauna tana fidda numfashi da kyar tare da faɗin Innalillahi... A zuciyarta, su Hauwa sune kan gaba gurin shiga suna rafka salati nan fa k'ƙauri ya fara fitowa waje, mai gadi ya zo da sauri tare da driver da suke bakin gate suka shiga cikin falon, duk matan suka fito ko wanne cike da tashin hankali, Driver shine yayi jarumta ya faɗa kitchen ɗin yana toshe hanci saboda ƙauri da hayakin dake tashi, ya hango electric gas ne ke ci da wuta sai ya juya yana dube dube sai ya hango abin kashe gobara dake manne a bango ya je ya sauri ya ɗauka ya shiga fesawa a inda wutar ke ci, cikin ikon Allah wutar ta mutu sai hayaki daya ke fita, dama tuni mai gadi yaje ya cire wutar daga nepa, ya shigo yana yiwa driver magana.

Wutar ta mutu kuwa? daga ina ne ma wutar ta kama.?

Daga wannan electric gas ɗin ne ya kama, ƙila an kunna an mance ba a kashe ba.

Driver ya bashi amsa, sai suka fito gabaɗaya, matan dake ƙofar falo ɗin suka tare su da tambayar wutar ta mutu? suka sanar dasu ta mutu sai mai gadi ya wuce ƙofar gate driver kuma ya ƙarasa inda Sameeha ke zaune ta dafe kanta da hannu biyu yace.

Hajiya munyi sa'a wutar ta mutu, daga electric gas ne ya tashi amma a iya shi ya tsaya, ƙila anyi mantuwa an barshi a kunne.

Da sauri Sameeha ta dago lokacin daya fara magana da ya kai aya ta sauke numfashi tayi masa godiya kana ya wuce, Sameeha ta kai kallonta ga Ikram da Najwa tana cewa.

Dama an bar kitchen a buÉ—e? Ya aka yi aka bar gas a kunne.
Chapter 11 · 0% Book details