← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 103

Sashe 15

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani sirri kuma ai wlh naji daÉ—i da kika faÉ—a mini, ko baki faÉ—a bama mun san ba haka ta barshi ba amma zamu É—auki mataki, nagode Najwa Allah yayi miki albarka yasa ki gama da duniya lafiya.

To yaya In Sha Allah na samu lokaci har gida zan zo, amma kafin nazo sai na sake komawa gidan Sameeha na samo miki labari, duk da nace bazan sake zuwa ba, amma kodan ku riƙa sanin meke faruwa a gidan dole na je dan nima babu abinda nake so sama da naga Anty Sameeha ta wulaƙanta kamar yadda take wulaƙanta mutane dan har Innata bata bari ba, shiyasa ai jiya bata je ba tace ni ce zan je dole ba dan halinta ba sai dan kirkin iyayenta.

Aiko nagode kin ga kina samo mana labari muna ƙara shirya wa matakin da zamu ɗauka, tunda ni ba zan sake zuwa gidan ba yazo ya zama abin magana.

Cewar Hauwa, a haka suka yi sallama ta kashe wayar tana duban Adama fuskarta cike da murmushi dan gabaÉ—aya tun jiya rabon fuskarta da annuri sai yanzu da Najwa ta gama labarta mata magananganu, Adama tace.

Hala wannan 'yar uwarta ce ta kira dan naga yarinyar tana da hankali ba irinsu ba.

Itace ta kira Adama, ai kina jin zagin da su Sameeha suka yi mana, yanzu zama bai ganni ba bari naje babban gida nayi magana da Laure, dan zuciyata ta fara kwanciya da yarinyar nan, itace dai dai wacce ta dace Aminu ya aura, kinga su can mun haÉ—a musu rikicin dangi kamar yadda taso ta raba kawunanmu, sannan Najwa tamu ce sai abinda muke so zata yi a gidan, duk da abin zai yi wuya amma sai nasa anyi mana aiki akan Aminu kai waye.

Amma mama anya hakan zai yuwu? kin fa ce da Baban Sameeha da maman Najwa uwa É—aya uba É—aya.

Adama zai yuwu mana ai babu haramci.

Amma ana barin halak dan kunya.

Ba a wannan zamanin ba, nasan ba zamu sha wuta gurin shawo kan Najwa ba, tunda Aminu yanada nagartan da za a so shi, ga kyau ga kuɗi ga nasaba komai ya haɗa, in yaso sai ya raba musu gida, ni dai in hakan ya faru wallahi baƙin ciki na ya yaye banda saurin ɓacin ran Sameeha, dan mun gama ƙunsa mata baƙin ciki, kuma kiri kiri zan nuna mana mune muka haɗa auren dan tasan mun isa da Aminu.

To Allah ya tabbatar, in dai hakan zai faru to ƙarshen Sameeha yazo.

Ke bari na tashi naje gida, wlh ji nayi ma na ƙoshi.

Cewar Hauwa data miƙe cikin sauri ta wuce ɗaki, ba jimawa ta fito sanye da hijab ta fice tana cewa sai ta dawo. Gida uku ke tsananinta da gidansu dan haka tana shiga bata tsaya ɓata lokaci ba ta wuce sashin Laure, tayi sa'a Alhasan ya fita yaran ma duk sun tafi makaranta, ta zauna dirshen akan kafet kamar yadda Laure take zaune a gurin ta baje ƙafa daga ita sai ɗaurin kirji, tana cin taliyar Hausa da ta dafa ta zuba naman kaza a ciki, ta kalli Hauwa tana cewa.

Idan na ganki a irin wannan lokacin to nasan akwai labari Allah yasa dai mai daÉ—i ne.

Hmmm maganganu kam nazo dashi duk da dai na ɓacin rai ne, sannan kuma akwai shawarar dana yanke wanda nake so mu tattauna. Yanzun nan Najwa ta kirani ta gama faɗa mini ɗibar albarkan da Sameeha tayi mana.

Nan fa Hauwa ta shiga zayyano mata maganganu tana yi tana tafa hannu da riƙe haɓa tare da ƙanƙance idonta, Laure salati kawai take tana kwashewa Sameeha albarka, da Hauwa ta gama ne tace.

Kin san shawarar dana yanke domin mu huce takaicinmu, to na samarwa Aminu mata cikin sauƙi ba sai na sha wuya ba.

Wacece kika samo? Ni dai da kin bari mun bincika da kyau mun samo wacce ba zata watsa mana ƙasa a ido ba.

To Najwa na yanke shawarar zai aura, dan itama cewa tayi da ba dan Sameeha 'yar uwarta bace da sai ta auri Aminu taga karshen wulaƙanci, kin ga kuwa wlh yarinyar nan zata share mana hawaye, kuma mun jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, na farko Sameeha zata shiga cikin kunci akan zata yi kishi da 'yar uwarta, na biyu kuma Najwa tamu ce sai abinda muke so zata yi mana, kinga a hankali zamu saka tayi waje da Sameeha ba sauran labarinta a gidan Aminu, can kuma zasu ƙarata da rikicin dangi, mu kuma cikin ruwan sanyi buƙatarmu zata biya.

Wayyo Allah daÉ—i, Ayyiririri, amma wannan shawara tayi Hauwa. Sai dai akwai sauran rina a kaba, ya za muyi da uban gayya Aminu dan kin san abu ne mai wuya ya yarda da aurenta cikin ruwan sanyi.

Haba Laure sai kace mu ba 'yan cikin garin Kaduna ba, wajen malam mai allon ƙarfe zan kai sunan sa ya cika masa aiki, sannan ma ai ba zamu bayyana Najwa bace kai tsaye, hatta Sameeha ba zamu bari tasan ita zai aura ba har sai anyi ta ganta, dan Najwa zamu gargaɗeta ko a gidansu karta bari asan Aminu mijin Sameeha ne zata aura, dan ba lallai iyayenta su bamu haɗin kai ba.

Gaskiya naji daɗin wannan magana yanzu mu bari komai ya lafa tukuna kafin mu taso da wannan maganar, mu dai mu cigaba da shirinmu, ki ƙara jan yarinyar a jikinki har ki sanar da ita buƙatar mu, in ta amince sauran masu sauƙi ne.

Cewar Laure, Hauwa ta bata hannu suka tafa tana jin farin ciki kamar ma aniyarsu ta biya, haka suka cigaba da ƙulle kullensu sai wajen sha ɗaya da rabi kafin Hauwa ta bar gidan.

****

Sameeha.

Tana zaune a falo tana hutawa dan basu daɗe da karyawa ba, ta kunna tv tana kallo gasu Abi suna wasa a carpet da yake duk sunyi wanka kuma Jamila ta gama gyaran falon, farfajiyar gidan ma mai gadi ya kira wasu sun zo sun tattara gidan sun kwashe bola an biyasu sun tafi. Ikram kuma tana kwance a gado tana kallon abubuwa a facebook, nan taci karo da videon faɗansu na jiya sai ta karanta bayanin da aka yi a ƙasansa, tsabar mamaki da fargaba yasa ta tashi zaune tana rafka salati, nan ta shiga comments section ta samu sai zagin Sameeha ake yi, cike da tashin hankali jiki yana rawa ta sauko a gado ta nufi falo.

_Abin da ciwo ace naka shike bada kai, ana zaton wuta a maƙera sai a tsinceshi a masaƙa, kuma wani lokacin makashinka yana nan tare da kai_ Mu je zuwa.
[2/9, 9:45 PM] Rahma Kabir: *ABIN DA CIWO*

Na
©Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 11.

Ikram tana isa falon ta miƙawa Sameeha wayarta tace cikin rawar murya.

Anty kinga an samu wanda ya ɗauki video ɗinmu na rikicin jiya sun yaɗa a social media har da tagging fuskarki da aro ana cewa ke ce matar da kike yiwa dangin mijinki wulaƙanci dan sun zo gidanki walima. Kalla dai ki gani.

Hannun Sameeha yana rawa ta amsa ta shiga kallo zuciyarta ta gama tsinkewa sai hawaye ya soma zarya a kuncinta, har ta gama kallo ta miƙawa Ikram wayar tana share hawaye tana cewa.

Sharrin su Hauwa ne dan a cikinsu aka samu shaiÉ—anin daya É—auka ya yaÉ—a domin su zubar mini da mutunci a idon duniya, kuma duk wanda ya zageni Allah ya isa dan bazan yafe ba.

Amma wlh mutanen nan basu da kirki rashin imaninsu har ya kai su yaɗa video irin wannan dan suci mutuncinki, sauƙin abin hoton fuskarmu bai fito sosai ba saboda daga nesa aka ɗauka.

Koma waye yayi mana haka to yama kansa kuma...

Bata gama magana ba wayarta ta shiga ƙara taga Zaidu ne, tana ɗauka shima maganar video yayi mata, nan ta fashe masa da kuka ya dinga bata haƙuri yace tabarwa Allah duk wanda yayi mata haka sai Allah ya saka mata, haka suka aje wayar, a takaice haka ta dinga amsa wayar mutane wanda suka gani duk dai haƙuri suka bata, dan har Yaya Kamalu ya kirata yace zasu ɗauki mataki. Cikin damuwa ta kira Aminu yana ɗauka ta bashi labari yace cikin fada.

Na gaji da abinda su Hauwa suke yi mini yanzu, su rasa abinda zasu saka mini da shi sai suci mutuncinki, ai bake suka tozarta ba ni suka tozarta, kiyi haƙuri zan ɗauki mataki.

Yana kaiwa nan a maganarsa sai ya kashe wayarsa, ya duba agogo yaga ƙarfe sha biyu saura sai ya kira wani da yake aiki a gurin jirgin ƙasa yace zai tura masa kuɗi ya siya masa ticket na ƙarfe biyu zai je Kaduna da yake yanzu sau biyu jirgin ke zuwa Kaduna daga takwsa na safe sai kuma biyun rana, yana gama wayar sai ya shiga toilet dan ya watsa ruwa ya fito ya shirya.

Sameeha kuwa saboda damunta da aka yi da kira dan duk wanda yaga videon sai ya kirata, ya sata kashe wayarta gabaɗaya, tayi kuka harta gode Allah Ikram sai bata haƙuri take yi, umma ma ta kira a wayar Ikram ta bata haƙuri tace dama dole rayuwa tana tafiya da ƙalubale dan haka jarabawa ce sai ta ɗaure zata ci, kuma matakin nasara yana tare da yin haƙuri, maganganu ta gaya mata masu daɗi da ya sakata samun natsuwa. Da aka kira sallar azahar ne suka shiga ɗaki dan gabatar da sallah.

****

Najwa.

Lokacin data kira Hauwa tana tare da Nafeesa dan rubuta mata maganganun tayi a takarda wanda zara faɗawa Hauwa kuma itama ta ƙara da nata, sun haɗu a islamiyya ne wanda dama tun jiya suka shirya zata kira Hauwa ta shinfiɗa mata karyan maganganu da zai sa ta samu shiga a gurinta, wani aji suka shiga da ba a amfani da shi wanda empty yake ko kujeru babu, a nan ta saka katin data siya ta kira Hauwa kuma tayi sa a ta ɗauka, shine ta samu damar faɗa mata maganganun da suka ƙara hautsina Hauwa ta dinga sakin magana, lokacin da ta gama wayar ta saki shewa cike da tsantsar farin ciki Nafeesa ma tana dariya ta miƙa mata hannu suka tafa tace.
Chapter 15 · 0% Book details