Sashe 81
Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maza ya kamata a barwa su Auwal gidan nan ka koma naka gidan, ayi mutum yaƙi aure yana niman tsufa a gida.
Haba dame kwaÉ—o yafi gaya ai kaima ba jimawa kayi da auren ba, wato ka ji daÉ—insa zaka fara yi mini gori, to bama wannan ba nasan duk in ka nimeni da akwai magana, meye labari?.
Hmmm Nafeesa da Binafa ne suka nima chager mini kai yaran nan ƙiri ƙiri suna niman ɓata sunan zuri'armu.
Me suka yi? Amma nayi mamaki daka ce har da Nafeesa dan ita tana da natsuwa da hankali ba irin Binafa da kullun cikin saka mu magana take yi ba.
Nan Taju ya gyara zama ya ciro wayarsa ya buɗe WhatsApp ya bashi saƙon da aka tura masa, Hassan ya amsa ya karanta, koda ya gama mamaki ne ya maye fuskarsa Taju ya ƙara da bashi labarin abinda Hamisu yayi masa daya kirashi, sosai ran Hassan ya ɓaci ya miƙe cikin zafin nama yana cewa.
Haba dama biri yayi kama da mutum, shegiyar yarinya kullun sai ta fita ko ta jawo mana ƙawaye su zo gidan nan, ashe iskancinta take yi son ranta wlh idan na gamu da Binafa rai kaɗan zan bar mata.
Yana gama faÉ—ar haka ya isa gurin daya saka chargy wayarsa ya É—auka sai ya dawo ya zauna ya shiga kiran layin Binafa, har sai da ya tsinke ba a É—auka ba ya kuma kira sai aka dauka yadda yaji murnar namiji ne sai ya dannw zagin daya yi niyyar dura mata, yace a dakile.
Malam ina me wayar?
Kana magana da Sagent Lawal mai wayar kuma mun kama tana nan police station bisa laifin FyaÉ—e da suka yiwa wata yarinya suka lalatata, to dama mun so ta faÉ—a mana wanda zamu kira a 'yan uwanta amma tace bata da kowa tana so mu bada belinta amma hakan ba zai yuwu ba.
Ok wane police station ne?
Nan ɗan sandan ya sanar da shi, Hassan yace gashi nan zuwa sai ya kashe wayar yana duban Taju tare da bashi labarin a taƙaice, Taju ya miƙe yana cewa.
Zama bai ganmu ba wato dai maganar da Hamisu ya faÉ—a ta tabbata, Allah ya shirya.
Hassan bai iya cewa komai ba saboda takaici sai ya miƙe suka fita tare, a motar Taju suka je police station ɗin wanda sagent ɗin da ya ɗauki wayar shine ya turasu gurin DPO ya gabatar dasu, bayan sun gaisa DPO yace.
Wlh munyi munyi su faɗa mana wani nasu amma sunƙi, iyayen yarinyar da suka yiwa Fyaɗe sun ce ba zasu haƙura ba sai anje kotu, a takaice tun wata guda daya wuce suka yaudari yarinyar suna kaita gidan Hanan a nan suka ɓata ta, yarinya 'yar shekara sha shida kuma ba sau ɗaya suka yi mata ba yafi sau biyar, mahaifiyar yarinyar ne ta kamata a ɗaki tana saka brush a gabanta shine data duketa matsa mata take faɗa mata yadda aka yi ta zama haka, to a nan gidan Hanan muka kamo su yanzu haka muna son ranar monday zamu miƙa maganar kotu tunda basu yi gardamar laifinsu ba, sai dai sun nima su bamu cin hanci dan mu rufe maganar hakan kuma ya ƙara laifinsu.
Ni sunana Hassan wannan kuma Taju mu yayyin Binafa ne dan haka ina so ku cigaba da riƙe su har sai an shiga kotu an yanke musu hukunci, kamar yadda taƙi faɗar kowa nata ina so koda danginmu sun zo nimansu ku nuna basa nan, dan Allah ina son wannan ya zama sirri karku nuna mata mun zo ma, zan tafi da wayarta ta yadda ko ta bukaci yin magana da wani ba zata samu ba ku nuna mata babu dama.
Haba Hassan ya zaka ce haka bai kamata in ta aikata laifi mu rufe maganar ga iyayenmu ba.
Cewar Taju, Hassan ya saki guntun murmushin takaici yace.
Ina so wannan ya zama babban darasi a garesu, kasan halin Binafa ba tada natsuwa ga taurin kai, ta jima tana aikata ɓarna ina son wannan ya zama hanyar shiriya a garesu, Allah yasa a kaisu gidan yari ma. DPO dan Allah kayi abinda nace maka dan wlh wannan shine kadai hanyar da zaisa Binafa ta shiga hankalinta.
Karka damu zamu yi aikin daya kamata dan ba zamu taɓa yarda a danne zalunci akan gaskiya ba.
Nan suka yi masa sallama ya basu wayar Binafa suka wuce. A mota Taju take cewa.
Anya hakan bazai sa sunan zuri'armu ya ɓaci ba? bana so maganar nan taje kotu.
Wlh sai taje fa, Taju kai dai ka saka ido kawai, ai su Dady sune suka ɗaure mata gindin yin komai dan haka bana tsoron duk abinda zai faru ta yadda kowa zai gane kuransa, kuma babu sunanmu da zai ɓaci nata ne dai zai ɓaci wlh.
Haka suka dinga tattauna maganar Hassan ya roƙi Taju akan karya sanar da kowa maganar har sai anje kotu kafin maganar ta fita, ta hakane za a samu daidaiton tarbiyya dan abin yayi muni da yawa. Haka Taju ya sauke shi a gida sai ya wuce abinsa, ko shi yaji daɗin abinda Hassan yayi kawai baya son ya nuna rashin damuwarsa akai ne yasa yake ta bashi magana, amma hukuncin daya yanke shine daidai yana so Binafa ta gane kurenta ta yadda ba zata sake sha'awar wata mace ba a rayuwarta.
******
Hauwa.
Ta kasa fitowa waje saboda kunyar abinda Aminu yayi mata sai da aka yi sallar magriba kafin ta tattara yanata yanata ta koma gidanta tare da yaranta duka. Dama tun rana baƙi kowa ya kama kansa sai 'yan kauye da suka rage akan washe gari zasu wuce suma. Saboda naushin da Aminu ya yi mata sai da ya saka hakoranta na gaba yin girgiɗi alamar zasu faɗi, gashi ya sakar mata zazzaɓi sai da tasha maganin rage zugi kafin ta samu barci a ranar. Adama kuwa baƙin ciki goma da ashirin ga saki ga kuma wulaƙancin da Aminu ya yiwa mamanta ga kuma lalacewar aurensa da Najwa wanda a dalilin auren itama ta rasa nata auren, tun tana yin kukan fili har sai da ta koma yin na zuci, dan hakanan take jera ajiyar zuciya wanda ya saukar mata da ciwon kai mai tsanani da alama jininta ya hau, da kyar ta samu barci.
Washe gari Hauwa ta tashi saman dashishinta ya kumbura daga sama, sun tabbata fita zasu yi dan sosai suke yi mata ciwo, da kyar ma ta iya karyawa, bini bini take jan tsaki ta ƙumdumawa Aminu ashar, a haka Laure ta shigo gidan domin ta ƙara dubata da kuma jaje. Bayan sun gaisa Hauwa take cewa.
Wallahi Tallahi bazan yafe wannan cin kashin da Aminu yayi mini ba, sai yayi nadamarsa dan sai na saka shi yayi kukan jini.
Ni kam Hauwa da za kiji shawara da kin saki komai kin barwa Allah dan wlh ni na sare da komai saboda babu nasarar da muka samu komai lalacewa yake yi ba biyan buƙata, jiya fa Alhasan kamar zai rufeni da duka saboda masifar da yake ta yi mini wai ai duk bakina ɗaya dake, dana nima kare kaina ya ce inna kuma magana abakin aure na wai ya gaji da halina kuma aure dai zai ƙara ya huta da baƙin cikin dana ke ƙunsa masa, yanzu ma ƙarya nayi masa akan zanje dubiya na shigo nan, ƙila daya san nan zan zo ba zai bari ba, dan sosai ya goyi bayan abinda Aminu yayi miki cewa yayi da zai samu dama shima da sai ya nakaɗa miki duka, saboda duk cikinku ke ce kika fita zakka ya rasa ina kika samo mugun hali.
To yanzu kin zo kina faɗa mini ne ki ƙara mini baƙin ciki ko jajenta abin da ya same ni, idan kin saduda ni ban sadudu ba kuma ki bar mini faɗar dama ban gayyace ki ba, zaki iya barin mini gida bana son damuwa.
Haba Hauwa abokin kuka shi ake faɗawa mutuwa, ni na baki labari ne domin abin bai yi mini daɗi ba muyi wa juna jaje, kema kinsan muna tare, sai dai kawai na fita daga sabgar Aminu da Sameeha dama duk abinda ya shafesu dan in zauna lafiya, bana son na rasa aurena a karo na biyu kema shawarar da zan baki ki yi hakuri ki saki komai ki ɗauki haka a matsayin rubutaccen ƙaddara, ki kama 'yan uwanki ki zubar da makamanki.
Kutumar kaza kaza 'yan uwan, mutanen da suke son ganin bayana, to ganin bayana mana dan babu wanda yake goyon bayana balle a tsawatarwa Aminu wulaƙancin daya yi mini, sam basa ƙaunata saboda Aminu yana da kuɗi ni kuma fuƙara'u ce, dan haka na san duk yadda zan zauna da ko wani tsinanne ne wlh, banda nasan uwa ɗaya uba ɗaya muke da sai nace ƙila ni tsintoni aka yi aka saka ni a cikinsu. Da wanne zanji da sakin Adama da aka yi akan wannan tsinannen auren ko da wulaƙancin Aminu.
Haƙuri dai za kiyi Hauwa mu karɓi wannan ƙaddarar In Sha Allah Adama zata samu wanda yafi mijinta, muyi kokarin gyara kuskurenmu dan Allah, saboda in ɓera na da sata daddawa na da wari, Alhakin Sameeha ne yake binmu.
Laure tashi ki bar mini gidana tun kafin raina ya ƙara ɓaci na zageki.
Allah ya baki haƙuri yasa ki gane amma wlh ni dai na cire hannu na daga lamarin Aminu babu ruwana.
Tana kaiwa nan ta miƙe ta gyara hijab ta fice daga dakin, Hauwa ta bita da mugun harara, wanda tana fita ta fashe da kukan baƙin ciki, ji tayi duniyar tayi mata zafi ga mari ga tsinka jaka da wanne zata ji.