Sashe 88
Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana kaiwa nan ta kashe wayar Saleema kuwa wani ashar ta saki jin ta kashe wayar ta fito da sauri ta nufi ɓangaren Malam.
[5/12, 7:31 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*
52
Saleema tana isa falon malam ta sane shi ya fito daga bedroom alamar fita zai yi, yadda ya ganta a hargitse yasa ya tambayeta ko lafiya? Cikin damuwa ta sanar da shi koma yasha mamakin rashin jin Najwa yace.
Wato wannan yarinyar shaiɗaniya ce, ina shirin yin aiki akanta yau sai ta rigani ƙaddamar da nata shirin, amma duk da haka zanyi maganinta jeki ni zan mayar miki da kuɗin data ɗauke miki Allah ya shirya ta.
Amin malam dan Allah ayi aikin da zaisa ta dawo dan ni ta yiwa baƙin cikin samun alkhairi saboda na san Alh. Atiku ba baya ba.
Hmmm ni tafi yiwa baƙin ciki dan alkhairin da nake hangen zan samu a dalilinta da yawa, amma karki damu zata dawo da ƙafarta.
Saleema ta saki murmushi saboda bayanin malam yasa taji É—an natsuwa, musamman ma daya ce zai dawo mata da kuÉ—inta sai kawai ta fita ta koma sashinta, bata yi yunkurin kiran baban Najwa ba ta san zasu nimeta da kansu.
***
Najwa.
Da wuri suka isa kd wanda Mujaheed har gida ya sauke Najwa bayan sun amsa Number juna, yace in ya samu natsuwa zai kirata sai ta yi masa godiya ta shiga cikin gida tana jan trolley, ta samu gabaɗaya 'yan gidan suna tsakar gida Inna tana suyar kosai daga gefe, su kuma suna kan babban tabarma da baba suna karyawa, sallamarta ya katse musu hirar da suke yi cikin nishaɗi wato barinta gidan bai sa sun fasa yin walwalarsu ba, sororo suka bita da kallo itama ta tsaya tana ƙare musu kallo, yaya Junaid ne ya daka mata tsawa.
Dalla malama ki ƙaraso ciki kin tsaya kina kallonmu sai kace wacce ta warke cutar makanta.
To nayi sallama ai banji kun amsa ba
Ta bashi amsa tana turo baki tare da jan trolley ɗin zuwa ciki ta jingine shi a gefe, ta samu ƙaramar kujera ta zauna daga gefensu.
Baba ina kwana.
Lafiya lau baba ya amsa a takaice kana ta gaisa da Inna ta amsa sai tabi sauran yayyinta ta gaishesu ɗaya bayan ɗaya, Sadiq ne ya amsa mata nashi daga ƙarshe yana cewa.
Lafiya kika bugo sammako zuwa Kaduna sai ka ce an koro ki me ya faru ne? dan na san ba lafiya ba.
Wai kawai auren dole zasu yi mini, sun turo mini mutum akan mu daidaita da juna ni kuma dana ganshi baiyi mini ba, shine wai ban isa ba dole sai na aureshi, shine na dawo nan dan sanan babu me yi mini dole a nan gida.
Ba shakka Najwa itama Saleemar kin manna mata tsiyar ko, to ai shikenan sai ki cigaba da zama a nan tunda haka kika zaɓa, Allah ya shiryeki yasa ki gane gaskiya kan lokaci ya ƙure miki.
Cewar baba, nan su Junaid suka rufeta da faɗa Najwa dai bata ce komai ba sai ƙunƙune take yi musu, Inna kam suyarta take yi bata saka baki ba dan takaici, daga bisani ne baba ya kira Saleema a wayarsa bayan sun gaisa yace mata sunga Najwa ta dawo, Nan saleema ta sanar dashi komai daya faru yayi murmushi yana cewa.
Tunda ta gwada miki halinta yanzu ai shikenan Allah ya kyauta sai kiyi haƙuri.
To yanzu yaya haka za a zura mata ido ba aure, sannan ni dan Allah zan turo mutumin yazo nan ku ganshi sai a bashi damar ya turo.
Saleema kenan, kina tunanin in mun tursasa Najwa zata yarda da auren ne, aurenta na farko ita ta kawo shi bayan ɗumbin cin amanar data aikata, dan haka yanzu ma bazan taɓa yi mata dole ba dan nasan zata iya bani kunya, duk wanda ta kawo mini shi zan aura mata, ki bawa mijinki haƙuri ku bar maganar wancen mutumin kawai, domin ni nasan halin Najwa ku barta kawai.
To shikenan yaya Allah ya shiryeta.
Yace amin kana suka yi sallama suka aje kan wayar. Najwa ta miƙe ta isa ɗakinta taga a rufe sai a lokacin inna tayi mata magana.
Ki wuce É—akina ki aje kayanki dan É—akinki an zuba kayan aurenki a ciki.
Bata amsa mata ba ta wuce É—akin inna ta cire hijab ta aje kayan kana ta fito ta É—auki kofi ta É—iba kunu, Inna ta zuba mata kosai sai ta koma kujerar data tashi ta zauna ta soma karyawa tama manta ko brush bata yi ba. Mazan gidan gabaÉ—aya suka fita suka yiwa inna sallama, baba ma wanka yayi ya wuce kasuwa aka bar inna da Najwa, inna ta kalleta tana cewa.
Tunda kin dawo sai ki tashi ki naÉ—e tabarma ki share gidan ga kuma wanke wanke yana jiranki nima wanka zanyi zan fita dubiya.
Haba Inna daga dawowata sai aiki sai kace baiwa ga gajiyar tafiya, waye ma ba lafiya da zaki fita da sassafen nan naga kamar ma da kunu zaki tafi.
Najwa me yasa yanzu sam baki tauna magana kike fitar da ita, ke har yanzu baki shiga hankalinki akan abinda kika aikata bako, hmmmm ba baki nayi miki amma duniya zata koya miki hankali.
Kai inna irin wannan maganar fa kika faÉ—a mini ranar aurena sai gashi washe gari an sakoni, ki yi mini Addu'a da fatan alkhairi mana.
Hmmm ki dai tashi kiyi abinda nace miki dan ba zan daÉ—e ba yanzu zan dawo. Ikram ce ba lafiya an kwantar da ita a asibiti kwananta biyu kenan, ita ta saka nayi mata kunu da kosai dan jiya naje na duba ta.
Inna waike sam bakya kishin abinda ya faru dani ne da ba zaki kyale su Sameeha ba, bayan duk sune sanadin halin da nake ciki, kina nuna sun fini daraja a gunki bayan ni ce taki su kara ne.
Sun fi mini ke Najwa domin zuciyarsu tana da kyau ba irin taki bace kuma sun san nasu. Abin farin ciki ma ciki ta samu shine yake É—an bata wahala.
Sadda inna tace ciki ta samu sai da Najwa taji wani abu ya tsirga mata a zuciya nan take taji haushi, a zuciyarta tace.
Allah yasa cikin ya zube ko ya kasheta muga idon É—an iskan nan Shamsu.
Sai ta ƙare da jan guntun tsaki tana miƙewa, Inna tana kallon yanayinta ta girgiza kai ta miƙe ta shiga ɗaki dan tasan in dai Najwa ce ba zata yiwa Ikram fatan samun lafiya ba saboda mugum halinta. Cikin sauri ta shirya ta ɗauki ƙaramin basket data saka jug ɗin kunu da kular ƙosai ta fice abinta. Najwa badan ranta ya so ba ta soma gyaran gidan, sai taji dama bata dawo ba saboda tasan ta dawo kenan aikin gidan yana kanta.
****
Ikram.
Tun bayan bikin Najwa ta soma laulayi kaɗan kaɗan sai dai kwaɗayi yafi yawa a ciki, da suka je asibiti likita ya tabbatar tana da shigan ciki wata ɗaya har da sati biyu, farin ciki wajen Shamsu ba a magana haka ma su Khairy sunji daɗin labarin dan Shamsu ita ya fara faɗawa ta sanar dasu Hajiya, nan suka yi musu fatan alkhairi da sauka lafiya. Musamman Hajiya ta aika cousin ɗin su khairy Zainab wacce take gabanta domin ta riƙa taya Ikram ayyukan gidan tunda har lokacin ba a samar mata mai aiki ba, kuma itama bata so domin tace tana tsoron masu aiki saboda abinda ya samu Sameeha. Umma ma taji daɗi labarin cikin, nan ta soma ɗawainiya da ita dangin kayan kwaɗayi tana aika Zaidu yana kai mata. Sameeha kuwa taso zuwa Kaduna dan ta ganta amna Ibrahim ya hana dan baya so tayi nesa dashi ko kaɗan, a waya dai suke magana tana jin lafiyarta. Kwana biyu daya wuce ne taci wani alale data saka Shamsu ya siyo mata a wani rastaurant taci shine ya sakata gudawa da amai duk ta galabaita, dalilin zuwanta asibiti kenan aka bata gado, Hajiya data samu labari ba ƙaramin faɗa tayi wa Shamsu ba akan me yasa bai faɗa ba tasa anyi mata a gida bata son suna cin abincin wajen nan saboda basu san yadda aka haɗa shi ba, nan ya bara haƙuri akan bazai kuma ba, shima a tsorace yake saboda kar cikin ya zube dalilin haka, sosai yaji haushin kansa daya sayo mata abinda ya illatata. Umma kam Ikram ɗin ta yiwa faɗa akan in ita ba zata iya dafawa ba me yasa bara kirata ta girka mata ba, taso ta zauna jinyarta amma su Hajiya suka ce ta barshi wata dattijuwa mai girka abincin gidan Hajiyar itace ta zauna da ita tare da Zainab, kuma tana samun kulawa sosai dan har ta fara dawo da jikinta data rame a lokaci guda.
Inna tana isa ta wuce dakin da aka kwantar da ita nan asibitin garkuwa, wanda yake ita kaɗai ce a ciki ba wasu marasa lafiyan. Ta samu umma ma tazo tana zaune tana matsa mata akan tasha tea ɗin da aka haɗa mata amma taƙi sha, tana ganin inna da Kwanko ta haɗiye miyau dan dama tasan Inna zata kawo mata abu bata faɗa musu bane, inna suka gaisa da umma da Zainab dan baba Jimmai ta koma gida ta dawo, nan Ikram ta gaisa da inna tace cikin zaƙuwa.
Allah yasa kunu da ƙosan ne Inna kika kawo mini.
Aiko shine, da wuri na tashi na haɗa komai saboda ke, muma dashi muka karya babanku yace a yi miki ya jiki yana nan zuwa su Junaid ma suna ƙara yi miki ya jiki.
Ina amsawa Inna, ai basu daÉ—e da fita ba ma yaya Junaid É—in kika zo.
Dama sunce zasu biyo su duba ki. Ga kunun ki fara sha saiki aje tea É—in da naga baki son sha.