← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 103

Sashe 38

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da safe Ikram zata tafi makaranta tace wa Sameeha ta jirata ta dawo sai su tafi kasuwar, Sameeha tace ba zata jirata ba dan bata son shiga kasuwa da rana, umma tace gaskiya gwara taje da wuri ta dawo, Ikram bata so ba taso ace tare suka fita dan wannan fitan shine na biyu da Sameeha zata tayi tun dawowarta gida, na farkon gidan kakaninta taje ita da Ikram da Anwar, Ikram ta tafi da zummar zata dawo da wuri harta roƙi Sameeha akan ta jirata. Sameeha ta shirya cikin baƙar jallabiya ta sanya marron ɗin hijab ta sauki ATM ɗinta ta saka a fos sai ta yiwa umma sallama wajen goman safe ta fito daga gida, sai taji kamar iska zai ɗauketa dan rabon data fito waje ta manta dan koda zasu gidan kakansu a motarta suka tafi, ta isa titi ta tari napep drop dan bata son ɓata lokaci, yace dubu ɗaya da ɗari biyar ta ciro kuɗinsa ta bashi ta shiga suka wuce, sai kallon gari take tana ganin sauye sauyen unguwanni dan bata fahimci ma haka wurare suka sauya haka ba saboda a da fitarta a motanta ne, hanya kawai take kallo, sosai taji iskar dake dukan fuskarta yana mata daɗi ashe zama a gida tamkar preson ne wani lokacin dan sam baka sanin ya iska me daɗi yake saika fito. Har suka ƙarasa cikin gari mai napep yace ya jirata ne ta dawo ya mayar da ita ganin ya samu ta biyashi da kyau, tace masa ya tafi zata daɗe a kasuwar karta ɓata masa lokaci, sai ta wuce shima ya wuce. A hankali take tafiya tana ganin yadda kasuwar gabaɗaya ta sauya dan sabuwar kasuwa ta shiga, tana tafiya sai shagunan kayan yara take gani abin yana bata sha'awa da tuna nata yaran, nan take kewarsu ya dawo mata sabo har taji idanunta suna ciko da kwalla, ace da ranta da lafiya ƙiri ƙiri 'ya'yanta sunyi mata wuyar gani, wani mutum ne ya tare ta yana cewa me take son siya? tace shagon sayar da kayan saloon, sai ya jata can ciki suka isa wani shagon kayan Saloon, nan fa ta zauna suka fara ciniki tana faɗan abinda take so ana faɗa mata kuɗin su, ganin abubuwan sun tsefe da tsada yasa tace zata dawo dan gaskiya in ta biye zata kwashe kuɗin daya rage mata na bankin kaf, ta amsa card ɗin me shagon akan in ta dawo zata kira dan da wuya ta gane shagon saboda can cikin kasuwa ne. Ta fito bakin hanyar kasuwa ta gaban wasu manyan plaza, daga kasan wani gidan sama ta karanta sunan wani ƙaton shago an rubuta Khairy boutique, Sameeha har ta gota sai ta tsinci kanta da komawa ta shiga shagon, kayan yarane English wears dana manya, harma da gefen atamfofi kusan komai da akwai har da takalma da jakuna, Sameeha tana shiga wani saurayi ya yi mata sannu da zuwa sai kuma wasu 'yan mata biyu suka tare da suma da nasu welcome ɗin tare da nuna mata gurin zama duk sanye suke da t-shirt da sunan boutique ɗin, suka tambayeta me take so Sameeha ta tsinci kanta da cewa kayan yara take so ɗan shekara goma dana mace 'yar shekara takwas, nan fa suka fara ɗibowa suna nuna mata, ta shiga zaɓa har sai da ta cire musu bibbiyu, suka ce bari su kira ogansu tana nan suyi maganar kuɗi, ɗaya daga cikin 'yan matan ta isa wani ƙofa da yake nuna alamar ƙaramin office ne sai ta shiga, ba jimawa sai ga wata mace kyakkwawa black beauty ta fito tare da wancen yarinyar data je kiranta, ta samu guri ta zauna a wata farar kujera, suka gaisa da Sameeha kana suka fara cinikin kaya sai kuɗin ya tashi akan dubu talatin da biyu, Sameeha tana ƙoƙarin ciro ATM ɗinta ta basu su cire a pos, sai kira ya shigo wayarta sai ta fasa ɗauko ATM ɗinta ta ciro waya, sai taga Ikram ce ta ɗauka tana cewa.

Ikee ya har kin dawo makarantar ne?"

Na dawo Anty saboda mu tafi kasuwar, sai na tadda har kin wuce umma tace ki tafi kar ki jirani, shine nace ki faÉ—a mini ina zamu haÉ—u yanzu na hawo mota na zo.

Sannu Hand back É—in Sameehan Umma, wato dole dai sai kin biyo ni, to nima yanzu zan dawo dan gaskiya kayan saloon É—in nan sunyi wuta sai na sake nazari da lissafi kan na siya, yanzu haka ina wani boutique ne zan siyawa su Abi kaya.

Haba Anty kema kin san sai umma tayi miki faÉ—a, yaran da ba ganinsu kika yi ba balle kice zaki siya musu, kuma kin san ubansu yana da kuÉ—in siya musu kaya, idan ma kin saya waye zai kai musu har Abuja.

Ikram yanzu tsakanina da yarana ba zan yi musu ihisani ba dan bana tare da ubansu, kawai kayan sunyi mini kyau ne shiyasa nace zan siya ko Yaya Kamalu zan aika masa ya aikawa Aminu. Tunda na kira na kira yaki ɗauka ƙiri ƙiri ya rabani dasu sai kace rabuwar kiyayya muka yi.

To wlh gwara ki fasa saya tun kafin ki zo umma ta rufeki da fada, keda kike niman kuɗin da zaki bunƙasa kanki zaki ɓarnatar dasu a iska ga yaran da suka yi miki nisa.

Dan na siyawa su Amrah kaya Wlh ba ɓarna bane, Ikram 'ya'yana ne fa, kawai dai zan fasa siyan tunda kin saka wannan bakin naki, na tabbatar kan na dawo kin haɗa mini bomb a gurin umma.

Ai gaskiya na faÉ—a kuma ko umma da yaya Zaidu abinda zasu ce kenan.

To naji Sameeha tace tana kashe wayar matar da suke cikini tana danna waya akan ta gama ta bada kuÉ—i, Saneeha da duk jikinta yayi sanyi, da kunyar tace mata ta fasa siya, haka dai ta daure ta cije tana cewa.

Hajiya kiyi haƙuri na fasa sayan kayan gudun faɗar ummata amma In Sha Allah naga waje da zarar na samu dama zan zo na yiwa yarana siyayya.

Ai daga jin wayar da kika yi na fahimci maganarki ba komai, amma ko ke ya kamata ki sayawa kanki abu muna da leshi atamfa da jakuna da takalma harma da gyale da kuma material, akwai wani da zai yi miki kyau bari na kawo miki.

A'a hajiya da dai kin barshi kawai sai dai wani zuwan In Sha Allah.

Matar ta miƙe taje ta ɗauko material ɗin ta miƙa mata lokacin Saneeha ta miƙe tana shirin tafiya, ita kanta material ɗin yayi mata kyau amma tace.

Idan rabona ne inna dawo wani lokacin zan saya kiyi hakuri banyi miki ciniki ba zan tafi.

Babu komai, kuma duba tara ne É—insa ba tsada, amma ina zuwa.

Sai shiga office ɗinta ta ɗauko jaka da key mota tare da ɗauko leda ta saka material ɗin a ciki, ta ƙaraso gurin Sameeha tana cewa.

Nima tafiya zanyi in ba damuwa na rafe mini hanya.

Wani kallo Sameeha ta yiwa matashiyar matar, wacce ba zasu wuce sa'anni ba ko ta girmeta da kaÉ—an ne, sai Khairy ta sakar mata murmushi.

Kiyi haƙuri naga kamar baki yarda dani ba, domin Allah zan rage miki hanya duk da ban san unguwarki ba hakanan naji kin yi mini. Sunana Ummulkairi Aliyu Turaki ina aure a sabon kawo yarana huɗu, Faisal, Hydar, Khadija da Humaira, sunan mijina Ahmad. A kaice kenan.

Mamaki ƙarara ya nuna a fuskarta wanda yasa ta saki baki ta kasa magana, Khairy tace cikin sanyin jikin.

Idan baki Aminta dani ba zaki iya tafiya amma har ga Allah da alkhairi a gare babu sharri, kuma banyi mamaki ba dan kin ƙi yarda dani saboda duniyar cike take da mutane ɓata gari marasa gaskiya, mutum abin tsoro ne.

Sameeha ta sauke ajiyar zuciya tana jin ba daÉ—i kar matar taga ko bata yarda da ita ba ne, kuma har ga Allah tsoron mutane take saboda abinda ya faru da ita a gidan Aminu, sai tace.

Babu damuwa ai hanyar muma ɗaya danni rafin guza nake, amma naga kamar baki ji daɗi ba, kiyi haƙuri kin san mutane ba gaskiya ina tsoron abinda zai je ya dawo mini.

Khairan In Sha Allah, saboda Allah naji ina buƙatar zumunci dake duba da kema ba yarinya bace, sannan ni ban da ƙawayen sai 'yan uwana shiyasa kawai nace in rage miki hanya.

Sameeha ta ce ba damuwa in ta shirya su wuce amma a zuciyarta cike take da zullumi da fargaba dan gaskiya tana tsoron mutane, musamman 'yan matan nan da suka yi mata sharrin lesbian, Khairy ta yiwa yaran shagonta sai da safe su kula idan wata matsala ta taso su kirata, sai suka fito suka wuce ta buɗe motarta data yi parking a gefen shagonta, ta shiga ta buɗewa Sameeha ƙofar gefenta ta shiga da bisimillah tare da addu'ar kariya a zuciyarta, ta kunna mota suka kama hanya, ba wani hira suke yi ba saboda Khairy ta kunna waƙar 'yan Sudan suna saurare, wani ma tana bi tamkar dai labaraci suke a wakar, Sameeha dai kallon hanya take tana tunani barkatai a zuciyarta.

*****

Aminu.
Chapter 38 · 0% Book details