← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 103

Sashe 74

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana gama faɗar haka ya fita daga ɗakin ya tafi zuwa ɗakinsa ba jimawa ya dawo da key ɗin ɗakin ya rufeta ta baya ya koma ɗakinsa ya kwanta a doguwar kujera yana mayar da numfashi, dukan da yayi mata yasa ya rage kaso ashirin daga cikin ɗari na baƙin cikin daya ke kunshe a zuciyarsa, jira yake safiya tayi ya je ya ƙaddamarwa Hauwa nata, dan yayi alwashin sai yayi mata borin da harta koma ga Allah ba zata manta shi ba, tausayin Sameeha ne ya rufeshi kamar zai yi kuka, ashe ba Hauwa bace kaɗai take son ganin bayanta hatta ƙanwarta ta jini take niman ganinta a ƙasa, wannan wace irin duniya muke ciki mai cike da mutane masu son kansu, lokacin daya soma jin hirarsu da Nafeesa yayi mugun kaɗuwa bai taɓa kawo Najwa zata iya tunanin aikata haka ba, ashe Nafeesan da ta ke kiransa akwai dalili, wato itama so take ta aureshi saboda ya zama soko mara lissafi, yara ƙanana suna niman wasa da hankalinsa, ya tabbatar Hauwa da nata manufarta data nima haɗa aurensa da Najwa, sai yayi ƙofa yana girgiza kai dan shi kaɗai yasan matakin da zai ɗauka.

*Watan Najwa ya tsaya fa asakata a addu'a*
[4/30, 4:57 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

44.

Aminu barci barawo ne ya ɗauke shi anan doguwar kujera sai kiran sallar asubahi ne ya tashe shi, ya miƙe ya fara yin wanka kafin ya saka jallabiya ya tafi masallaci bai dawo ba sai da gari yayi haske wajen shida da rabi, ya shiga falonsa ya zauna ya ɗauki wayarsa ya kira Junaid yayan Najwa, har kiran ya kusa tsinkewa kafin ya ɗauka cikin muryar barci, suka gaisa kana Aminu ya ce.

Dan Allah ina so zan baka saƙo gurin su Inna, ka sanar dasu su shirya ƙarfe takawas zuwa da rabi suje gidansu Sameeha zamu haɗu a can akwai muhimmiyar maganar da za muyi.

Ok ba damuwa In Sha Allah zan sanar dasu.

Yauwa nagode.

Aminu ya faɗi haka kana ya aje wayar, Junaid cike da mamaki ya tashi ya zauna yana tunanin me zaisa Aminu yace su inna suje gidansu Sameeha, da alama wani babban al'amari ne duk yadda aka yi, lamarin ya ɗaure masa kai wanda yasa ya kasa komawa barci sai ya cigaba da danne danne a waya da nufin zuwa anjima kaɗan sai ya sanar dasu inna tunda akwai sauran lokaci, kuma shima zai bisu dan ayi komai akan idonsa. Aminu kuwa miƙewa yayi ya shiga bedroom ɗinsa ya sauya kaya zuwa shadda ɗinkin tazarce, ya saka hula ya feshe jiki da turare sai ya ɗauki waya ya kira driver ɗinsa akan ya kawo masa mota, driver yace yana hanya ya kusa ƙarasowa, sai ya kashe wayar ya dawo babban falo ya zauna yana ɗan duba abu a waya.

Najwa.

Da kyar ta iya jan jiki ta hau gado ta kwanta daga haka barcin wahala yayi awon gaba da ita, ko kaya ta kasa sakawa sai bargo ta rufe jikinta dashi, ba ita ta farka ba sai ƙarfe shidan safe da minti biyar, ta buɗe ido sosai tana kallon silin wanda ya tabbatar mata da ba a gidansu ta kwana ba, abubuwan da suka faru a yinin bikinta suka dawo mata sabo, a hankali ta sauke numfashi tana jin wani tuƙuƙin baƙin ciki yana turniƙe ta, bata jin a tarihi akwai amarya kamarta akan irin abunda ya faru da ita a safiyar aurenta na dukan da Ikram tayi mata da kuma daren amarci da ango ya zaneta, komai ya lalace mata ta tadda bata yi tsammani ba, ta samu nasara akan auren Aminu amma kuma yazo a gaɓar da take jin dama bata same shi ba, bata so asirinta ya tonu ba da wuri duk Nafeesa ne ta ɓata mata komai, dana sani ne ya rufeta amma ba na nadama ba na tunkarar Nafeesa da maganar Aminu, tsabar wauta kuma har falonsa ta shiga suka yi magana yaji komai, tsananin haushin kanta ya rufe da kuma na Nafeesa tare da alwashin itama sai ta tona mata asiri, babbar damuwarta bata san ya makomar aurenta zai zama ba, zata so Aminu duk wulaƙancin da zai yi mata kar ya saketa dan taza jure duk wata uƙuba da wahala akan ya saketa ta zama ƙaramar bazarawa sakin wawa, dan in har ya saketa ya gama tona mata asiri ta san zaman kaduna sai ya nima ya gagareta, saboda maganar mutane sai yasa kamar tayi hauka, ta runtse ido hawaye yana kwaranta a kuncinta, ashe ma Aminu ba lafiya ce da shi ba da take ɗokinsa, sai duk taji wani sonsa ya fice mata a rai sai tsanarsa da yake maye zuciyarta, ko bai faɗa ba itama ba zata so ta zauna dashi ba har ƙarshen rayuwarta ba, domin zata so ta san ya namiji yake sannan ma ta haihu, kawai dai babbar damuwarta kar ya saketa yanzu ya ja mata gutsiri tsoma na mutane, zata jure zama dashi na shekara guda ko fiye zuwa lokacin ta tara kuɗin da zai isheta rayuwar zawarci kan tayi wani auren, ashe duk kyansa a fuska ne hoto ne shi Namiji ba abin, ina lafiya kuwa tunda babu ginshiƙin auren, data san da haka ba zata kwallafawa ranta son aurenshi ba da ta barshi da Sameeha su cigaba da zamansu tunda bama jin daɗin auren take yi ba zaman yara take yi, kuɗin ne a fili amma a baɗini cutuwa take yi, sai ta cije yatsa tana jin takaici yana rufeta da dana sanin da bata shiga lamarinsu ba tunda suna rayuwa da giɓi ne ba jin daɗinsa suke yi ba wannan kadai ya ishe su, sai gashi Sameeha ta samu wanda ya fishi lafiya kuɗi da komai ta samu duk wani abu na more rayuwa, Ikram ma ta biyo baya, ita ce dai bata zo duniya a sa'a ba. Babban maƙiyanta a yanzu da take jin in bata ɗauki fansa ba akansu ba zata rayu cikin salama ba, Nafeesa dole sai ta tona mata asiri, Ikram da Sameeha tana fatan ta samu damar da zata haifar musu da matsalar da ba zasu ji daɗin rayuwarsu ba, Aminu kuma da zata samu dama tabbas mutuwa ya dace dashi, domin ta samu babban kaso a dukiyarsa kafin yace zai saketa, dole ne ta zauna ta sake tsari yadda zata sauya daga wancan Najwa zuwa wata sabuwar Najwa, don ta kula a rayuwar nan in kana so ka zama wani abu to lallai sai mutum ya aje tausayi da imani kafin yake samun cikar burinsa, tun farko data bi shawarar Nafeesa akan ta asirce Aminu ta dage ta niman magani a waje mabambanta da ta samu kansa tuntuni, da bai isa ya yi mata abinda ya aikata jiya ba, kuma da alama malamin nan baiyi mata aiki mai kyau ba tunda ga sakamakon davta samu. Motsin shigowar Aminu data ji ya dawo daga masallaci yasa ta duba agogon dake manne a jikin bangon ɗakinta sai taga shida da rabi har da minti biyu, taja guntun tsaki dan ko sallar Asubahi bata yi ba ga kuma sallolin jiya data tara bata yi su ba, tunawa da hakan yasa ta miƙe da kyar ta sauko daga gadon duk jikinta yayi mata mugun tsami, a haka ta shiga bayin ta haɗawa kanta ruwa mai zafi tayi wanka da alwala ta fito, kayan jiya da Aminu ya cire mata su ta mayar ta yane gyalenta akai ta shimfiɗa dadduma ta shiga ramakon sallah a zaune dan jikinta babu ƙarfin da zata yi shi a tsaye, ta ɗauki lokaci mai tsaho tana abu guda, daga bisani ta idar kana tayi gajeriyar addu'a ta miƙe da kyar dan ƙafarta har tsami yayi ta isa jikin madubinta tana kallon irin yadda fuskarta tayi shedan bulala yayi ja, har wata 'yar rama tayi na wahala dan rabonta da abinci tun jiya da rana, sai yanzu ne ma ta fara jin yunwar tana taso mata amma halin da take ciki ko ta ga abinci ba zata iya wani ci ba dan sosai take fargaban Aminu ya saketa a yanzu, haka ta koma bakin gado ta zauna tana jiran shigowarsa dan ya rufeta ta baya balle ta iya fita ta haɗawa kanta ko ruwan tea ne ta jiƙa 'yan hanji.

Driver ya kawowa Aminu mota sai ya sallame shi akan zuwansu Zaria ba zai yuwu yau ba sai gobe In Sha Allah, kana yasa mai gadi ya buɗe masa gate ya fita zuwa wani rastaurant, oder ɗin waina da miya yayi musu sai ya saya ruwan gora da kuma coka drink ita kuma ya saya mata fanta, wajen bakwai da rabi ya dawo ya aje nashi a falo ya isa ɗakin Najwa ya buɗe ta tana ganinsa ta miƙe zubbur tana kallonsa a firgice dan gani take kamar dukanta zai kuma yi, baice mata komai ba ya aje mata leda ya juya ya rufeta ya koma falon ya zauna ya buɗe takeway ya soma cin wainarsa yana yi yana kurɓan coke, Najwa kuwa ƙamshin daya ratsa hancinta shine ya bata tabbacin abinci ya kawo mata, sai hakan yasa ta dan samu natsuwa da tunanin ƙila ba zai saketa ba, da sauri ta isa ledan ta zauna a gurin daya aje ta ciro takeaway ɗin ta soma cin wainar, duk yadda tayi tunanin ba zata iya cin abinci sosai ba ta kasa dan kusan waina biyar ne sai da taci huɗu kafin ta kora da ruwan fanta, taji ta ƙoshi sai ta mike taje bayi ta wanke hannu ta dawo ta saka takeaway ɗin a leda ta mayar da komai ta zauna a gefen gado tana jiransa.

****

Gidansu Najwa.
Chapter 74 · 0% Book details