Sashe 53
Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dama na samu matar da zan aura ne shine nace in fara yin magana daku kuje ku tambayar mini kafin su Baba Tijjani suje su kai kuÉ—in aure.
Alhamdulillahi masha Allah, Yaya naji daÉ—in maganar da Ibrahim yazo mana da ita dama abinda muke ta buri kenan addu'armu ta amsu.
Cewar Hajiya Fati, Hajiya kuma murmushi tayi tana cewa.
Ni kam wlh akwai yarinyar data kwanta mini dana so ka aura, wannan yarinyar ƙawar Khairy mai kama da Mubeena, duk da bazawara ce amma ni natsuwarta tayi mini kuma yadda khairy ke faɗar tarbiyyarsu ta dace a aureta duk da ba musan dalilin mutuwar aurenta ba. Amma ba damuwa ko wacece zaka kawo nasan ba zaka auro irin Nabeela ba, saika faɗa mana gidan nasu muje mu tambayo maka.
Murmushi Ibrahim yayi jin zaɓinsa yazo dai dai dana hajiya yace cike da natsuwa.
Hajiya itama zaki sota in kin ganta domin macece mai natsuwa kuma itama bazawara ce idan da hali yau Shamsu sai ya kaimu gidansu ku tambayo mini in ba a rigani ba dan bana so nayi nema a cikin nema. Kuma shima Shamsu yana son ƙanwarta shima sai a tambayo dashi dan yace mini yana zuwa zance amma basu gama daidaitawa ba.
Ikon Allah wai shamsu namu ne yake son ƙanwar wacce kake so? Hajiya kinji wani irin haɗaka, to Allah ya tabbatar da alkhairi yanzu ƙarfe nawa ne sai muje yanzu in dare bai yi ba.
Cewar Hajiya Fati, Hajiya kuma tace.
Yanzu kusan tara saura taya zamu je gidan mutane a wannan lokacin, a dai bari sai gobe In Allah ya kaimu.
Hmmm Hajiya ayi haƙuri aje yanzu ai da sauran dare, tun wancen satin naso ma aje a tambaya sai ban samu damar dawowa ba.
Ibrahim ya faɗa yana sunne kai ƙasa Hajiya tayi murmushi tana kallonsa ta tabbatar wannan yarinyar da yake so bada wasa yake ba, ta kalli kanwarta tace.
Fati tashi mu shirya muje dan tunda kika ga Khalil ya dage to bada wasa yake yi ba. Saika kira Shamsu ya fito da motata a ciki zai kaimu, Allah yasa dai mu samu karɓuwa a gunsu.
Hajiya ni zan tukaku a motata Shamsu kuma zai yi mana jagora a motarsa.
Au da kai zamu kenan.?
Hajiya ta faɗa tana kallonsa, Ibrahim yace uuum ya miƙe tana sosa kai ya fice tare da yin murmushi suma da murmushin suka raka shi suka miƙe zuwa ɗakunansu dan su shirya, saboda ɗaki guda aka warewa Hajiya Fati nan take jinyarta tamkar gidanta.
Ƙarfe tara da minti ashirin a ƙofar gidansu Sameeha tayi musu, Shamsu ya fito ya nuna musu ƙofar gidan yana cewa.
Hajiya nan ne gidan.
To sai ku koremu a mota mu fito, Allah yasa a baku aurensu dan wlh kunyi zari da yawa, ace duk ku biyun zaku auri 'yan gida É—aya.
Hajiya ta faÉ—a tana É—an murmushi suma murmushin suka yi Ibrahim bai fito ba yana mota dan gudun mutane su ganeshi su baibaye motar, Shamsu kuma ya koma nashi motar ya zauna zaman jiran fitowar su Hajiya.
***
Sameeha.
Suna zaune a falon umma suna kallo a tv Ikram kuma tana ƙarawa Anwar karatun Al-qur'ani a tsakar gida, sallamar da su Hajiya suka yi yasa ta ɗago tana kallonsu ganin kamar mahaifiyar su Khairy yasa ta ware ido dan ta tabbatar, ganin tabbas ita ce yasa ta miƙe da sauri ta shiga yi musu sannu da zuwa ta bawa Anwar Al-qur'ani tace su shiga falo tayi musu jagora, Hajiya itama mamaki ya cika ta ganin Ikram ƙanwar Sameeha, kenan dai zaɓinta shine zaɓin Ibrahim shine yaƙi faɗa mata direct, koda suka shiga Ikram ta sanar da su hajiyar su Khairy ce umma cikin fara'a itama ta miƙe tana yi musu barka da zuwa tare da nuna musu gurin zama Sameeha dake zaune a capet itama ta miƙe ta na yi musu sannu da zuwa har suka zauna kana suka gaishe sai ta basu guri ita da Ikram zuwa tsakar gida, suna mamakin ganinta amma kuma sanin Shamsu yana son Ikram ɗin suka bayar ko sun zo tambayar masa aurenta ne, umma bayan sun gaisa sai suka danyi jim umma ta kira Ikram akan ta kawo musu ruwa, ta je kitchen ta dauko plate mai kyau ta shigo ɗakin ta ɗibo ruwan pure water a fridge ta aje musu a gabansu ta fita Hajiya Fati tace.
Wannan itace Ikram ko wacce Shamsu ke nima.?
Eh itace.
Allah sarki to Hajiya ga baƙi mun zo niman iri nasan baki wayemu ba amna su yaran sun gane mu. Nice mahaifiyar su Khairy wannan kuma ita ce Ƙanwata Fatima mahaifiyar Mubeena da ta rasu wacce take kama da Sameeha.
Allah sarki sannunku da zuwa ita kuma Allah ya jikanta.
Ameen, Ibrahim da Shamsu sune suka taso mu cikin daren nan akan a nima musu auren yaranki Sameeha da kuma Ikram, Allah yasa ba a rigamu ba.
Umma sai yaji abin daga sama domin tasan Ikram ne kaÉ—ai Shamsu ke so har yake zuwa hira bata san da zancen Sameeha ba sai tace.
Ikram dai ko kuke magana, dan maganarta ne kaÉ—ai na sani bansan na Sameeha ba.
Eh Muma yau muke sanin Ibrahim yana son Sameeha dan ɗazu ya zo ya sanar damu maganar shice muka taso ƙafa da ƙafa mu nima musu izini. Ibrahim shine yayan Khairy da duke uwa ɗaya uba ɗaya, Shamsu kuma ɗan yayanmu ne dake Zaria. Allah yasa ba a rigamu ba.
Allah sarki, to kunsan yaran zamani baka da damar yi musu zaɓi sai abinda suke so dan samun maslaha, amma ba wanda aka tsaidawa miji a cikinsu kuma ita Sameeha kunga yanzu itake da damar yiwa kanta zaɓi, Ikram ma da take budurwa sai ta yarda zamu aura mata, bari na kira su su shigo muji ta bakinsu.
Eh hakan ma yayi kira su muji.
Cewar Hajiya, Umma ta miƙe ta fito tsakar gida tace su shigo sannan Anwar yaje ta kira yayansu dake ɗakinsa yazo, sai suka shiga ciki umma ta zauna a mazauninta kan cushing su Sameeha suka samu kan carpet suka zauna, gabaɗaya sun bayar da zancen Ikram ne ya kawo su, sallamar Yaya Zaidu ne ya katse tunaninsu ya samu carpet ya zauna yana gaishe da su Hajiya suka amsa fuska sake Umma tana cewa.
Wannan shine babban yayansu na kira shi domin ayi maganar a gabansa. Zaidu, Sameeha, Ikram magana su Hajiya suka zo da ita akan zancen nima wa yaransu aurenku to nace musu duk abinda za a yi dole sai da yardanku.
Nan ta kwashe komai a takaice ta sanar dasu, Sameeha kam zuciyarta ne ya shiga luguden bugawa jin wai Yayan Khairy ke sonta, ita data yankewa kanta zancen ba zata yi wani aure ba koma zata yi ba yanzu ba, sannan ma a yadda tasan matsayinsa ai yafi ƙarfinta ina iita ina auren Senator, maganar yaya Zaidu taji yana cewa.
Sameeha kinji da zancen da suka zo kin amince ko kuma a baki lokaci?
Shuru tayi tana jin nauyin su hajiya idan tace ba ta amince ba, dan gaskiya bai dace ta nuna bana amince ba kai tsaye, suka aje duk wata mulki da kimarsu da darajarsu suka sauke su tare da daidaita matsayinsu dasu suka zo nimawa yaransu aure bai dace ma tace a'a ba.
Kinyi shuri, kiyi magana karki takura kinki muma zamu fahimci duk abinda kika yankewa kanki.
Cewar Hajiya Fati, Sameeha ta ƙara sunne kai tace cikin dakiya.
Duk hukuncin da Umma da yaya Zaidu suka yanke a kaina shi zan bi muddun suka amince ko akasinta.
To ke Ikram meye zaɓinki, kin yarda da auren ɗansu?
Zaidu ya faÉ—a yana dubanta.
Nima duk abinda kuka yanke na amince da shi.
Tana gama faɗar haka ta miƙe da sauri ta fice tana ɗan murmushi, Sameeha ma miƙewa tayi tabi bayanta suka fice, umma tayi murmushi tana cewa.
To kun ji abinda suka ce kuma idan tani ne na amince. Sai dai basan shi Zaidu ba.
Ai umma tunda kika amince nima na amince dan amincewarki ne zaɓinmu gaba ɗaya.
Ya faÉ—a yana 'yar dariya, suma sai suka saka yi murmushi suna hamdala tare da jera musu godiya.
Mungode Allah ya saka da alkhairi yasa a ƙulla alkhairi yasa gidajen zamansu ne. Mun baku dama kune kuyi bincike akanmu kuma nan da sati mai zuwa maza zasu zo ayi maganar aure dan muna so ayi shi nan da wata biyu ko uku.
Da wurwuri haka? to Allah ya tishemu alkairi.
Cewar umma tana dariya, suka amsa da amin kana Zaidu ya fito ya basu guri suka cigaba da hira tamkar sun jima da sanin juna, Basu suka bar gidan ba sai bayan ƙarfe goma har gate umma da Zaidu suka yi musu rakiya suka tafi, umma tana dawowa cikin gida ta zube akan tabarma ta dubi gaban tayi sujjadar godiya ta ɗago tana cewa.
Rabon da naji farin ciki irin na yau harna manta, lokaci guda a gida guda aka nima aurenku, ina ma mahsifinsu yana raye ya tayani wannan farin cikin.
Sai ta fashe da kukan murna, Ikram ma sai ta samu kanta cikin farin ciki dama ta daɗe tana addu'a da alama Shamsu shine alkhairi a gareta, Sameeha kuwa ta kasa gane wani matsayi take ciki farin ciki ko damuwa, kallonsu take yi tana murmushin yaƙe, Zaidu ya zauna yana cewa.
Matar Senator, hohoho wa zai hango mini idon su Hauwa suga yadda Ubangiji ya É—aga dajarki hassadarsu ya zame miki taki, kin auri wanda yafi É—an uwansu matsayi, kuÉ—i, mulki, daraja da komai, wlh wannan lamarin aya ce Ubangiji zai nuna ga duk masu hassadarki Sameeha, ke dashen Allah ce gashi a dalilinki itama Ikram zata lashi tagomashin arziki, umma kinyi farar haihuwa albarkanki tana yawo da naso a cikin rayuwarmu, Allah ya saka muku da gidan aljanna keda baba.
Ya faÉ—a yana jin hawayen farin ciki yana cika masa ido, maganganunsa yasa Sameeha taji damuwarta ya yaye farin ciki ya maye zuciyarta gabaÉ—aya, nan dai suka dinga firar maganar har lokacin barci yayi suka shiga É—aki, Anwar ya É—age tabarma kowa ya nufi makwancinsa cike da farin ciki.
****
Ibrahim.