Sashe 64
Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Cewar Sameeha tana dariya Ikram ma dariyar tayi ta fice zuwa falo. Sai wajen tara da rabi Shamsu yazo ya É—auketa suka wuce gida cike da farin ciki.
***"
Aminu.
Tunda ya tabbatar da an ɗaura auren Sameeha da wani ya kulle kansa a ɗaki da yake weekend ne ba aiki, yaci kukansa ya gode Allah daga bisani yayi mata addu'ar fatan alkhairi yasan ya rasata har abada dan abune mai matuƙar wahala ta fito daga gidan mijinta, saboda yadda yasan ta da iya kula da miji, haka ya yini yata tunanin rayuwarsu ta baya, ko yaransa a ranar sun san babansu yana cikin damuwa shiyasa basu takura shi ba da yake basu san mamansu tayi wani aure ba, baaba ce kawai ta sani itace ma ta dinga kwantarwa Aminu da hankali. Wajen misalin ƙarfe tara na dare yana zaune yana kallon tv, rabin tunaninsa yana ga Najwa da duk ranar basu yi waya ba wanda in bai kirata ba zata kirashi, sai ya bayar ko kila wani uzurin ne ya riƙe ta, yana cikin tunanin ya kirata sai wayarsa ta soma kuka ya duba yaga baƙuwar number ne, kamar ba zai ɗaga ba sai ya ɗauka ya kara a kunnensa yana sallama, ɗaya ɓangaren kuma Nafeesa ta amsa cike da natsuwa ta gaishe shi ya amsa yana tambayar wacece, sai da ta gyara kwanciyarta ta daidaita natsuwarta kafin ta amsa da cewa.
Sunana Nafeesa Sabo Mai kanti, na siya waya ce second hand a hannun wani mai sayar da waya sai na tsinci number ɗinka a cikin wayar, dalilin daya saka na kiraka saboda sunanka ya kasance sunan fiyayyen Halitta ni kuma duk abinda ya danganci Manzon Allah s.a.w yana matuƙar burgeni. Allah yasa ban takuraka ba.
Ta ƙare maganar tana jan fasali, Aminu kuwa yadda ta jero masa bayani ta kuma sako fiyayyen Halitta s.a.w sai hakan yayi matuƙar kayatar dashi, ya ƙara riƙe wayar yana cewa.
Masha Allah kuma baki takurani ba sai dai nayi mamakin ƙarfin halinki na kiran wanda baki sani ba.
Hakane amma na tabbatar Aminullah ba mai cutarwa bane domin suna linzami ne.
Gaskiya ne ina godiya na yaba halina duk da baki waye ni ba. Nagode.
Nice da godiya daka saurareni amma in ba damuwa zan iya cigaba da kiranka muna gaisawa saboda soyayyar Manzon Allah s.a.w .
Tunda kika ce Manzon Allah s.a.w ai kin gama magana, kuma masoyina ne da babu tamkarsa a duk duniya, ina kuma son mu'amala da duk wanda yake ƙaunar Rasulillahi.
Nagode sosai a gaida iyalin, zan barka haka karna cikaka da surutu. Idan kana yin WhatsApp chart zamu riƙa gaisawa ta can dan ba kowa ne ke son amsa waya ba.
Ayya? ni chart bai dameni ba amma gaisawan ma ba damuwa nagode.
Nima na gode sai da Safe yaya Aminullah.
Bata jira amsar sa ba ta kashe wayar tana sakin murmushin farin ciki, shima Aminu tsintar kansa yayi yana yin murmushi dan sosai yaji ta rage masa damuwar da yake ciki saboda tsara zancenta, tunatar dashi da tayi akan soyayyar Manzon Allah s.a.w, sai nan take ya soma yi masa salati saboda yasan yin salati ga Annabi s.a.w waraka ce daga damuwa, mafita ce daga ruÉ—ani, sannan kuma kuma samar da farin ciki da natsuwar ruhi.
Muje zuwa....
[4/23, 8:47 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*
39.
Aminu a daren saida ya rayashi da sallolin nafila ya mayar da lamarinsa ga Allah, kafin daga bisani ya samu barci mai daɗi sosai, haka ya wayi gari wasai ba tare da sauran damuwa ba, hakika ya ƙara tabbatar da duk wanda ya bar Allah to shima sai ya barshi, da tun farko ya mayar da lamarinsa ga Allah to ba zai tsinci kansa a damuwa da auren Sameeha ba. Bayan ya kammala karyawa sai ya tuna da Najwa hakan yasa shi kiranta, wayar harta tsinke bata ɗauka ba a kira na biyu ne ta dauka bayan sun gaisa yake tambayarta lafiyarta tace tana fama da ciwon kai shine yasa ma jiya bata kira ba, yayi mata fatan samun lafiya kana suka ɗan taba hira daga bisani suka yi sallama akan zai kara kira anjima yaji jikinta, yana ƙoƙarin miƙewa saƙo ya shigo wayarsa ya duba yaga number jiya ce da ko saving bai yi ba, ya duba saƙon tana cewa.
Barka da safiya mai babban suna fatan ka tashi lafiya ya kwanan iyali? Na duba ka a WhatsApp sai naga baka hau ba shiyasa na gaisheka ta nan, ka yini lafiya.
Guntun murmushi yayi yana cewa a fili.
Allah mai mutane kowa da irin halinsa da tunaninsa, ita Najwa da zan aura bata damu da saƙo haka ba amma ga wata ta damu dani.
Ya kuma sakin murmushi kana ya miƙe ya wuce zuwa bedroom dan yayi wanka ya fita zuwa gurin wani likita da aka haɗashi dashi domin tattauna matsalarsa.
****
Nafeesa.
Tunda ta bar gidansu Najwa take tunanin yadda zata kira Aminu, harta isa gida tana tunani, da yake ba wani aiki zata yi ba sai ta kwanta a gado ta hau facebook tana duba abubuwan da mutane suka ɗaura, a nan taci karo da wani video na wani malami da yake magana akan Monzon Allah s.a.w, yayi bayani sosai akai, wannan ne ya bata damar yin tunanin hanyar da zata ɓullowa Aminu kuma cikin ikon Allah tayi nasara har ya ɗauki wayarta kuma ya saurareta, wato taci arzikin Manzon Allah s.a.w kuma ga dukkan alamu zata cimma nasara tunda ta kula Aminu yana da sauƙin kai, koda gari ya waye ta duba shi a WhatsApp bai hau ba sai ta yi masa saƙo duk da bata saka a ranta zai mata Reply, ta ɗan tsaya kaɗan bayan ta tura taji shuru sai kawai ta kunna data ta cigaba da sabgoginta, ba jimawa Najwa ta kirata take sanar da ita abinda Shamsu yayi mata jiya, Nafeesa kamar zata kwashe da dariya dan ba karamin daɗi taji ba dama sai da tayi addu'a akan kar Allah ya bata nasara dan ta fara gajiya da son zuciyar Najwa, sai tace cikin kulawa.
Gaskiya banji miki daɗin haka ba, yanzu yasa kin ji kunya, amma ni shawarar da zan baki ki ɗaure kije har gidan Sameeha ki bata haƙuri na san zata yiwa Ikram magana ta yafe miki, kin ga saiku koma zumuncinku ba tare da wani tangarɗa ba.
Allah ya kyauta naje na sauke kaina gaban Sameeha, ai ni dasu mun raba jaha kowa tashi ta fissheshi, dama an gaya miki inna auri Aminu zan yarda muyi hurÉ—a dasu ne, hmmm nifa wlh bani ba su, kuma Shamsu yaci bashi saina yi masa mummunar tabo da ba zai manta ni ba, dani yake wasa.
Daɗi na dake Najwa riƙo baki da yafiya, kuma fa ke ce mai laifin amma sai kiyi kicin kicin ki azawa mutum, kawai ki bar komai ya wuce ki fuskanci aurenki tunda ya kusa.
Hmmm Nafeesa naga kin fara saduda kina bin bayan su Sameeha, kodai da wata a ƙasa ban sani ba.
Haba Najwa duk abinda nake faɗa miki domin cigabanki ne kuma kin san ke tawace bazan taɓa juya miki baya ba, kiyi tunani da kyau, ba kida kuɗi ko ƙarfin da zaki tunkari Shamsu ki rama abinda ya yi miki, dan wlh idan kika dage sai kin rama to kwaɓarki zata yi ruwa kuma ina mai tabbatar miki da zaki saka kanki a matsala, suna da mulki da kuɗi ke kuma ba ki da komai tunda baki auri Aminu ba balle kiyi tutiya dashi.
Hmmmm Najwa ta sauke ajiyar zuwa domin duk maganar Nafeesa gaskiya ce, hakan yasa ta karaya tace cikin sanyin jiki.
Shikenan na bar komai ya wuce, amma yaushe zamu haÉ—u mu fara shirin bikina tunda lokacin ya fara matsowa zan mayar da hankali akan haka.
Yauwa ko kefa, kibari next week mu huta sosai lokacin sai mu haÉ—u mu yi maganar, sannan ya batun zuwa gurin malamin dana baki shawara.
Sai kin zo muyi maganar.
Cewar Najwa, da haka suka yi sallama. Haka Najwa ta kama ƙumbiya ƙumbiyarta bata bari Inna ta gane komai ba, dan dagewa tayi ba tada lafiya shiyasa bata je gidajen Amare ba, saboda Inna ta matsa lallai sai taje amma ganin ba lafiya ce da ita ba yasa ta rabu da ita kuma yadda ma taga bata fita ko ina yasa ta yarda da rashin lafiyar nata har tana saka Sadiq yana siyo mata magani.
*****
Sameeha.