Sashe 67
Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kasan kana son mamansu ka saketa, ai da sai ka zauna da ita duk laifin da tayi maka, taya zata kuhunta yara da laifin da basu aikata ba, Aminu kada da son zuciya ya rufe maka ido ka riƙa aikata ba daidai ba, taya zata raba yara da uwarsu alhalin tana raye, duk da kun rabu wlh baku rabu ba domin yaran nan sun riga sun haɗa ku, idan kai ba zai yuwu kayi zumunci da ita ba to su bai dace ka shiga tsakaninsu ba, naga ma ƙoƙarin Sameeha data zuba maka ido har tsawon wannan lokacin bata buƙaci ka dawo mata da yara ba, in wata ce wlh kotu zata kaika tunda in Abi Musulunci ya baka ka riƙe shi ai Amrah musulunci ya bawa Sameeha damar ta riƙe ta har sai ta kai munzalin balaga, kayi tunani da kyau idan ƙanwarka aka yiwa haka ko ɗiyarka zaka ji daɗi ne, yau ko baram baram kuka rabu bai dace ka rabasu da uwarsu ba dan ba a sauyawa tuwo suna, uwa uwa ce ba a shiga tsakanin ɗa da uwa.
To Baaba In Sha Allah zan gyara.
Ya dai fi maka tunda kaga aurenka yana ƙaratowa sai ka kaisu can wajen mahaifiyarsu, mu mu tafi Kaduna ayi biki damu na yi zumunci da 'yan uwa, in yaso kaima sai ka samu damar ganawa da Amaryarka ba tare da takuran yaran ba, ni in an kammala biki zan komon nan Abujan na samesu, in ka dawo shikenan.
To baaba za a yi yadda kika ce, Allah ya kaimu lokacin.
Ta amsa da Amin kana ta miƙe tabi bayan yaran, shi kuma Aminu ya shiga mazarin maganarta, kuma tabbas yasan gaskiya ta faɗa amma a zuciyarsa bai so yaran su zauna hannun Sameeha ba, amma tunda Baba ta saka baki zaiyi haka ya huta tunda zai zamu damar yin bikinsa kuma shima zai zo Sameeha tasan aure zaiyi, hakan zai bashi damar ta gane ya samu lafiya taji haushi, wanda kuma lafiyar har yanzu bai samu ba yanata lallaɓawa ne da shan magunguna da aka ɗaura shi, wanda dai har yanzu ba wani sauyi.
A ranar da dare ya kira yaran yayi musu alƙawarin zai tura su gurin mamansu su zauna a gurinta saboda zai yi tafiya shi da baaba, a can zasu cigaba da zuwa makaranta, amma sai nan da karshen wata, sunji dadi sosai duk da ba a daɗe da shiga sabon wata ba dole suyi hakuri har lokacin tunda yayi musu alƙawarin haka.
****
Najwa.
Shirye shirye take yi sosai dan ta mayar da hankali kan bikinta, gashi an bugo kati tana ta yawon rabo ita da Nafeesa, wanda a cikin hakane suka koma gurin malamin nan ta bashi kuɗi akan yayi mata aikin da ko Aminu ya ga itace matarsa bazai yi mata wulaƙanci ba balle ya rabu da ita, malam ya tabbatar da aiki kamar yankan wuka haka zai yi mata, daga bisani suka wuce Nafeesa tana ƙara mata ƙarfin guiwa, wanda ita kuma a bayan fage tana ta tusa kanta ga Aminu, a yanzu har ta fara jan ra'ayinsa yana charting da ita duk da ba wani hira suke yi ba amma sukan ɗan taɓa hirar duniya, sannan ma yayi mata alƙawarin duk in ya shigo Kaduna zai zo su gaisa, kuma ya sanar da ita aurensa tayi masa fatan alkhairi da addu'a, ganin bata nuna masa komai ba kan batun aurensa yasa shi ƙara sakin jiki da ita, dan a tunaninsa ƙila sonsa take yi da take yawan matsa masa da waya ko text sai kuma yaga saɓanin haka.
Biki saura kwana biyu.
Aka kawo akwatin Najwa guda Huɗu da kit yaji kaya ba laifi su Hauwa sunyi kokari sosai sun gwangwaje Najwa, maza suka kawo akwatin hakan yasa babu wanda ya gane daga dangin Aminu ne aka kawo dan sai da suka kawo a daren jiya inna ta kira 'yan uwa yau suka zo ganin kaya ciki har da Umma, ta kira Ikram yazo tace ba zata samu zuwa ba saboda ta tafi gidan Khairy kuma ƙarya ne ba inda taje zuwan ne ba zata yi ba dan tace sai ranar ɗaurin aure zaje ita da Sameeha. A ɓangaren Najwa sam kaya baiyi mata ba yadda take so, amma ya zata yi tasan dai bata isa ta haɗa kanta dasu Sameeha ba, tunda ko ƙaramin zinari basu saka ba sannan babu key mota a ciki, kadaran kadahan ta nuna farin cikinta. A lokacin da Nafeesa ta zo ta gani sai da Najwa tayi mata ƙorafin akwati bai mata ba Nafeesa tayi dariya tace cewa.
Niko banga aibun akwatinki ba Najwa domin sunyi ƙoƙarin saka miki kaya masu tsada, ni da zan samu irin haka zan so wlh, Allah ya saka ni a damshin ki.
Haba haba wlh kiyi fatan naki yafi nawa, ai ni Hauwa ta bani mamaki duk cika bakinta bata saka kaya na gani na faÉ—a ba, yanzu haka Aminu ya bata kuÉ—i masu yawa ta coge wasu dan nasan halinta da mugun son banza.
Hmmm yau keda Hauwa za a ji kanku kenan, aiko sunyi ƙoƙari Najwa ki godewa Allah a haka.
Hmmm kina zaton yadda suka yiwa Sameeha haka zan zuba ido suyi mini, ai wlh mace tayi katdan duk ubansu zanci ki dai zuba ido kiyi kallo duk zan yi maganinsu, ba dai buƙatata ta biya ba to an gama magana.
Ohhh Najwa Duniya, wato kice shigo shigo ba zurfi kika yi musu dan ki cimma muradinki.
Hahaha Nice fa ake faÉ—a miki, kina zaton Hauwa ta yarda da aurena ne hakanan, hmmm to itama taga zata juyani ne yadda take so ne shiyasa ta dage da ayi auren domin cikar muradinta, saboda Sameeha ma turje musu data yi yasa suka tsaneta.
Lallai kice kowannenku yana da manufa a auren nan, to Allah ya baki sapa a kansu, dan wlh in kika yi musu bore ba ƙaramin rikici da tashin hankali zaki jawowa kanki ba. Ki dai bari ki kama Aminu a hannu yadda zaki ji daɗin yi musu abinda kika yi niyya.
Murmushi Najwa tayi dan ita kaÉ—ai tasan yadda zata yi maganin su Hauwa, sai sun ce Sameeha nafila ce dan ba zata É—auki iskamcin da suka yi mata ba.
*****
Abuja.
Sameeha ta gama shiri a ranar juma'a zata tafi Kaduna domin bikin Najwa, wanda Jirgin kasa zata bi tare da securety saboda shi Ibashim ba zai samu zuwa ba dalilin aiki, ranar Alhamis tana zaune a falon ƙasa tana magana da Ikram a chart sai ga kiran Aminu ya shigo wayarta, bata yi mamaki ba dan tasan dole watarana zai nimeta dan tasan yaran zasu matsa masa akan ya kawo su gurinta, ya kusa katsewa kafin ta ɗauka suka gaisa kana ya sanar da ita zai kawo mata yara saboda aurensa ya matso, tayi mamaki sosai wanda yasa ta kasa haƙuri tace.
Ashe ka samu lafiya kenan? Wacece zaka aura? Allah yasa wacce zata kula mini da tarbiyyan yarana ne.
Inna samu lafiya inma ban samu ba wannan bai shafeki ba, ki tura mini adireshin gidanki driver zai kawo su yanzu.
Tace ok tare da yi masa fatan alkhairi bata jira amsarsa ba ta kashe waya, nan take ta tura masa adreshinta ta massage, sai ta miƙe da sauri ta hau sama dan ta duba ɗakin da zata sauke su, sosai ta samu kanta a farin ciki wanda har a fuskarta ya nuna, ta kira Ibrahim ta sanar dashi shima murya ya tayata yace ta gyara musu masauki kana yace zai tawo musu da kayan ciye ciye na tarba dan sosai yake so ya saba da yaran, suka yi sallama ta cigaba da shirya ɗakin kusa da nata akan Abi ya zauna a nan Amrah ta sauka a ɗakinta, ita kuma ta riƙa kwana ɗakin Ibrahim dan dama nan ne makwancinta basu taɓa raba ɗaki ba in yana gari sai dai in baya gari ne take kwana ɗakinta, tayi kamar ta kira Umma ta faɗa mata sai kawai ta fasa dan dasu zata je Kaduna suga su Umma in yaso lahadi ko monday sa dawo saboda makarantarsu duk da taso sai tayi sati biyu kan ta koma amma saboda yaran zata dawo da wuri. Wajen karfe biyar da rabi sai gasu Driver ya kawo su ya sauke su da kayansu ya juya, Sameeha ta fito da saurinta suma suna ganinta suka ruga suka rungumeta sai farin ciki suke, ko ba komai zasu ɗebe mata kewarsu kwana biyu, tunda aure yayi tasan zai kwana biyu a Kaduna bai dawo ba in ya dawo ma da amaryansa yana buƙatar kaɗaicewa da ita, haka suka wuce cikin falo ta wuce dasu sama, sai da ta sada Abi ɗakinsa ya aje kaya sannan suka wuce ɗakinta suka zauna bakin gado suka shiga hirar yaushe rabo, Sameeha sai tambayarsu karatu take yi suna faɗa mata, a haka har aka kira sallar magrib kafin suka yi alwala suka yi sallah a tare kamar yadda suka saba a da. Ibrahim sai bayan sallar Isha'i ya dawo ya samesu a falo sun gam acin abinci, da fara'arsa ya shiga ya same su Abi ya gaishe shi ya amsa fuska sake, Amrah kuwa gum tayi sai da Sameeha tace ta gaishe shi kafin ta faɗa, Ibrahim ya kirata ta maƙe kafaɗa sai ya shiga ciro kayan ciye ciye daga leda, Amrah tana gani ta miƙe tsalam ta isa gurinsa, sai ya lakaci hancinta yana cewa.
Ba zaki zo ba sai da kika ganni da kayan kwaÉ—ayi ko, ya sunanki?.
Amrah kuma zaka baki chocolate É—inka?
Ta faÉ—a tana marairaicewa.
Zan baki tunda kin zo guna amma daga yanzu nima Abba ne ki daina jin tsorona.
Ta gyaɗa masa kai alamar to kana ya miƙa mata kayan yace ta ɗiba abinda take so, shima Abi ganin an bata dama yasa shi miƙewa yazo ya kwashi nashi, Sameeha ta miƙe tana cewa.
Muje kayi wanka ka huta tunda ka samar musu abin hira nasan ba zasu damu ba.