Sashe 4
Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Eh lallai akwai babban aiki a gurin Zaidu da su Ikram dan ba dani za ayi wannan hirar ba.
Cewar Umma tana 'yar dariya, suma dariya suka yi suka shiga ɗakin umma wanda yake madaidaicin falo ne da kuma uwar ɗaka a ciki, akwai kujerun zamani da kuma kayan kallo a ciki, Sameeha sosai take fito da ummanta dan tana kashe musu kuɗi sosai sam basa cikin matsin rayuwa duk da Mahaifinsu ya rasu, umma ita ce kaɗai matar Malam Aliyu, asalinsa shi ɗan Maiduguri ne zama ne ya kawo iyayen iyayensu Kaduna har suka yaɗu, umma kuma 'yar nan kaduna ce fulanin Zaria, a nan suma iyayenta suke a unguwar kawo har Allah ya haɗa ta da Aliyu ya ganta suka yi soyayya har ya aureta ya ajeta a nan gidan gadansu dake nan kawo, yana aikin sayar da kayan mashin a nan kasuwar kawo har Allah ya hore masa ya gida masu wannan gidan da suke ciki a rafin guza, Zaidu shine ɗansu na farko sai Sameeha da kuma Ikram sannan Usman da suke kira da Anwar dan ya ci sunan mahaifin babansu. Anwar yana ƙarami Baba ya rasu wanda mota ce ta bigeshi a babban titi kawo nan take yace ga garinku, kaf danginsu ba wani mai ƙarfi umma ce ta tsaya akan ƴaƴanta tana sana'ar sayar da waina a cikin gida tana biya musu kuɗin makaranta har suka kawo girma, Zaidu shine ya samu yin digree wanda Saneeha a iya secondary ta tsaya. A taron walimar saukarta na Al-qur'ani ne da ya zo ɗaya da walimar 'yar gidan yaya Kamalu dan ajinsu ɗaya a islamiyarsu dake a sabon kawo, shi ne Aminu yaga Sameeha a wannan taron ya kamu da sonta, har ya bi ta hannu Laila 'yar Kamalu ya kafa soyayyarsa a gurin Sameeha. A haka dai soyayya tayi ƙarfi har ya kaisu ga yin aure wanda ana ɗaurawa washe gari aka wuce da Sameeha Lagos in da yake aikinsa. Tun da Sameeha tayi aure umma ta dena wahalar aikin waina dan duk wata take yi musu aike da kuɗin da zai wadace su, har sunan Zinariyar dangi ake kiranta saboda ta fita zakka dan ta auri mai rufin asiri sosai, dangin umma gidansu gidan yawa ne amma a ɗakinsu su biyu ne rak umma Halima itace babba sai kanwarta Rukayya, ita tana aure a can Zaria da zuri'arta. Dangin Baba kuwa akwai wansu Baffa Talle da suke uwa ɗaya uba ɗaya dan du uku ne a ɗakinsu, yana zaune a cikin gidan family hause ɗinsu, sai kuma ƙanwarsu Gaggo Zulaihatu tana aure a badarawa, sannan sauran waɗanda suke 'yan uba maza uku mata biyu, dan mamansu ita ce amayar kuma duk sun rasu har da kishiyarta da mahaifinsu, ya rage yaran ne kuma sun rike zumuncinsu sosai. Goggo Zulai tana da yara huɗu, Junaid da Abdullahi sai Sadiq da autarta Najwa, baba Talle kuwa Allah bai bashi haihuwa ba da yake baida cikakken lafiya, sai dai yaran 'yan uwansa yake riƙewa a matsayin nashi.
..
Suna gama cin abinci waina ce da miya yaji tantakwashi sai jelof ɗin shinkafa wanda umma ta dafawa su Abi kila ba zasu so waina ba, dan duk yara akwai ƙauna mai ƙarfi a tsakaninsu da shinkafa, wainar kuma sunyi ne saboda Sameeha dan tana mugun sonsa, sai kunun Aya mai daɗi da soyyyar kaza. Sameeha ta samu takeawy na roba ta zubawa Aminu soyayyar kazan ta kulle a leda kana ta ɗaukar masa kunun aya da aka zuba a medium ɗin gorar swan suka fito yayi sallama dasu Umma, sai ta rakoshi har mota ta saka masa kaza da kunun a mota suka yi sallama tana kara bashi haƙuri akan kar ya yiwa su Hauwa magana yavbar komai ya wuce, gyaɗa mata kai yayi yana murmushi ya tada mota ya wuce yana yaba kyawun halin Sameeha, mace ce mai rufin asiri da sanin yakamata, shiyasa har abada ba zai gushe ba gurin kyautata mata, haka ya tafi yana tunaninta da shiga kewar yau ba zasu kwana a tare ba.
Sameeha tana shiga gida suka gabatar da sallah kafin suka fito tsakar gida gabaÉ—aya suka zauna a tabarma, nan ta shiga bawa umma labarin abinda ya faru É—azun, umma tace cikin kulawa.
Ai ni banga abin ƙorafi ba a nan tunda mai sonka shike ɗokin ganinka, su Alhasan da basu yi musu magana ba, dan gyaran gida ko a nan zaki samu masu tayaki ku gyara.
Umma kenan na kula sam bakya so na faɗi ƙorafin su Hauwa, amma wlh gumunta ce kawai suka yi.
Wlh kuwa Anty mugunta ce taya zasu ɓata gida har kujeru sannan su kwashe muku ruwa da lemuka.
Cewar ƙanwarta Ikram data saka baki a hirarsu, umma ta nunata da yatsa.
Ba ruwanki a wannan maganar karna sake jin bakinki, ke kuma wlh ki shiga hankalinki dan banga amfanin wannan ƙananun ƙorafin ba, in ma da biyu suka yi muku haka kansu suka yiwa ai.
Murmushi Sameeha tayi dan ta san umma ba zata taɓa bin bayanta ba, tunda ta auri Aminu in dai ta kawo mata maganar anyi mata abu wlh umma bata bin bayanta sai dai wani abin ma ta bata laifi, shigowar Yaya Zaidu daya dawo daga masallaci ne ya katse muna hira ya samu karamar kujerar mata ya zauna yana cewa.
Mutanen Lagos ansha jirgi dan bazan ce hanya ba. Ya rayuwa da kuma halin da kasarmu take ciki.
Alhamdulillahi ai kasarmu sai addu'a, shuwagabanni ne gasu nan kowa ya samu dama sai dai yayi shanya, Allah yasa mu dace. Ya batun aiki har yanzu baka samu ba?
Ameen dai, aiki ya samu tunda na buÉ—e shagon aikin printing karashe ne ya rage na fara aiki, kinsan harkan ne yanzu komai sai da kuÉ—i.
To Allah ya taimaka, amma zan kara yiwa Abban Amrah magana in ya samu dama sai ya baka.
Ai nasan da ya samu zai nime ni kawai dai lokaci ne bai yi ba Allah yasa muna da rabo a gomnatin.
Suka amsa mishi da amin kana umma tace.
To kin ganshi nan aure yake nima a haka shi ba aiki amma yana nimarwa kanshi nauyi.
To umma ai ya kai ya aje iyali kuma In Sha Allah in ya É—auko mu zamu haÉ—u mu dafa masa, kuma muna da Allah.
Au haka zaki ce?
Cewar umma, sai Sameeha tasa dariya Zaidu yana taya ta yace.
Yauwa 'yar gari na san dama ko kowa ya juya mini baya ke kina tare dani. Kin san ma wacece?
Sai ka faÉ—a yayanmu.
Najwa ce 'yar gidan Goggo Zulai kinga abu ne na gida tuwona maina ba za a cika buri ba.
Kai amma naji daɗin wannan magana kunga zumunci zai ƙara karfi. Amma da fatan Najwan ta amince dan kar a tilastata.
Ta amince amma kinsanta da rawar kai, mu uku take tare damu wai saboda tsaro, tasan kuma cewa ni bana cikin mayaudara tunda ni na gidana.
A hankali zata rabu dasu kasan ba zai yuwu lokaci guda ba, har yanzu tana zuwa haddar ko ta haÉ—a?
Ta hadddace izu ashirin da biyar, kafin Aurenmu In Sha Allah zata haÉ—a.
Sameeha tace Allah ya kaimu, sai suka cigaba da hira, nan take Sameeha ta turawa Zaidu dubu É—ari a account É—insa dan tana da shi, yana gani ya kalleta yana murmushi.
Kuɗin gyaran shagonka ne ka ƙarasa Allah yayi jagora.
Cewar Sameeha, Zaidu yama kasa magana dan wlh gani yayi kuɗin sunyi yawa bai taɓa zato ba, ya kalli umma yana cewa.
Dubu É—ari fa ta tura mini umma.
Rabonka ne ya rantse, sai ka amsa kayi mata fatan alkhairi.
Cewar umma cike da jin daÉ—i, nan Zaidu ya dinga kwararo mata addu'a suna amsawa da amin, gabaÉ—aya fuskarsu cike da farin ciki da annashuwa duk da mahaifinsu baya raye amma suna cikin rufin asirin Allah babu wanda yake cikin damuwa, duk da Zaidu ne kaÉ—ai yayi karatu mai zurfi ya karanta computer seiance digree, ita kuma Sameeha iyakarta secondary duk ta taso ta cigaba amma Allah bai mufa ba tayi aure, Ikram data gama secondary ta cigaba da Islamiya sanawiyya yanzu aji biyar take itama ana jiran saurayinta ya fito ne ayi maganar aure, Anwar kuma yana aji shida a secondary yana shirin fita, suna da ilimin addini daidai gwargwado kuma sun samu ingantacciyar tarbiyya. Sai gabda magrib Zaidu ya fita su kuma suka yi alwala suka shige É—aki.
***
Najwa.
Bayan sallar isha'i Zaidu yaje zance, suna zaune a ƙofar gidansu kan dalaki ga hasken tantarki ya haska gurin, a cikin hirarsu ne yake faɗa mata Sameeha ta dawo, Najwa ta soma murna tana cewa.
Alhamdulillah naji daÉ—in dawowarsu kuwa da fatan suna lafiya.
Lafiya lau sunan a gidanmu zasu kwana gobe In Sha Allah zata koma gidanta da wuri saboda suyi gyare gyare.
Aiko zan zo nima a yi dani dan na ƙosa naga yadda gidanta ya tsaru, kasan ni a rayuwata ina mugun son harka ta masu kuɗi, balle kuma abu namu maganin a kwaɓemu na samu gidan yin walima in na tashi aure.
Hajiya Najwa sarkin son kuÉ—i, to kiyi fatan nima na samu kuÉ—i na gida miki gida na alfarma.
To Allah ya baka, wlh kasan ni abinda ke burgeni da masu kuɗi yadda suke rayuwa cikin sauƙi da jin daɗi, gida mai kyau motoci na alfarma ga kuma sutura mai kyau, kai komai masu mai kyau ne, mafarkina shine na ganni a irin wannan rayuwar.
Kiyi fatan Allah ya baki arziki mai albarka ba wanda zai zame miki damuwa ba, da yawan masu kuɗin da kike gani wlh damuwar da suke ciki na jarabawar da Allah yayi musu yafi ƙarfin tunaninki.
Kai yaya amma dai suna cikin kuÉ—i, ai da wani talaucin gwara kayi kuÉ—in Allah ya jarabceka ko ba komai mutum baya cikin wahala.
Allah ya kyauta to dan naga kinyi nisa, ni anya ma nan gaba in wani mai falleliyar mota ya zo gunki ba zaki rabu dani ba kuwa?
Kai yaya duk son kuÉ—i na bai kai haka ba, kuma ai mun gama magana lokaci muke jira, tunda ko wani bawa Arzikinsa yana goshinsa.
To yanzu naji kin yi magana mai kyau, ni bari na tafi sai zuwa jibi ko gata In Allah ya kaimu zaki ganni.