Sashe 87
Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na wuce haka ma in dai akan kaina ne, bazan yarda idona biyu ku cutar dani ba wlh.
In kin san wata ai baki san wata ba zan nuna miki iyakarki kuwa.
Saleema ta miƙe afusace ta bar ɗakin, Najwa ta ja guntun tsaki tana mele baki.
Kafin kiga iyakata ni zan ga naki ', wlh ko inna bata isa ta sa na auri wannan baƙar halittar ba balle ke.
Sai ta miƙe ta sakawa ɗakin key ta sauko da trolleyn kayanta ta saka waɗanda suke a wadrob a ciki ta mayar ta rufe ta kimtsa komai kana ta buɗe ɗakin ta samu Siyama suna kallo ta wuce kitchen ta saka abinci ta fito falon ta zauna tana cin abinci, Siyama ta kalleta tana cewa.
Anty Najwa Mama tace ta tafi sashin baba, in kinyi sallar asuba tace mu fere doya mu dafa sannan ki yiwa su Auwal wanka ki shiryasu kafin tazo nima sai nayi nawa shirin makaranta.
To Allah ya kaimu Najwa ta faɗa kana ta cigaba da cin abincinta a zucitarta tana ganin daidai lokacin da zata yi abinda take ganin shine daidai yayi, tunda Amty Saleema tana gurin malam yau ita ce da girki, data gama ci ta wuce ɗakin Saleema ta fara yi mata bincike a nan ta samu kuɗi a ƙaramar pos ɗinta cikin kaya ta ƙirga dubu talatin da uku ta saki murmushi ta kwaahe su duka, ta fito ta shiga ɗakinsu ta saka kuɗin cikin trolley ɗinta ta mayar yadda yake, sai ta bi lafiyar gado tana jin wani daɗi yana rufeta da guduwan data shirya yi, nan take ta seta alarm a wayar ƙarfe huɗu, sai ta koma ta cigaba da kallon data fara a youtube, a haka har Siyama ta shigo kwanciya Najwa tace.
Su Auwal sun kwanta ko?
Eh tun É—azu.
Kin rufe ƙofa ne.
Eh na rufe.
Ok sai da safe.
Najwa tace mata Siyama ta amsa tare da kwanciya kusa da ita ba jimawa barci ya ɗauketa, itama Najwa aje wayar tayi a ƙarƙashin filo ta rufe ido dan tayi barci saboda ta samu ƙarfin tashi.
Ƙarfe huɗu na dare alarm ya tashe ta ta tashi ta zauna sai ta cigaba da zama har kusan ƙarfe huɗu da rabi lokacin ne barcin ya saketa, ta sauko daga gadon a hankali ta zura babban hijab ɗinta ta sauke trolley ta buɗe ɗakin ta fito falo ta jawowa Siyama ɗakin, sai ta isa ƙofar fita ta murɗa key ta buɗe ta fita da addu'ar kariya daga shaiɗanun dare, ta kuma rufe ƙofar sai ta ɗaura trolley a kanta ta bi bayan gidan ta wuce part ɗin Amaryar malam cikin sanɗa, har ta dangana da katangar baya sai ta ganta tana da tsaho amma da yake ta sakawa ranta sai ta fita, a gefe ta aje trolley kayan ta juya ta hango wani dogon benci na masu aikin fenti ne suka barshi a gurin, cikin dabara ta ɗauko shi ta ƙara a bangon sai ta ɗaura trolley ɗin akai itama ta hau, da dubara ta ɗaura trolley ɗinta a katangar itama ta hau daga gefen kayanta, sai ta tura trolley ɗinta ya faɗa waje itama ta diro akan trolley ɗinta, nan ta miƙe da sauri ta ɗauke shi akai ta soma tafiya sauri sauri tabar lungun ta fita titi ba kowa sai kiran sallar farko da wasu mallatai ke yi, a haka tabar nan unguwar ta faɗa wani layi shima sai da taga ƙarshensa kafin ta isa titi, nan ta hango junction ɗin 'yan napep gasu nan burjuk sun parker, da sauri ta isa gurin ta samu wani ba kowa a ciki ta shige ta yi pilow da kayanta ta soma mayar da numfashin wahala. Wajen ƙarfe biyar da kwata tana nan a cikin Napep ɗin dan sai da ta huta sosai har an shiga masallaci salla, a lokacin ne masu abin hawa suka fara gilmawa a hanyar, hakan yasa ta fito daga napep ɗin data ɓuya ta isa titi, ba jimawa ta samu napep ta tare ta sanar dashi Na'ibawa zai kaita can kan hanyar da zata samu motar Kaduna dan ba zata tasha ba sauri take yi, yace kuɗinta dubu uku ba musu ta shiga suka wuce. Sai wajen ƙarfe shida suka isa saboda nisan gurin gari yayi haske mutane sun fara hada hada, ta sauka ta biyashi ya wuce ita kuma ta cigaba fa tsayuwa tana duban hanya, duk motar data gani kamar ta haya ce saita saka mata hannu har kusan shida da rabi bata samu mota ba sai ta fara tunanin ko ta dawo baya ta tsaya a tashar dake wajen na'ibawan ta samu mota, tana wannan tunanin sai ga wata mota jeep ta wuceta can kuma aka yi ribas aka dawo aka tsaya, ƙirjinta ne ya shiga bugawa dan sosai ta razana, a tunaninta ko malam yasa anbi bayanta, shiyasa yltaƙi yarda taje tasha dan kar ma su binciketa a can su ganta, da yake motar tinted ce ita bata ganin na ciki sai da aka sauke gilas kafin ta sauke a jiyar zuciya ganin bata san mamallakin motar ba.
'Yan mata ina zaki ne da wannan farar safiya?
Kaduna zani mota nake nima, in hanyar kayi dan Allah ka rage mini ko a zaria ne ka sauke ni.
Ok ya ce sai ya sauko ya buÉ—e mata boot ta saka kayanta kana ya koma ya shiga itama ta shiga gefensa ya tada mota suka wuce, saurayin ya kuma cewa.
Amma bakay tsoron faɗawa motar mugayen mutane da kika zo hanya ki hau mota, ana yawan faɗa a riƙa daurewa a shiga tasha saboda halin rayuwa.
Wlh nima dole ce ta saka amma ban taɓa hawa motar hanya ba sauri nake yi.
Duk saurinki lafiya ai tafi komai, in ma kuɗin mota ce ba kida shi wadatacce saiki haƙura har ki samu.
Wlh ina da ma kuÉ—i ina da dalilin daya saka banje tasha ba, kuma In Sha Allah daga yau bazan sake wannan gangancin ba.
Allah yasa. Ni sunana Mujaheed ina zaune a Kaduna da kowa nawa, bikin wani abokina nazo jiya aka É—aura sai kuma aka yi mini kiran gaggawa a gida shiyasa na fito da sassafe zan koma, kinga yanzu na samu abokiyar hira dama da niyyar haka na fito akan na rage wa wani hanya dan kar nayi tafiya ni kaÉ—ai.
Allah sarki naji daɗin haɗuwa da kai domin nima ka taimakeni a lokacin da nake buƙatar hakan, ni sunana Najwa kuma nima asalin 'yar kaduna ce iyayena da kowa na can yanzu ma gidan ƙanwar babana na baro dalilin auren dole da suke son yi mini.
Mujaheed ya juyo ya kalle ta ya kuma mayar da fuskarsa kan hanya, yace cikin murmushi.
Kyakkyawa da ke ayi miki auren dole ai an wuce zamanin.
To dole suke son yi mini sun kawo min mutum akan mu fahimci juna nace bai yi mini ba, sun dage akan ban isa ba dole sai na yarda shiyasa na nuna musu iyakarsu na bar gidan tun asubar fari don na koma gidan iyayena wanda nasan ba zasu bari hakan ya faru ba.
Gaskiya suma sun zaƙe da yawa ina ake yiwa mace kamar ki dole kuma ba su suka haifeki ba, gwara da kika gudu tunda gashi Allah ya haɗamu wataƙila ke rabona ce.
Najwa ta kalleshi a takaice ta kawar da kai gefe tana ɗan murmushi ganin yana niman tusa kanshi gareta. Ba wani fari bane yana da hanci da idanu sannan kuma yana da ƙaramin jiki sai dai akwai shekaru a tare dashi daga gani, bafulatani ne amma na Hausawa tunda Hausarsa raɗau ne.
Kinyi shuru baki ce komai ba ko banyi miki bane?
Hmmm me zance bayan ban gama kashe wata wutar ba kai kuma kana ƙoƙarin kafa gomnatinka.
Hmmmm Ni dai ina sonki saka ni a cikin list ɗin samarinki dan nasan kina su da yawa, saboda samari irinmu suna ƙaunar mace kyakkyawa haka kuma...
Bai ƙarasa maganar ba kira ya shigo wayarsa ya duba yaga ogansa ke kira sai ya mayar yana jan tsaki.
Duk kun dameni da kira sai kace dole ne sai kunyi tafiyar dani, in na ga dama Allah ko na zo gida bazan biku ba.
Lafiya kake faÉ—a haka.
Wai wani sabon company Abbanmu ya gina mini a Abuja to gobe ne suke son a yi lunching ɗinsa shine suka dameni akan dole sai na dawo yau mun tafi Abujan a yau, kuma na sanar dasu ni bana son company su barni na cigaba da harkan kasuwancinmu na Dubai amma sunƙi.
Nan fa Najwa taji wani farin ciki ya cika mata zuciya jin yadda yake koro mata bayani, nan take taji wannan shine daidai da ita ga dukkan alamu in ta aureshi zata yi gogayya dasu Sameeha, shi kuma Mujaheed ganin kamar zurata da yayi ya samu gurbi sai ya cigaba da cewa.
Kinga in kin amince sai muyi aurenmu mu wuce Dubai dan ba zan yarda na zauna a Abuja ba.
Ya ƙare maganar yana ƙara sanyin AC motar, Najwa ta saki murmushi ta gyara zama tana cewa.
Ka dai bari nayi tunani sannan in gama kashe wancen wutar tukuna.
Haba Najwa wlh da gaske nake yi karki É—auka wannan batun a matsayin wasa, amma ba damuwa zan baki lokaci.
Najwa bata ce komai ba jin wayarta tana vibration ta ciro daga Aljuhun wando ta duba taga number É—in Anty Saleema ce ta saki murmushi ta É—aga wayar ba tare da tace komai ba.
Najwa ina kika je? nazo ban ganki ba Siyama tace tun asuba data tashi sallah itama bata ganki ba.
Na tafi gidan iyayena da ba zasu yi mini auren dole ba, ina hanyar Kaduna kuma kar kiga baki ga kuÉ—inki ba dubu talatin da uku nice na É—auka nayi kuÉ—in mota.