← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 103

Sashe 101

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan ubanki idan banje can ɗin ba ƙasa kike so mu fara ci, ina ce nan na roƙeki Allah ki haƙura da auren nan na fita takaba sai kiyi saboda abincin da kike sayarwa shike riƙe mu amma kika ce atafau ke sai kinyi, dan haka tunda ke kin kasa taimakona naje inda suke da imani da taimako domin Allah ba dan halin mutum ba, kuma sannan Sameeha ɗan siyasa take aure ko ba komai munci rabonmu na gomnati, kuma bamu gama ci bama dan wlh naga gurin zuwa tunda kowa ya juya mini baya babu mai tausayina a dangi.

Amma mama ni banji daɗi ba da kika je gurin maƙiyanmu niman taimako, ai dariya sun riga da sunyi mana, dan Allah karki ƙara zuwa.

Ni ba maƙiyana bane in ma su ɗin ne na mayar dasu masoya dan babu wanda zai iya maka irin wannan ɗawainiyar ka ƙi shi, dan haka wlh sun fi mini Aminu da nake ciki guda da shi yayi mini cin mutunci ya wulaƙantani a bainan nasi, shine mai ƙumbar susan cikinmu amma yanzu kuɗinsa ba mai ci, dan haka ta ƙarfi dole su Sameeha su zama masoyana, domin in ci rabona a jikinsu wanda Allah ya tsaga zan samu.

Hmmmm ke dai mama abin duniya nan da nan yake sauya mini tunani, amma wlh Abin da kunya ba kaÉ—an ba, ni ai bazan iya wannan sauke kan ba a gunsu duk kuwa da matsatsin da zan shiga.

Ke kika ni kuma nice Hauwa akan kuÉ—i zan iya sauke kaina na same su. Kuma maganar ki ta ishe ni zoki kama hanya ki bar mini gida.

Mamaa kenan, ni da nake shirin dawowa gidan gabaɗaya ma, dan wlh ba zan iya da auren Isyaku ba, ashe duk facakan kuɗin da yake mini ƙarya ne, bama wannan ke damuna ba gidan nan sai kace gidan bariki kullun faɗa kamar gidan 'yan dambe, hayaniyarsu sai ta haifar mini da hawan jini wlh bazan iya ba.

Aiko baki isa ba Adama kinyi kaɗan ki kaso aurenki ki zo mini nan, yadda baki ji tausayina ba akan karki yi auren nan nima bazan raga miki akan ki dawo min gida ba, tunda kika zaɓi Isyaku a kaina na riga na sallamaki, dan haka ki sake tunani ba dai gidan nan ba.

Mamaa ya kike so inyi? kin san banda inda yafi nan, ni dai na zo ne dama na faÉ—a miki dan kar kiga kwatsam na dawo.

Adama tashi ki bar gidan nan tun kan inci uwarki da ubanki, kuma wlh yanzu zan kira Alhasan yazo na faÉ—a masa, kin san halinsu dai ki kuskura ki kaso aurenki wlh sai kin gwamace baki fito ba.

Allah sai dai ayi mini duk abinda za a min, amma banga gidan zama ba nan ne zan dawo.

Adama ta faɗa cikin ƙunƙuni ta gyara zaman mayafinta.

Ni na tafi babban gida kafin ku É—aura sanwa na dawo naci.

Da ashar Hauwa ta bita Adama ta fice tana 'yar dariya dan tasan halin Hauwa dama dole su kwashi 'yan kallo, amma a hankali zata shawo kanta sai dai in bata nuna mata kuɗi ba. Hauwa kuwa miƙewa tayi tana gyara zani.

Zaki dawo ki sameni 'yar banza, ka haifi ɗa ya riƙa juyaka, to baki isa ba kuwa, yara ba tausayi ba jin ƙan iyaye kamar waɗanda aka tsine mawa.

Ta ƙare maganar tana ƙofa ta shige ɗaki.

Da dare.

Umma tasa Zaidu ya riƙa Aminu suka yi magana har ta kawo masa maganar Hauwa tana cewa.

Ashe mijinta ya rasu baka sanar damu ba Aminu? yanzu haka Allah yace a kula da zumunci, ya kamata ka zama mai yafiya kaima sai Allah ya jiƙanka, bai dace in abu ya faru ba a riƙe shi a rai dole ana mance baya a fuskanci gaba domin gaba tafi baya yawa, kuma hannunka baya riɓewa ka yanke ka yar, naka naka ne duk lalacewarsa, domin jini ba wasa bane dan yafi ruwa kauri, ka daure ka kirata a waya kayi mata ta'aziyar mijinta dan ɗazun nan nasa Sameeha ta kiratq tayi mata gaisuwa dan ta tabbatar mini da zata kira, dan haka komai ya wuce domin nan gaba baka san inda rayuwa zai kai ka ba.

In Sha Allah umma zan gyara kuma zan kirata na yi mata gaisuwa.

Yauwa, kuma ɗan taimakon daka saba yi ka yi mata dan tana cikin buƙata sosai.

To In s'Sha Allah umma.

Yauwa Allah yayi albarka.

Ya amsa da amin kana suka yi sallama, Zaidu ya amsa suka cigaba da magana daga bisani suka aje wayar Zaidu yana duban umma da cewa.

Umma da alama Aminu da zai samu lafiya dan yanzu haka yabar London yana ƙasar Germany an haɗashi da wani sabon likita, kuma yace Alhamdulillahi ya fara jin sauyi a jikinsa. Shine yace in faɗa miki mu saka shi a addu'a.

Kai Alhamdulillahi Masha Allah, Allah ya tabbatar da lafiyarsa, naji daÉ—in wannan labari.

Wlh nima Umma naji masa daÉ—i sosai, ace mutum har mutum ba lafiya irin wannan ai ba rayuwa, dan matacce ne shi a raye.

Hmmm ga dai shi nan rabo ya rabasu da Sameeha, amma banda haka ko shekara gashi ba ai da rabuwarsu ba amma kaga lafiyarsa tana niman samuwa.

Ƙaddara ce mai zafi ya rabasu umma nima abinda nake faɗa kenan kullun in na tuna gwagwar mayar da aka sha, gadai Sameeha da Ibrahim tamkar ma shine ta fara aure yadda suke mugun ƙaunar junansu, abinda wasu basa ganewa kenan sai suga in aurensu ya mutum kamar shine ƙarshen rayuwarsu, kuma wata daga nan ne rayuwar ke buɗe mata sabuwa, sai tayi rayuwar farin ciki a gidan mijinta na biyu wanda bata samu kamarsa ba a gidan mijin ta farko ba, kamar dai yadda Sameeharmu ta samu.

Wlh fa rayuwar kenan duk mai haƙuri shike fa riba, Allah kuma ya rabamu da mummunar ƙaddara ya bamu ikon cin jarabawar rayuwa.

Zaidu ya amsa da amin sai suka cigaba da tattauna maganar bikinsa wanda ake ƙoƙarin tsaida rana.
[5/30, 7:13 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

60.

Aminu tunda ya gama waya da umma ya zauna ya ƙara zurfafa tunaninsa nan ya tabbatar da bai kyauta ba tunda duk abinda Hauwa tayi masa mutuwa ta wuce wasa, kuma koda su yaya Alhasan suka sanar masa a cikinsu baba wanda yace masa ya yiwa Hauwa gaisuwa, saboda suma sun san ta yi masa laifi shiyasa basu takurashi ba sun san komin daɗewa zai sauko. Da tunanin abin ya yi barci wanda daya farka lokacin mu nan garinmu ya waye shi kuma can lokacin ake yamma dan haka ya kira Hauwa, koda taga kiran kamar a mafarki ta ɗauka data ga da gaske ne sai ta ɗaga kiran da sallama, sai da Aminu yayi jim kafin ya amsa sallamar suka gaisa kana yayi mata gaisuwa mijinta, ta amsa tana tambayarsa aiki yace Alhamdulillahi kana suka yi sallama ya kace wayar, nan take ya tura mata dubu hamsin Hauwa saboda murna har da dan shewa tana cewa.

Ikon Allah wato dai Umma ta yi masa magana kenan, sun dai rabamu da shi sun janyeshi, duk da sun rabu da Sameeha amma dai ba zasu bar shi ba, Allah ya wadaran naka ya lalace.

Ta faɗa tana taɓe baki, sai ta yi ƙoƙarin kiransa tayi masa godiya amma bai shiga ba saboda ya saka number ɗinta a in da ko ta kira ba zai shiga ba sai shine yake da damar kira. Ta dangwarar da wayar ta soma tunanin wani hanya zata bi domin fa ba zata fasa abinda nayi niyya ba, tunda ga kuɗi sun samu dole ne ta zagara gurin malam ta bashi yayi mata aiki akan Aminu ya lalace dukiyarsa ma ta ƙare ya dawo baida komai, ta tabbatar in ya talauce to baida wani izza ko ƙarfin sake yiwa wani ɗan Adam rashin mutunci bama ita ba, dan haka miƙewa tayi ta saka hijab ta ɗauki kuɗinta dubu sha biyar da ATM ɗinta dan ta tsaya a hanya ta cire kuɗin ta kaiwa malam dubu hamain ɗin dan da kuɗinsa ma zata yi masa maganin, inya so kudin da umma ta bata zata biya kasuwar gari ta saro kayan moya ta fara sayarwa a ƙofar gida, haka ta fice ta samu napep ta hau ya wuce da ita unguwar kanawa dan fara isa gurin malam, tama mance takaba take yi saboda mugun abu ya tsaya a ranta, mai napep ya zo daidai Junction ɗin NDA zai hau kan babban hanya bai kula da wata motar Bus ba sai ya faɗa hanya motar kuwa ta angajesu suka daɗi, wanda wani ƙarfe ya danne ƙafar Hauwa, ihu ta saki a gigice nan take kuma ta suma, Hauwa bata san a inda kanta yake ba sai farkawa tayi ta ganta a gadon asibitin yara dake nan kusa da NDA, koda ta farka taga ƙafarta ta dama suntum sai wani uban zafi da yake ratsata har kwakwalwa, hawaye wani yana bin wani wata nurse ta zo tana cewa.

Sannu ko Allah ya ƙara sauƙi, yanzu zaki bada number a kira 'yan uwanki domin su zo su ɗauke ki saboda kin samu karaya wata ƙila ɗaurin gida za a yi miki.

Hauwa ta gyaÉ—a kai tana cewa a hankali.

Fos É—ina tana ina? wayata tana ciki.

Gaskiya koda aka kawo ki babu fos da aka bamu, domin mai napep mun sallameshi da yake ƙujewa kawai yayi, mai motar daya bigeku kuma ya bada kuɗi an duba ku ko kafin mu an kara ya sulale ya gudu.

Na shiga uku na lalace wlh wayata da kuÉ—i dubu sha biyar suna cikin jakar ga ATM É—ina.

Allah ya kyauta na gaba amma mutane yanzu ba gaskiya, yanzu dai ki tuna ko kin haddace number da za a kira wani naki.
Chapter 101 · 0% Book details