Sashe 20
Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sameeha ta saka dariya shima yasa dariya sai ta zame jikinta ta wuce bedroom ɗinsa dan ta haɗa masa ruwan wanka, cike da tsantsar tausayinta ya bita da kallo har yana jin hawaye suna cika masa ido, yasan Sameeha macece mai matuƙar kirki, hakuri, kawaici da juriya shiyasa ko kaɗan baya son matsawa nesa da ita yana son su kasance a tare har abada mutuwa ce kaɗai yake fatan ya rabasu. Sai ya koma ya zauna ya ɗauki wayarsa ya kira Alhasan ya sanar dashi ya fasa tafiya da Sameeha zasu cigaba da zama dasu, Alhasan yaji daɗin haka domin ya tabbatar da Ƙaninsa ya sauko, haka ma daya kira Kamalu ya ji daɗi bayan sunyi sallama ya kira Hauwa ita jimantawa tayi, dan nunawa tayi da dai ya tafi dasu ko hankula zasu kwanta, yace tunda komai ya wuce zasu cigaba da zama anan kaduna yana son zumunci ya gyaru ya kuma ƙara karfi a tsakaninsu, Hauwa tace Allah yasa hakan shine Alkhairi, yace Amin kana suka yi sallama. Hauwa tunda ta wayi gari take cikin zullumi ta tunanin waye zai sanar da ita fasa tafiyar nasu, haka ta danne ta cigaba da hidimar gidanta sai dai abin yana cinta a zuciya, kuma bata so ta kira kowa dan kar asan da saka hannunta a fasa tafiyar saboda ko Laure ba zata faɗawa ba, zata bar abin a zuciyarta, kiran Aminu yana ɗaya daga cikin abinda ya faranta mata rai a wannan ranar tayi murna tayi shewa ta yi rawa tare da alƙawarin zata je har gidan malam ta yi masa godiya ta ƙara masa wani hasafi dan bukata ta biya, sai dai kuma yanzu ne ya dace ta tashi da yaƙi, dole ne zata nuna komai ya wuce ta fara ɗaura ɗamarar lalata zaman nasu, dan in har Sameeha bata bar gidan Aminu ba to fa ba tada kwanciyar hankali tunda ga malam yace Aminu ba zai taɓa ƙara aure ba sai in Sameeha ta bar gidan, haka ta dinga saƙa da warwara tare da hangen ina mafita.
Wajen ƙarfe sha biyu Aminu ya tafi Abuja tare da driver, sun rabu cikin kewa sosai, a lokacin ne Sameeha ta kira Umma ta faɗa mata itama bata so basu tafi tare ba, amma sai tayi musu addu'ar Allah yasa hakan shine alkhairi, umma tace sai ta fara tunanin sana'ar da zata yi dan hakan ne kaɗai zai rage mata damuwa tare da zama busy a hidimar gabanta, sannan ta kara ja mata kunne kar ta riƙa shiga harkan su Hauwa koda kuwa zaginta suka yi kar ta biye musu, tace.
Umma ai ni na kara daukar darasi akan su dan haka nayi hankali, kuma ina so na fara kiwon kifi dan ance akwai albarka a ciki kuma akwai lada sosai.
Masha Allah hakan kuwa yayi sai kiyi shawara da Aminu duk abinda ya yanke shikenan.
Sameeha tace to kana suka dan taɓa hira daga bisani suka yi sallama.
***
Najwa.
Tunda ta bar gidan Sameeha ta wuce gida rai a ɓace, ta zauna a gefen inna data yi shinfiɗar tabarma a tsakar gida tana zuge zogale ɗanye da baba ya siyo ɗazun a kasuwar sati.
Auta naga kin dawo da wuri.
Wlh kuwa ai lamarin nasu ne ba daÉ—i Inna, sam basa kaunar Anty Sameeha.
Ni da zata ji shawara da tabi mijinta ta huta da fitinarsu.
Haba inna mu kuma da muke zuwa cin arziki aja mana kenan, a'a wlh tayi zamanta tare da yin maganinsu dan ko ta bar garin ba zasu fasa binta da sharri ba.
Ke dai kin bani da kwadiya Najwa ashe da biyu kike ma zuwa gidan, to zanja miki layi da zuwa kuwa dan kin san dai Zaidu zaki aura ba zan bari ki gama zubar da mutuncinki ba wlh, dan na kula ke sam ba ki da hankali sai ana yi miki seti kamar tinkiya uwar tambele kike jin kanki.
Innaaa! nifa Allah bana jin na dace da auren Zaidu, dan haka zan cigaba da jira har Allah ya fito mimi da miji mai kuÉ—i, tunda masu hannu da shuni suna son farar mace kuma kinga nima ina da nawa kyan ga fari ga hanci.
Baki inna ta saki tana dubanta.
Allah inna ni matar manya ce ba ƙanana irin Yaya zaidu ba, ni sai yanzu ma nake ganin wautata dana amsa masa zan aureshi.
Aiko wlh baki isa ba, ba zaki sanya naji kunya ba, É—an yayana zaki ce baki so shifa ya saki nono na kama, haba Najwa ki sake tunani.
Aiko in kika matsa mini wlh sai na shiga duniya dan bazan taɓa aurensa ba, hmmm nifa nama fada masa kuma yace ya haƙura.
Innalillahi wa inna ilaihir raji'un wannan yarinya kin tona mana asiri, yanzu Zaidun kika cewa kin fasa, shikenan kin ɓata zumunci.
Ni ban ɓata zumunci ba inna, ai gwara da tun yanzu ne na faɗa ba sai da aka saka rana ba ko aka ɗaura. Wlh in kika takura mini sai dai ki nime ni ki rasa.
Cewar Najwa da ta miƙe tana zumɓuro baki ta shige ɗakinta tana ƙananun magana, inna baki sake ta bita da kallo cike da mamaki da kuma tsoron sauyawarta lokaci guda, dan ba haka halin Najwa yake ba ta rasa me ya sauyata haka, dole ne ta hanata zuwa gidan Sameeha dan zarginta yana bata ganin kayan alatun da take ne yasa ta soma sauyawa da tunanin auren mai kuɗi, damuwarta da wani ido zata kalli Umma Halima akan abinda Najwa tace ta faɗawa Zaidu ta fasa, girgiza kai tayi tana nimawa 'yarta tilo daya shiriya.
Da daddafe baba daya dawo, bayan naci abinci ya natsa sai Inna ta koro maza zancen Najwa akan tace ba zata auri Zaidu ba, baba yace ta kirata Inna ta miƙe ta fito ta shiga ɗakinta ta sameta tana amfani da waya wato charting.
Ki zo Babanku yana kira.
Au inna ƙarata kika kaiwa baba, to wlh duk abinda za kuyi mini sai dai kuyi amma bazan auri Zaidu ba.
Inna kasa magana tayi ta fice, Najwa ta miƙe ta fito ta shiga ɗakin baban ta zauna, bana ya dubeta da kyau.
Najwa me Zaidu yayi miki da kika fasa aurensa ko so kike muji kunya.
Baba dama fa ni ban yi masa alkawarin aure ba, kuma na faɗa masa ya shiga cikin manema ne in da rabonsa shikenan sai ayi dashi, kuma ni wlh bai kwanta mini ba tunda, kawai dai ina yi masa kawaicin ɗan uwa ne, kuma ina ganin ƙila a gaba in yana zuwa zance zan ji ina sonsa, to kuma har yanzu banji komai ba shiyasa na bashi hakuri kawai mu rabu lafiya dan kar gaba na zo na fito da wani yace na yaudareshi.
To shikenan ba zan miki dole ba, amma ina so nan da wani lokaci ki cewa wanda kike so ya turo dan bana son tara samarin nan, gwara ki fito da miji ayi auren kowa ya huta.
Yanzu malam abinda zaka ce mata kenan?
Cewar inna data yi kasake da kai, baba yayi 'yar murmushi.
To ya zamu yi Zulai, so kike muyi mata dole rai ya ɓaci, ai tunda ta riga ta sanar da Zaidu magana ta ƙare, kuma In Sha Allah ba abinda zai taɓa zumunci, dan nasan Halima tana da kirki da sanin yakamata.
Hakane, Allah yasa mu dace, Najwa hankinki ya kwanta ko.
Sosai ma Innataaa.
Ta faɗa tana dariya, Inna ta yi kamar zata kai mata hannu Najwa ta miƙe ta fice tana dariya, tare da jin farin cikin ta gama da matsala guda ɗaya, yanzu saura na gaba wato yadda zata auri Aminu.
****
BAYAN WATA BIYU.
A bubuwa da yawa sun faru ciki harda fara zuwan su Amrah makaranta, kuma zuwa lokacin Sameeha taga sauyi sosai daga dangin mijinta, yanzu basa nuna mata wata tsana ko kyara, tana zuwa gurinsu suma suna zuwa gidanta susha hirar zumunci, musamman yadda bikin Salma ƙanwarsu Aminu ya taso wanda suke saka ran nan da wata guda za ayi shi, hakan yasa duk wani tsare tsaren bikin da Sameeha suke yi dan har kiranta suke taje ayi shawara da ita, sosai hakan yake faranta ran Aminu dan yana da labarin komai saboda Sameeha tana bashi labari, shiyasa shima ya sakar mata bakin aljihunsa sosai dan duk abinda aka nima na maganar kuɗi nan take take badawa, idan kuma fita zasu yi ita ke ɗibarsu a motarta su tafi, haka suke binta kamar raƙumi da akala zuna zuba mata ido, a bayan idonta kuwa su tsine mata dan kuwa ba ƙaramin ƙara mata bakin jini yayi ba, a cewarsu duk son iyawa ne yasa take yi musu haka, ita kuma domin Allah take yi badan komai ba, Hauwa kuwa a ganinta ita ya dace Aminu ya riƙa bawa kuɗi tana aiwatar da komai tunda itace shirin komai ke hannunta.
_Zaku iya fara biyan kuɗinku domin muna gab da gama season 1 mu tsunduma a season 2 wanda sai kun biya kuɗinsa kafin zaku cigaba da samun cigaban wannan labarin ɗoɗar har zuwa ƙarshensa. Bononza na kwana biyar akan N300 idan kwanaki biyar ya ƙare In Sha Allah zai koma asalin kuɗinsa N400, dan Allah ku mara mini baya._
Pay N300 to 0106956864
Ramatu Muhammad Kabir
Access bank (Diamond). Ko a tura MTN card N300 a 09034940106, masu so ta pc su tura N600. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.
[2/14, 8:30 PM] Rahma Kabir: *ABIN DA CIWO*
Na
©Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 15.
Hauwa.
Tana zaune a falonta ta miƙe ƙafa tana duba kayan fitan biki data siyo a kasuwa, Adama ta ɗaga leshi tana cewa.
Wlh mamanmu zaki cizo da bikin nan dan ko matar kawu Aminu sai dai ku goga.
Ai shiyasa nayi ta shiri a hakali dan kinga daga kan Salma mun gama aurarwa sai na 'ya'ya.
Wai mama ya batun Sameeha ne naga komai ya daidaita kin saki makamanki.