Sashe 73
Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Wani irin kallo Nafeesa take yiwa Najwa cike da firgici dan babu wanda yasan wannan sirrin nata sai Binafa, dan bata taɓa gigin faɗawa Najwa ba saboda abin ya jima da faruwa tun kafin su san juna, shiyasa da ta rabu da saurayin, ce mata tayi an bashi mata a family ɗinsu ne sai ya aureta kafin yazo ya auri Nafeesa shine tace ba zata jirashi ba ta haƙura, a lokacin Najwa jinta kawai tayi dan musamman ta shirya taje gidansu Binafa akan maganar, saboda akwai ranar da ta kira Nafeesa tana cewa ta bar maganar zai sun haɗu, Najwa da ta je gun Binafa take bugun ruwan cikinta ita kuma ta fayyace mata komai har tana cewa, shiyasa bata yarda da soyayya ba take hulɗa da mata saboda maza ba su da amana ga shi ya bar Nafeesa bayan ya gama da ita. Najwa ta saki shu'umin murmushi tana cewa.
A tsakanin ni da ke wacece ba tada amana, ni na yarda dake kin san komai nawa amma ke kin kasa faɗa mini wannan, shiyasa na rabu dake tunda baki so na sani, ban taɓa zata sanin sirrinki zai mini amfani ba sai yau, dan haka ni dake shege ka fasa, zaki iya fita mini daga gida kuma ki cigaba da biyar mijina wlh saina baki mamaki.
Jikin Nafeesa a matuƙar sanyaye ta ja ƙafa ta fita zuwa babban falo ba tare da tayi magana ba, ta shiga shock sosai akan sanin sirrinta da Najwa tayi wanda ta jima da birnewa, amma Binafa ta cuceta data fallasa mata sirri, amma tunda tayi mata haka itama sai ta tona mata asirin lesbian ɗin da take yi kowa a dangi ya sani, sai dai kowa kwaɓarsa tayi ruwa amma ba zata taɓa bari a gane itace ta tonata ba dan karta faɗa sirrinta family su sani, haka ta tsaya a falon har Najwa ta shiga ɗakinta ta kira sauran kwayenta suka fito ta rakasu zuwa ƙofar falon, bayan sun fita Najwa ta tsaya tana kiran Nafeesa da ƙarfi wanda yasa ta juyo tana kallonta.
Ki cigaba da ririta wannan kwan karya fashe nima zan cigaba da ririta naki, amma ina jin kin fasa to nima zan fasa naki sai ya bure kowa da wari, idan kin shirya mu fahimci juna ina nan ina jiranki, amma in baki shirya ba to kowa tashi ta fishe shi.
Tana gama faɗar haka ta rufe ƙoma gwam da ƙarfi ta juyo tana sakin shu'umin murmushi, sai dai me ganin Aminu da tayi ya harɗe hannu ya tsaya a jikin ƙofar falonsa yana kallonta yayi matuƙar razanata ya kaɗa mata 'yan hanji, sai ta sunne kai jikinta har rawa yake, amma haka ta dake ita bata ƙarasa cikin falon ba kuma bata juya ba tana nan a tsaye kamar gunki. Aminu kuwa ganin haka sai ya saki hannunsa ya shiga tafa mata har ya ƙaraso falon ya zauna a cushing ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya yana kallonta cike da natsuwa a tare da shi, da ya ga ba tada niyyar ƙarasowa sai ya ce.
Hajiya Najwa Amaryar Aminu ki ƙaraso mana kin tsaya, ina ce gidan ba baƙonki bane domin yayarki Sameeha ta fara zama kafin ke kuma kin sha zuwa ma. Sannan naji daɗin sallamar ƙawayenki da kika yi domin zanfi samun damar sakewa dake sosai muci amarci. Tun ɗazu driver na ya sauke ni na shigo gidan akan zai je ya wanke mini mota gobe zamu je Zaria kan wani aiki, sai kuma na kasa fita ko sallar Isha'i a ɗaki nayi, na kwanta kenan naji shigowar motoci an kawoki, sai kuma ba jimawa sosai naji an shigo falona, banji hirarku ba amma kamar faɗa kuke yi ko? a takaice dai ban san ke ce Najwar da Hauwa ta zaɓar mini ba sai yanzu, ashe shiyasa ɗazu Zaidu yake yi mini wani kallo ban sani ba, sai yanzu na fahimta hmmmm.
Ya ƙare maganar yana sakin murmushin takaici, ya miƙe ya isa gareta ya kamo hanunta, har lokacin jikinta rawa yake yi sai ya soma janta zuwa ɗakinta ko a jikinsa, har ya danganata da gado kafin ya zaunar da ita ya tsuguna a gabanta yana duban fuskarta da ta sunne ƙasa bata so suyi ido huɗu, sosai yayi mata kwarjini dan bata yi zaton haka ba, babban farin cikinta da bai ji hirarsu da Nafeesa ba, Aminu ya miƙe ya isa gurin wuta ya kashe sai ya dawo ya soma ƙoƙarin cire mata kaya, Najwa tana noƙewa har sai da tace.
Ka bari muyi nafila mana kuma ni tsoro nake ji.
Allah ko yarinya, ina ce kir shiryawa hakan tunda kika amince da aurena, ni kam bazan iya jira ba gwara mu san juna tun kafin mu fara jin barci, a matse nake.
Ya ƙare maganar cikin sanyin murya, hakan sai ya kashe jikin Najwa tayi shuru, sosai ta samu kanta cikin tsananin farin ciki wanda gabaɗaya ta bayar da aikin malam yaci Aminu, dan bata yi tsammani zasu kwashe lafiya ba in ya ganta itace amaryarsa. Sai da ya rabata da kayan jikinta tsaf kafin ya kwantar da ita, shi kuma ya miƙe ya cire nasa kayan ko wando bai bari ba, Najwa kawai jira take yi ya hau gado su lula duniyar masoya, nan magunguna data sha na gyara suka motsa mata sha'awa, ji tayi ta ƙosa ya kusanceta. Aminu kuwa zuwa yayi ya kunna hasken ɗakin, Najwa tana ganinsa tsirara ta rufe idonta da tafin hannu tana cewa.
Dan Allah ka kashe wutar kunya na ke ji, wlh bazan iya ganinka a haka ba.
Aminu kuwa daure fuska yayi sosai babu alamar wasa a tare da shi domin yana so yayi maganin Najwa ta yadda nan gaba ba zata ƙara kuskuren kwatanta abinda ta aikata ba, sarai yaji hirarta da Nafeesa danne fushinsa yayi domin ya samu damar da zai ci ubanta da kyau, ya ɗauki rigarsa daya cire sai ya ciro wayar cable ɗinsa ya nufo gadon, ya samu ta runtse idonta ta rufe gabanta da hannunta biyu, Aminu ware cable ɗin nan yayi da kyau ya zabgawa Najwa a cinya, a wani irin gigicewa ta tashi ta zauna tana ware ido taga ta ina dukan ya zo, sai taga Aminu tsirara ga cable a hannunsa, ta shiga haɗa hannunta biyu tana cewa.
Dan Allah karka dukeni me nayi maka? ban cancanci haka daga gareka ina matsayin amaryarka da aka kawo.
Ina so ki buÉ—e idonki da kunenki da kyau.
To to zanyi duk abinda ka ce.
Najwa ta faÉ—a baki yana rawa, Aminu Ya nuna mata gabansa yace.
Kalli nan.
Ta kalla ta koma tana kallonsa, ita dai taga abu akwance kamar nama, ya cigaba da cewa.
Wannan abun shine yasa na rabu da Sameeha domin bana iya sauke hakkin aurenta, tun lokacin data haifi Amrah ni kuma nayi accident sanadin mutuwar Mahaifuyarmu, Sameeha tayi haƙuri da juriyar rashin kusantarta da bana yi na tsawon shekara shida, duk da ina ta niman magani amma ban dace ba, shiyasa na saketa taje tayi wani aure bawai dan sharrin lasbians da kika yi mata ba keda ƙawayenki. Ki sani har abada ina ƙaunar Sameeha ƙaddara ce ta rabamu kuma na yarda da ita dan tana da tarbiyya me kyau. Da farko na amince da aurenki ne domin na rama irin abinda Hauwa ta yiwa Sameeha da kuma muzguna mini da tayi, sai kuma na dawo nayi tunanin karɓanki a matsayin matata domin na yafe komai, sai dai kash! ashe ke ce Hauwa ta zaɓar mini donin ta cigaba da muzgunawa Sameeha, duk da na rabu da ita amma ba zaku barta ta huta ba. Hauwa tana haɗa nata tuggun kema kin haɗa naki duk domin ku kai Sameeha ƙasa saboda son zuciya hassada mugunta da kuma zalunci. Sai dai gashi Allah ya ɗaga darajar Sameeha ya kaita gidan aure na girma da daraja tare da ƙanwarta, amma duk da haka wannan bai isheku ishara ba ko? hassadarku ya zama taki a gareta har yana naso ga 'yar uwarta itama ta samu, wlh ke da Hauwa dama duk waɗanda kuke da saka hannu wajen muzguna mata tabbas zaku ga sakamako tun a duniya domin Allah baya yafe zalunci shiyasa ya haramta shi a tsakaninmu. Najwa kin yi asara kin ci amanar zumunci, Sameeha ta ɗaukeki tamkar ƙanwarta ciki ɗaya, ashe ke ba haka bane a zuciyarki, Allah ya wadaran halinki.
Ya faɗa cikin fushi ya cigaba da zabga mata cable ɗin, Najwa tana ihu tare da cewa ta tuba, ganin ba zai daina dukanta ba yasa ta duro daga gadon tayi hanyar ƙofar fita, Aminu ya cafko hannunta ya cigaba da dukanta, sai da yayi mata lilis ta kwanta a tiles ko motsin kirki bata yi dan duk ya fasa mata jiki hatta fuskarta sai da yayi mata shedar bulala, sai mayar da munfashi take tana kuka mara sauti dan hatta muryanta ta dishe saboda wahalar ihun data yi, Aminu ya koma ya mayar da kayansa ya juyo yana kallonta.
Gobe in ance ki ci amanar wani ba zaki yi marmari ba. Sannan ki tabbatar zuwa safiya kinyi wanka kin shirya kafin ƙarfe bakwai.