← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 103

Sashe 96

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka suka cigaba da tattauna maganar har suka isa gida, a daren Sameeha ta bawa Ikram labarin abinda ya faru na gidan Najwa, sosai Ikram tasha dariya tana cewa zata zo su je taga ɗaki dan wlh sai ta yiwa Najwa wulaƙanci, Sameeha tace ita ba ruwanta ba zata rakata ba haka suka sha hira. Washe gari ne Sameeha ta tashi da ciwon kai daga nan sai zazzaɓi da amai a takaice laulayin ciki ta soma, wannan yasa Umma bata samu komawa gidan inna ba balle susan meke faruwa, haka Sameeha tayi jinyar kwana biyu harta samu sauƙi sosai bayan sunyi zaryan asibiti. Ranar Laraba Ikram taje gida suka sha hira a nan ne take cewa washe gari tunda Sameeha ta samu sauki sai suje gidan Najwa, umma tace ba inda zasu je tunda itama Najwa bata je ɗakunansu ba bata son damuwa, suna cikin wannan maganar ne sai Najwa ta kira umma da wayar inna. Umma ta ɗauka da sallama sai dai muryan Najwa taji tana gaisheta ta amsa cike da mamaki tana cewa.

Amarya ce da kanta ba dai har kin fara fita ba. Ina innar take?

Umma ai ina gida tun ranar da aka kaini ashe inna bata faÉ—a miki ba.

Subhanallahi me ya faru? Aiko Zulai bata faÉ—a mini ba, da yake nima ban samu dawowa ba saboda Sameeha ba lafiya.

Allah ya ƙara sauƙi, dama ina so ki je gidan da kuka kaiki ki bawa mamansa haƙuri ta yarda na koma ɗakina, wlh abubuwa dai da yawa sun faru yanzu haka babu mai kulani a gidan nan kona gaishe su basa amsawa.

Ta ƙare maganar tana matsalar kwalla, salati kawai umma ke yi zata yi magana taji inna ta amshe wayar tana faɗar waye Najwa ta kira, nan ta dinga surfa masifa ta inda take shiga bata nan take fita ba, Umma dai kashe wayar tayi tana mamakin me ya faru kuma.

Umma menene ya faru?

Cewar Sameeha, Umma ta sauke ajiyar zuciya tana cewa.

Najwa ce wai take gida tun ranar da aka kaita ta dawo, na kasa gane kan lamarin yanzu haka innar ta amsa wayar bata bari mun gama magana ba sai faÉ—a take yi mata, wannan yarinyar kuma me ta kuma É—aukowa? sam bata jin magana.

Wlh umma alhakin anty Sameeha ke binta ai duk wanda yace tukanyar wani ba zata tausa ba to nashi ko zafi bazai yi ba. Dan ba tada kunya shine zaya kiraki kije kiyi mata me?

Cewar Ikram. Umma ta danƙara mata harara.

Wai ke abu baya wucewa ne a gunki ita wacce aka yiwa ta yafe komai ya wuce amma kita dawo da magana baya, Sameeha bari naje naji meke faruwa zama bai ganni ba idan su Khairy sun zo kwa gaidasu ƙila har su tafi ban dawo ba.

Ta kare maganar tana miƙewa, Sameeha tace sai ta dawo umma ta shiga ɗaki ta sauya kaya ta saka doguwar rigar atamta ta sa babban hijab ta fito tana kwalawa Zaidu kira, dan yana ɗakinsa yana barci, cikin yanayin barci ya fito tace yaje ya shirya zai kaita anguwa yanzu, ba musu ya koma ɗaki ya zura riga ya ɗauki hula da key mota ya fito suka wuce.
[5/24, 7:51 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

57.

Umma abakwa ta wuce Zaid har ƙofar gidan ya kaita yayi parking yana duban umma.

Wai ina ne muka zo umma?

Gidan sirikan Najwa ne bari na shiga na fito yanzu, ka jira ni.

To yace mata sai tafi ta shiga gidan da sallama, su mama suka amsa da suke zaune a tsakar gida bisa tabarma, umma da fara'a ta ƙarasa ciki suka yi mata masauki akan tabarman da mama ke kai nan suka gaisa fuska sake mama ce tace.

Kamar naso na wayi fuskarki kuwa.

Eh mune muka kawo muku amarya Najwa har muka danƙa amanarta hannunki yanzu ma dalilin zuwana kenan, bawai dan naji me ta aikata ba sai dan na bayar da haƙuri ku yafe mata kin san halin ɗan yau basa abu da lissafi ko tunani, iya gwargwado Najwa mun bata tarbiyya dan har haddar Al-qur'ani ta fara Allah bai nufa zata haɗa ba, taci arzikin mu iyayenta ki amince ta dawo ɗakinta zuwa yanzu na tabbatar ta gane kurenta.

Banƙi ta taki ba Hajiya, wlh lamarin ne ya bani tsoro tunda ta ambashi zata kashe Jaheedi, amma tunda kin zo ba zaki tafi haka ba dole na amince da buƙatarki dan haka na yarda ta dawo ɗakinta Allah ya kyauta na gaba.

Mun gode Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci, ina ganin anjima sai mijinta yaje ya É—auketa da kansa hakan ya nuna mutuntawa kuma iyayenta zasu ji daÉ—i.

Eh gaskiya ne hakan za a yi kuwa In Sha Allah zan turashi yaje ya É—auketa Allah ya haÉ—a kansu ya kauda shaiÉ—an.

Ameen ya rabbi nagode sosai da karamci, ni sunana Halima matar yayan maman Najwa ce ina zaune a rafin guda In Sha Allah a hankali zamu yi zumunci tunda 'ya'ya sun haÉ—a.

Aiko sun haÉ—amu kuma In Sha Allah za muyi shi, dan zumunci abu ne mai kyau.

Cewar mama cike da jin daɗin sauƙin kan umma, sosai tayi mata kwarjinin da ba zata iya amsar roƙonta ba, haka suka dan taɓa hira umma tace zata wuce, mama tace ta tsaya Safara'u ta kawo mata ruwa tasha, umma tace ta gode daga haka ta miƙe tana ƙara yi mata godiya, mama har ƙofar gida ta rakota, abinda ya ƙara burgeta ganin da mota aka kawota hakan yasa mama ta dakatar da umma tana cewa.

Hajiya da kin bani number ɗinki mu riƙa gaisuwar zumumci, sannan in yarinya ta yi ba dai-dai ba na samu hanyar da zan sanar miki domin arzikinki taci wlh.

Umma tayi murmushi tana ƙara bata haƙuri, ta buɗe ƙaramar fos ɗinta ta ciro waya touch da Zaidu ya siya mata tace mama ta saka number ɗinta.

Riƙe abarki wannan waya saiku manya ban san kanta ba, ga dai tawa ki saka naki number ɗin ki kira akwai 'yan canji a ciki.

Mama ta faɗa tana ɗauko wayar a cikin lalitarta dake manne a jikinta, ta miƙawa umma ta amsa ta kaiwa Zaidu ya saka number ɗinta sai ta dawo ta kira ta miƙawa mama wayar tana ƙara yi mata godiya, a haka suka rabu ta koma ta shiga mota suka wuce, Mama sai da ta ga wucewarsu kafin ta koma gida tana jinjina umma yadda take da sauƙin kai ta wuce cikin gida tana.

Aiko na samu ƙawa dan wlh zan je na dangwali arziki, da gani suna da kuɗi gashi ba tada wulaƙanci.

A haka ta ƙarasa ciki tana kwalawa Safara'u kira akan tazo ta yi mata saving number umma da Hajiya Halima. Umma sai da suka hau hanya Zaidu ke tambayar meya sa tazo gidan, umma a taƙaice ta bashi labari Zaidu yayi murmushi yana cewa.

Kina nufin a wannan gidan Najwa zata yi rayuwa, lallai ruwa ya daki ɗan zakara, dole tayi bori tace ba zata zauna ba, yanzu haka ƙarya yayi mata hali yazo ɗaya, Allah yasa ta zauna.

Amin, fatan alkhairi zamu yi mata kuma in tayi haƙuri komai zai wuce, dan Maman mijin tana da kirki ba tada damuwa.

Ta dai riga ta yiwa kanta, Abin da ciwo daga ɗari ta dawo sifili, dan kam ni data gujewa na fi ƙarfin abinda take kwaɗayi, nifa umma ina so ayi maganar aurenmu zuwa bayan sallah.

Ya ƙare maganar yana shafa kai, umma tayi murmushi tana cewa.

Maganar bikin Najwa ya É—auke mini hankali amma mun fara maganar da Sameeha, Sannan ma ita kanta Rukayya ta kirani kan batun, In Sha Allah da anyi azumi da wata nake so ayi komai a wuce gun.

Tp Allah ya tabbatar mana da alkhairi.

Ameen, sai ka fara cigita gidan da zaka zauna kafin maganar tayi kwari ya zama akwai muhalli a ƙasa.

Umma ai ni ina da gida dan Ibrahim mijin Sameeha shekaran jiya daya zo yayi mini maganar aure nake ce masa ina sa ran nan kusa nayi, shine yace gidana yana wuyansa karna damu da an sa key zai miƙa mini, amma kar na sanar da kowa tukuna, shiyasa ban faɗa miki ba.

Ikon Allah to Allah ya saka da alkhairi sai ka cigaba da haÉ—a akwati.

Wannan ma umma banda damuwa dan kuɗi zan baku ku ƙarasa haɗawa, kin san na samu wannan kwangilar na jakunan 'yan siyasa da zan haɗa Shamsu mijin Ikram ya samo mini, kuma ga dukkan alamu In Sha Allah umma bana zaki aikin Hajji dan da kuɗina zan biya miki.

Kabbara umma tayi tsabar farin ciki tana sanya masa albarka, Zaidu yana amsawa da amin kana ya cigaba da cewa.

Da gida nayi niyya in saya amma dana ji Ibrahim zai bani nasan kuma ba zai bani mara kyai ba, shiyasa kawai nace gwara na biya miki Hajji tunda kinga ga motar hawa ma ina da ita, sauran kuÉ—i zan faÉ—aÉ—a sana'ata kafin aiki ya fito, dan kinsan na bawa Ibrahim takarduna ina sa ran zan samu.

Alhamdulillah i rayuwarku tayi kyau Allah yasa kyawunta har a aljanna, Allah ya ƙara shirya mini ku ya albarkace ku.

Umma ta faÉ—a cike da jin hawayen farin ciki, Zaidu yayi murmushi.

Ameen umma, kuma Duk yadda muka zama ke ce sila domin ke ce kika jajirce a kanmu kika bamu tarbiyya da muka san kanmu a yanzu, baba ma yayi nashi ƙoƙarin, Allah dai ya saka muku da gidan Aljanna. Yanzu ina zamu nufa.?

Mu wuce gida kawai ba sai naje gidan Zulai ba na riga nayi abinda ya dace saji labari a can.

Umma ta faÉ—a, haka suka cigaba da hira gwanin ban sha'awa har zuwa gida.

****

Bayan sallar magrib.
Chapter 96 · 0% Book details