← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 103

Sashe 12

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaskiya anty a kashe yake dan last shigata ba komai akansa kuma bangon ma a kashe yake, sai dai in wani mugun ne ya shiga ya kunna dan ya tada gobara saboda ƙeta da hassada, Allah ki sallami koma tunda la'asar tayi in ba haka ba kar a zo a tayar miki da wani tashin hankali dan na kula dangin mijinki baƙin ciki suke yi da ganinki a wannan gidan.

Cewar Ikram ranta a ɓace, Najwa ta mele baki tana cewa.

ÆŠazun naga wata yarinya ta shiga sai dai bazan iya gane fuskarta ba kuma babbace, wlh yanzu haka ita suka aika ta kunna dan su tayar da gobara In Sha Allah ta Allah ba tasu ba, gwara ki sallame su kawai, tunda mu namu dangin kaÉ—an ne duk sun tafi.

Sameeha bata ce komai ba ta miƙe ta isa inda masu abinci suke ta saka su tattara kayansu su bar mata sauran abincin, kana ta juya ta mufi inda 'yan uwan umma suke tace musu ta gode da zumunci su gaida gida taron ya ƙare dama la'asar suka yi da Aminu a watse, suka yi mata fatan alkhairi dan sun fahimci bata cikin natsuwarta shiyasa basu ja ba suka yi mata uzuri tunda abu yana niman zama da tashin gobara, ta ƙirga dubu goma ta basu na kuɗin mota cikin kuɗin da Aminu yace ta sallami mutane, suka amsa suna ƙara yi mata godiya da nuna jinn daɗinsu da kuɗin, ta koma gurin masu abinci ta saka suka yanka mata wani part na rago suka saka a leda suka bata taje ta basu, da farin ciki suka bar gidan sai da suka tafi ta koma wajen su Hauwa dan tayi haka ne kar suga abinda zai wakana a tsakaninta dasu, saboda tasan ba zasu kwashe ta daɗi ba, Sameeha tace musu.

Dama ƙarfe huɗu Aminu yace a tashi a wannan taron shiyasa nazo na faɗa muku, ga dubu goma sha biyar daya bayar kuyi kuɗin mota in kun tashi tafiya, nagode da zumunci Allah ya saka da alkhairi sai mun sake haɗuwa, In Sha Allah zan zo yi muku ban gajiya.

Wlh baki isa mu tafi yanzu ba dan sai bayan sallar magrib zamu tafi, haba ai da sauran lokaci mu mun saba sha'ani sai dare muke tafiya, ki kira Aminu ki faÉ—a masa in kowa ya tafi to mu sai dare. Kuma nawa kika bawa 'yan uwanki suka tafi da zaki bamu dubu sha biyar na tabbatar ba haka Aminu yace ki bamu ba.

Cewar yaya Hauwa a cikin faÉ—a kamar tana jiranta, Laure ta saki shewa ta tafa hannu tana cewa.

Su Sameeha masu gida, ai ba sai kinyi mana kora da hali ba zamu tafi, ke Hauwa tunda bata buƙatar mu kai dare tashi mu tattara yanamu yanamu mu kama gabanmu.

Wlh yaya Laure ba inda zamu, haka kurum da sauran lokaci mu tafi z in ta sallami wasu to mu ne zamu sallami kanmu, nan fa gidan É—an uwanmu ne ko kwana muka ce za muyi banga abin damuwa ba.

Eh nasan da gidan ɗan uwanku ne yasa nake baku haƙuri tare da isar da umarninsa tunda kuna kallo gobara ta nima tashi a gidan, ni kuma bani da natsuwar da za a cigaba da wani hidima, abu ne da aka fara tun safe ina ganin dan an tafi yanzu ba matsala bace. Kuma da kike maganar kuɗin dana bawa 'yan uwana ina ruwanki idan nayi adalci wannan kai nayi wa, in kun raina kuɗin ne sai ki kira ɗan uwanki ki faɗa masa kuɗin daya bayar yayi kaɗan.

Ta juya zata wuce, Adama ɗiyar Hauwa ta jawo gyalen Sameeha da ƙarfi har yana sauka a kafaɗarta ta shiga nunata da yatsa.

Wlh baki isa ki faɗawa mamana magana a gabana ba ina kallonki, taya zaki wulaƙanta ta a bainan nasi saboda mun zo gidanki, to wlh ahir ɗinki in ba haka ba zan keta miki rigar mutunci kuma babu abinda kika isa kiyi, dama ance ɗan talaka bai iya samun guri ba, baki gaji arziki ba shiyasa kike niman yiwa mutane rashin mutunci to bari kiji...

Bata ƙarasa ba Sameeha ta wanka mata kyakkyawan mari, Adama ta kama kuncinta tana waro ido waje, nan fa duk matan dake gurin suka miƙe, waɗanda suke can nesa ma suka matso, su Ikram ma suka ƙaraso gurin inda Hauwa ta shiga surfa masifa Laure tana tayata, sai kumfar baki suke sauran mata suma suna tayasu, Ikram tazo ta shiga tana rama zagin da suke yiwa Sameeha, wanda ita tama kasa magana sai kallonsu take suna dungure mata kai, abinda yasa bata yi magana ba saboda tasan duk abinda zai fito daga bakinta ba mai daɗi ba ne, kuma hakan zai ƙara wutar faɗan har yakai ƙila su bigeta tunda sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, Ikram da ta shigar mata sai faɗan ya koma gunta suka shiga zaginta, sai Adama ta tsakumota suka fara dambe, wuri ya kaure da hayaniya wanda Najwa komawa gefe tayi ta shiga ɗaukar su video a wayarta, tana jin daɗin ɗaukar yadda zata ji daɗin nunawa Nafeesa da bata labarin abinda ya wakana, da yake gabaɗaya hankalinsu yana gurin faɗan babu wanda ya kula da Najwa tana ɗauka, da kyar Sameeha ta kwace Ikram a hannun Adama dan tafi ƙarfinta Ikram ba tada jiki siririya ce, Ikram da aka kwaceta da kyar ta shiga yi mata Allah ya isa tana zaginta tana cewa dangin mayu saboda ta ji mata ciwo a fuska da yaƙushi, Sameeha janta tayi sai da suka isa ƙofar shiga falo ta buɗe ƙofar ta turata ciki tana gargaɗinta akan karta sake ta fito, sai ta dawo ta tasa ƙeyar yaranta tace suje falo, a lokacin ne Najwa ta fito daga maɓoyarta na ɗaukar video da take yi, Sameeha ta ce ta wuce falo tace to, sai ta koma ta sallami masu abinci ta saka suka shigar mata da sauran tace gobe In sha Allah zata kawo musu kulolinsu, sai da suka shigar mata da komai kana ta wuce falon ta shiga ta kulle ta ciki ta barsu Hauwa a tsakar gidan sunata surfa zagi da masifa.
[2/6, 7:10 PM] Rahma Kabir: *ABIN DA CIWO*

Na
©Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 9.

Sameeha zama tayi a cushing ta shiga zubda hawaye saboda ɓacin rai da kuma damuwar da suka jefata ciki, abin da ciwo yadda suke niman ɗaura mata laifin da bata san tayi musu ba, tasan ko ranta zata basu ba zasu taɓa sonta ba muddun bata yi musu abin da suke so ba, wato ta riƙa binsu tana yi misu biyayya sauda ƙafa tare da bin duk wani umarninsu da suka sharɗanta mata, gabaɗayansu jugum jugum suka yi ko wanne da damuwar da yake damunsa, tunda har lokacin su Hauwa masifa suke yi da zage zage har da buga musu ƙofar falo suna cewa su buɗe musu su shigo su ga yadda ake koyar da biyayya, Sameeha ta goge kwalla ta ɗauki wayarta ta kira Aminu bugu biyu ya ɗaga yana cewa.

'Yan walima har an watse kenan? Ko da yake dama la'asar muka yi ki sallami kowa kema ki samu ki huta..

Sasshekar kukanta yasa shi gimtse maganarsa ya ƙara gyara zama cike da mamaki ya cigaba da cewa.

Sameeha meya faru naji kamar kuka kike yi, su Hauwa ne ko? Dan nasan halinsu basa ƙaunar a zauna lafiya.

Sameeha sai ta fashe masa da kuka ta shiga bashi labarim duk abinda ya faru cikin kukan bata rage masa komai ba, salati ya shiga jerawa sai ya kashe wayar da sauri ya duba number ɗin Yaya Alhasan ya kira shi, yana ɗauka ya shiga zayyano masa komai shima Alhasan salati yayi yace zai je gidan yanzu ya kwantar da hankalinsa In Sha Allah zai tsawatar musu, sai suka kashe wayar Aminu ya kuma kiran Sameeha ya shiga lallashinta yana bata haƙuri yana cewa.

Naga alama su Hauwa ba zasu barki ki zauna cikin kwanciyar hankali ba dan haka zan nima mana gida anan Abuja idan na dawo sai mu ɗiba kayanmu na sawa mu koma can in yazo ma riƙa zuwa hutu a nan gidanmu.

Yanzu saboda su sai muƙi zama cikin ahalinmu, bayan burina na kasance cikin dangi nima a dama dani kuma mu kara sanin juna da fahimtar juna a tsakaninmu, wlh dalilin su Hauwa ba zai sa na bar kaduna ba dan na dawo kenan ba wani garin da zan ƙara zama. Kawai dai kuyi wa abin tufka dan wlh ina musu kawaici duk ran da suka ƙureni za a yi ɓatacciya.

Shiyasa nace kafin akai ga haka dole kiyi hakuri kibar kaduna dan bazan iya da wannan rikicin ba, da aiki na zanji ko da tashin hankali da suke jawo mini, ki ƙara bawa Ikram hakuri In Sha Allah hakan bazai sake faruwa ba, kuma ki fara haɗa kayanku dan baza mu cigaba da zaman kaduna ba na gama maganata.

Yana kaiwa nan a maganarsa ya kashe wayar Sameeha ta bi wayar da kallo tana jin zuciyarta na zafi, Ikram tace.

Ai dama nasan ƙarshe dole ki bar garin nan ki bishi Abuja, dan haka shine kawai mafita.

Wlh Ikram ba inda zani basu isa su saka nabar kaduna ba dan nan nake son zama, idan har muka koma Abuja hakan ya nuna sun ci galaba akai na, so nake na zame musu ciwon ido mai wuyar warkewa kuma sai gani sai hange, dole na fito musu da asalin halina tunda rashin mutunci ba a gadonsa kowa ara yake ya yaɓa.

Wlh da gaskiyarki anty karki yarda ki koma Abuja, taya zasu raba mana zumunci muna jin daɗin kin dawo nan zamu riƙa zuwa muna cin kayan daɗi.

Cewar Najwa cikin zuga Sameeha dan sosai zuciyarta ta tsinke data ji hukuncin da Aminu ya yanke, idan har suka koma Abuja ta san ta shiga uku Aminu ya ƙara yi mata nisan da ba zata taɓa samunsa ba, karshe ta kamu na ciwon so da zai yi ajalinta, dan haka dole ne tayi iya ƙoƙarinta ganin basu bar kaduna ba, jin maganar Sameeha da tayi yasa taji kwarin guiwar zugata akan karta yarda su koma can, Ikram ta galla mata harara.
Chapter 12 · 0% Book details