Sashe 72
Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cewar Sameeha tana miƙewa, Zaidu ma ya miƙe ya wuce ɗakinsa cike da tunani, umma sam bata son ana maganar amma daya fita ya bincika gaskiya, sai dai yadda tace abar maganar shima ya barta, Ikram kam wayarta ta ɗauka ta shiga charting da mijinta tana faɗa masa abinda ya faru, Umma kuma ɗaki ta shiga ta kwanta doguwar kujera tana huta gajiyar data kwasa a gidan biki, sosai lamarin auren Aminu da Najwa ya dameta amma ta danne hakan ne dan kar yaran su shiga damuwa, saboda abin baiyi mata daɗi ba ko ba komai Najwa ta nuna ba tada mutunci da kara, yadda suka ɗauketa ita ba haka ta ɗauke su ba. Haka suka yini jugum jugum har yamma, a lokacin ne yayan babansu yazo gidan ya bawa Umma Haƙuri akan abinda ya faru, ta nuna ita ba damuwa Allah ya ƙaddara Najwa matar Aminu ne kuma In Sha Allah ba zata yarda zumunci ya lalace ba a kan haka zata yi magana da yaranta, sai yayi mata godiya ya kuma bawa Sameeha Haƙuri itama tace babu komai ya wuce, haka ya tsaya suka sha hira sai gabda magrib ya bar gidan.
Gidan Aminu.
[4/29, 7:33 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*
43.
Gidan Aminu.
An kai Najwa gidan Aminu wanda ta jima tana mafarkin kasancewa a cikinsa, sosai 'yan uwan mahaifinta suka yaba da gidan suna faɗin Allah ya kaita gaba ta toshe kunnenta da 'yan gulma ta yi zaman aure, dangin Inna kuwa ba um ba um um dan lamarin baiyi musu daɗi ba duk da ya rabu da Sameeha amma a abun da kunya. Ɗakin Sameeha nan ne ɗakin Najwa, sun samu gida an tsara shi Masha Allah komai yana a mazauninsa, hakan yasa aka ce ba wanda zai kwana saboda an gama danki, shiyasa basu jima ba suka fara haramar tafiya, Najwa tana zauna a gado Salima ƙanwar baba ta dafa kafaɗarta tana cewa.
Allah yasa gidan zamanki ne Najwa, sai kin toshe kunne musamman a gurin dangin mahaifiyarki, sam ni banga aibun wannan aure ba saboda sai da suka rabu kan ya aureki, ki bawa mara ɗa kunya ki kafa naki gamnatin ki zauna ki ci arziki, dan kaf danginmu a cikin 'ya'ya babu wacce ta samu irin wannan gidan, ki kama mijinki sau da ƙafa kiyi masa duk abinda yake so matsawar bai saɓa Shari'a ba, naji ance a Abuja yake aiki ƙila ma watarana ki koma can da zama. Mu zamu tafi sai zuwa gobe In Sha Allah mu dawo mu ƙara ganin gida ido na ganin ido.
To Anty Salima Allah ya kaimu.
Cewar Najwa, Salima ta amsa da amin kana ta wuce suka tafi tana cewa ƙawayen amarya da zarar angwaye sun zo suma su wuce karsu zauna. Bayan tafiyarsu ba jima Najwa ta kalli ƙawayenta tana cewa.
Aminu fa ba yanzu zai shigo da abokai ba, kafin dare ya yi muku zaku iya tafiya.
Yanzu ke kin yarda mu barki ke kaÉ—ai a wannan gidan ko tsoro ba kya ji.
Tsoron me zan ji? bayan gidana ne ai dole ma na saba dashi, kuma gidan ba baƙona bane.
Cewar Najwa data bawa ƙawarsu Zainab Amsa, aiko tana rufe baki suka miƙe akan zasu wuce tunda bata buƙatar zamansu alamar ransu ya sosu da haka, Nafeesa ce ta kalli Najwa cikin rashin jin daɗi tana cewa.
Ke kuwa Najwa meye haka? taya zaki ce su wuce dare kar ya musu, ai sun san da dare ne suka zauna suyi miki kara, ko baki son su samu kuɗin siyan baki ne? dan Allah ki bari su ƙaraso nasan duk daɗewa ba zasu kai ƙarfe goma ba.
Eh duk da haka tafiya zaku yi har da ke, saboda Aminu ba abokai gareshi ba kuma tuntuni ya sanar dani ba wani siyan baki dan bubu wanda zai rako shi.
Kina nufin har da ni zan bar miki gida Najwa, yaushe aka ɗaura da har zaki fara wulaƙanta mutane kuma ciki harda ni.
Yauwa gwara da kika ma kawo wannan maganar, dama ina da magana dake su jiraki mu fita muje muyi ta, dan bazan bari sai gobe ba.
Cewar Najwa tare da aje mayafinta tayi hanyar ƙofarta ta buɗe Nafeesa da jikinta yayi sanyi ta miƙe tabi bayanta, Najwa har ta tsaya a falo taga nan bai yi mata ba dan maganar tana buƙatar sirri, sai ta nufi asalin falon Aminu tayi sa'a kuwa a buɗe yake dan haka ta murɗa handle ta shiga dan tasan baya cikin gidan, ta tsaya daga tsakiyar falon tana cewa tare da kallon Nafeesa cikin ɗaure fuska.
Nafeesa me Number ɗin Aminu yake yi a wayarki? kinyi masa saving da Amina, na ɗauka a tsakaninmu akwai amana ashe ke a zuciyarki ba haka bane, kenan kin ƙulla wata alaƙa da shi a ɓoye ba tare da na sani ba, me hakan ke nufi?
Ban gane me kike nufi ba Najwa, ya zaki zo mini da maganar da hankali ba zai É—auka ba.
Nafeesa ta faɗa cike da ƙarfin hali amma a zuciyarta ta rikice da fargaban ya aka yi Najwa tayi saurin ganeta, Najwa ta yi wani guntun murmushi tana cewa cikin ɗaga murya dan tasan ba wanda zai ji tunda sauran ƙawayensu suna a ɗakinta.
Nafeesa wlh ki faɗa mini gaskiya ko nayi miki wulaƙanci da baki taɓa zato ba, kar kiga kinsan sirrina zan iya saka a ɓatar mini dake kamar yadda na shafe tarihin Sameeha a cikin gidan nan, kar nake kallonki domin ni kaɗai hatsabibiyar kaina ce, in banda cin amana taya zan ga number din Aminu a wayarki harda saka masa sunan mace, sannan ki riƙa charting da shi nida ko hira bama yi a online dan yace bai dame shi ba, ban san tsawon lokacin da kuka ɗauka kuna tare ba dan ya nuna kun jima, ko kinyi haka ne ki tona mini asiri ki aure shi ko kuma kiyi yadda zan rasashi gabaɗaya kamar yadda kika rasa naki saurayin.
Dana so yin haka da ba wannan maganar ake ba, domin kuwa zan aiwatar da komai ba tare da kin gane ko waye ya aikata miki haka, idan da naso rabaku ne to da ba zan bari ya aure ki ba, kuma akwai wani cin amana daya fi naki ne da kika raba mata da mijinta kika aureshi bayan kinyi mata sharrin lasbian, ai Najwa sai dai in sara miki akan cin amana dan ko kaɗan ban kama ƙafarki ba. Banso kika gane alaƙata da Aminu da wuri ba domin kuwa kamar yadda kika bi ta ƙarƙashin ƙasa na tuggu da makirci da sharri, to ni kuma ta sauƙaƙƙiyar hanya na so bi dan nima na samu ya aureni muyi zaman kishi tare, kinga tsakanin ni da ke babu wani ɓoye ɓoye.
Kutumar kaza kazanki ne ba ya aureki ba, ashe ke ɗin butulu ce Nafeesa? to Alhamdulillahi Allah ya tona miki asiri tun yanzu, kuma zan baki mamaki yadda baki zato ba, sannan har gaban abada Aminu haramiyarki, daga yau karna sake ganin ƙafarki a gidana dan gayyar ta watse daga yau bani ba ke, ko a hanya in kika nuna kin sanni sai na ci ubanki.
Hahaha Najwa! Najwa 'yan mata ko nace Amarya, wa zaki wa baraza bayan kinsan komai naki a tafin hannuna yake, idan naso tona miki asiri walli sai nabi gida gida na fasa kwai kowa warinsa ya dame shi, na tabbatar hattar iyayenki sai sun tsine miki, kin yi sake nasan gidansu Sameeha nasan gidan Hauwa nasan kuma gidanku, ina da makaman da zan lalata gobenki ta yadda sunanki in aka ji sai an tsine miki. Amma mu zuba ni da ke shege ka fasa.
Nafeesa ta faÉ—a tana wani shu'umin dariya ta kuya zata fita daga É—akin, sosai kuma maganganunta suka kaÉ—a hantar cikin Najwa ta saki guntun murmushi tana daka tar da ita.
Wlh in kika tona mini asiri zaman Kaduna sai ya gagareki dan matakin da zan É—auka ba zai miki daÉ—i ba, kuma ki sani gidan nan babu gurin zamanki, wlh Aminu ya haramta a gareki ki saka a zuciyarki.
Haka kika ce?
Eh haka na ce Nafeesa.
To ki zuba ido da kunne kiji labarin da zai fara yawo a social media, Najwa itace ta yi sanadin mutuwar auren Sameeha Cousin sister ɗinta tayi mata ƙazafin lesbian, mijinta ya saketa ita kuma Najwa ta samu ta shiga jikin Hauwa yayar Aminu dan tasa Aminu ya aure ta, kuma ta haɗa da bin malamai da bokaye, ke abinda ma ba kiyi ba zan ƙara dashi.
Ke kuma ki zuba kunne kiji yadda zan fallasa abinda ya raba ki da saurayinki, ko an gaya miki ke kaÉ—ai ce kika san sirrina, to Binafa ta sanar dani cewar saurayinki ya gama kwarfeki, da yaga ba kida mamora ya rabu dake dan har ciki yayi miki Binafa ce ta taimaka aka cire cikin kuka bin ne maganar, hakan ya faru tun kina zuwa Poly, bayan kin gama karatu yace zai karo nashi karatun a bashi lokaci, shine kika shigo islamiyarmu hadda dan ki nunawa duniya ke mutumiyar kirki ce.