Sashe 14
Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da daddare tana kwance a É—akinta tana chart da Nafeesa tare da bata labarin abubuwan daya wakana a gidan Sameeha ta voicing, bata rage mata komai ba dan har video data É—aukar mata ta tura mata, Nafeesa ta buÉ—e tana kallo, sai da ta gama ta tura mata voicing da cewa.
Shegiya ƙawata amma kwakwalwarki tana bala'in ja, lokaci guda kin yi abubuwa da yawa masu muhimmanci, to ina mai tabbatar miki da in kika ɗaure a haka zaki cimma nasara wlh, kuma kinga video nan da kika turo mini bani kaɗai zan gani ba sai duk duniya sun gani, dan yaɗa shi za muyi a social media mu rubuta cewa matar ɗan uwansu ce tayi musu wulaƙanci dan sun zo gidanta saboda su talaka ne, bata ƙaunar kowa ya raɓeta tare da Allah ya wadaren masu hali irin nata.
Najwa data gama saurare ta saki wani shewa tana dariyar mugunta na jin daɗi, sam wannan tunanin bai zo mata ba ga shi Nafeesa ta ƙara hasko mata matsalar da zata ƙara saka Sameeha a ciki sai tace.
Wlh nayi matuƙar murna da kika tunatar dani wannan labari dan haka na bar miki wuka da nama ki bayar a yaɗa yadda ko bincike ya zo ba za a gane waye ya ɗauka ba, kuma ina kyautata zaton wannan videon zai ƙara wutar ƙiyayya a tsakaninta da su Hauwa, zata ƙara tsanarsu da tunanin sune suka yi mata haka da gangan dan zu tozarta ta a idon duniya.
Nafeesa ta turo mata sticker na rawa tana cewa.
Akwai wani É—an makarantarmu da muka yi poly tare, yasan kan media sosai shi zan turawa ya yaÉ—a.
Najwa ta yi mata godiya sai suka cigaba da hira inda Najwa ke bata labarin yadda suka yi da Zaidu É—azun, Nafeesa tace gwara ta yi masa haka ta fara zame masa dan ya cire rai da tunanin samun aurenta.
[2/7, 7:30 PM] Rahma Kabir: *ABIN DA CIWO*
Na
©Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 10.
Hauwa.
Da tsananin ɓacin rai suka bar gidan suka kama tafiya a ƙafa ba mai cewa wani a tsakanin Hauwa, Laure da Sa'a da yake su uku suka jera, sauran sunyi gaba da yara wasu kuma sun tari abin hawa sun wuce, suna cikin tafiya har su Alhasan suka wuce su a motar Kamalu, Sa'a ce tayi ƙofa tana cewa.
Allah ya wadaran naka ya lalace, ina takaicin yadda su Kamali suke bin Aminu sai kace shine babbansu, komai ya tsara musu shi suke yi basa iya yin ra'ayinsu, ko da yake mai kuÉ—i sarki ne dole ya amshe girman su sun zama fadawa, basa ganin laifinsa da matarsa komai suka yi daidai ne.
To Aminu ya gama kashe musu zuciya basa iya ƙoƙarin nima ya gama ɗaure musu gindi komai yana yi musu, ina ce motocin da suke hawa duk shi ya siya musu, idin hidima ya taso musu shi suke faɗawa yayi musu kunga kuwa har abada Sameeha ba zata taɓa yin laifi ba a gunsu, dan haka sai dai mu zuba ido muga abinda zai turewa busu naɗi, dan kuwa wulaƙanci yanzu muka fara gani a gunta tunda ta samu masu tsaya mata kuma bamu isa mu ja dasu ba dole ta taka mu son ranta.
Cewar Laure rai a ɓace, Hauwa kuma ta kasa magana sai taunar leɓenta na ƙasa take yi saboda tsabar baƙin ciki da ke nuƙurƙusanta.
Hauwa baki ce komai ba kinyi shuru.
Cewar Sa'a, Hauwa ta taɓe baki tana cewa.
To ni me zan ce bayan sun gama yanke hukunci, kamar yadda suka faÉ—a nima bazan sake zuwa gidan Aminu ba in dai Sameeha tana ciki, tasha zamanta nima na zauna a inda Allah ya aje ni, ta dai gama lalata mana zumunci.
Ta ƙare maganar tana jan tsaki, wayar Sa'a data yi ƙara yasa basu yi magana ba, tana ɗaukota a jaka taga Kamalu ne tace cikin damuwa.
Kunga Kamalu ne yake kira har sun kai gida, bari na tari napep na ƙarasa dan bana son rikicinsa, in ba haka ba yau sai ya hana mini barcin kwanciyar hankali wlh.
To mu dai sai mun zo, dan babansu ma baya nan daga ni sai yara shiyasa na ce sai dare zan tafi, to uwar iya ta koremu sai kace wasu tumaki.
Cewar Hauwa, nan Sa'a ta tari napep tayi gaba sai da ta wuce kafin Laure tace.
Wani mataki zamu ɗauka dan Wlh ni bashi ta ci, yadda ta saka su Alhasan suka dizgamu gaban sirikanmu da 'ya'ya. Banyi maganar bane saboda kin san Sa'ade uwar surutu ce ina buƙatar sirri.
Nima ganin ta yasa banyi magana mai zafi ba, amma wlh Sameeha sai ta bar gidan nan kamar yadda ta saka aka koremu itama sai Aminu yayi mata korar kare, ai ta jawa kanta dan wlh watan barin ta gidan ya kama, sai ta yi dana sanin abinda tayi mana, dan sam ba matar aure bace ita tunda tana niman haÉ—a mu da 'yan uwanmu, In Sha Allah ni da kaina saina sama masa mata ta mutunci wacce zata yi mana biyayya taso mu tamkar nata 'yan uwan.
To Hauwa kina ganin ta wace hanya zamu ɓullo wa lamarin dan lokaci yayi da zamu nunawa Sameeha ita ƙaramar 'yar iska ce, kuma mu nuna mata muma muna da rana.
Ki bar komai a hannuna, aure zan fara niman masa mu gani in zai yarda, in yaƙi kuma sai mu bi masa ta bayan gida na shiga malamai ayi musu farraƙu shi da Sameeha, dan sai ta bar gidan nan wallahi da ni take zancen.
Cewar Hauwa tana tafa hannunta cike da masifa, haka suka cigaba da ƙulle ƙullensu suna ta kwashewa Sameeha albarka wanda kuma kansu suke zagi kuma fata nagari aka ce lamiri. Sai da Laure ta shiga gidan Hauwa ta ɗibar mata naman kaza kafin ta wuce gida tana cewa zata ɓoye abinta taci a hankali. Adama data shigo bedroom ɗin mamanta tana cewa.
Allah mama ki bani dama na koma naci uwar miki Sameeha, dan ji nake in ba dukan kawo wuƙa nayi mata ba ba zan huce takaicina ba.
Sha kuruminki akwai abinda zanyi mata wanda yafi duka ciwo, daga ni har ku ba mai sake zuwa gidan idan Aminu ya dawo mayi zumunci dashi a babban gida sai naje mu gaisa.
Ai mama baiyi dacen mata ba, ƙiri ƙiri take nuna bata son hurɗa damu, Allah yasa ya ƙara aure muga ta iskanci.
Adama ta faɗa tana zama a gefen gadon Hauwa tare da buɗe ledan naman kaza ta ɗauki cinya, tana ci tana cigaba da zagin Sameeha, Hauwa dai ranta a dagule yake dan sai mugun alwashi take ɗauka a zuciyarta dan in har bata ga Sameeha ta wulaƙanta ba to hankalinta ba zai kwanta ba.
...
Da safe suna karyawa wayar Hauwa ta hau ƙara, yaron Adama Sadiq yaje ya ɗauko mata a tv stand ya kawo, ta duba sai taga Najwa ce sai ta ɗauka da sauri suka gaisa kana Najwa ta ɗaura da cewa.
Yaya dama na kira ne nayi muku ban gajiya jiya da kuma jimamin abin da ya faru, Allah ya ƙara muku haƙuri dan wlh Abin da ciwo, ko ni korata tayi tace na tafi ta sallame ni bata son damuwa, haka na tafi komai bata bani ba, kuɗin napep ma sai da na isa gida na shiga na amso a hannu Inna kafin na sallame shi.
Allah ya kyauta, ai dama in bata yi haka ba to bata ci sunanta ba, gajiya tabi lafiya Najwa, 'yar uwarku dai ba tada mutunci tasa an wulaƙantamu a bainan nasi.
Ai wlh naso ace kunyi musu dukan ciya kun fasa musu jiki dan har Ikram ba mutunci ne da ita ba, jiya kun sha zagi da tsinuwa, cewa take taji daÉ—in hukuncin da yayyinku suka yanke, kuma duk wacce ta zo gidanta sai ta kira ta faÉ—a masa, Ikram tace ai kawai ta saka a kawo mata karnuka duk wacce ta zo tasa a sakar mata kare su korata, Sameeha tace ita bin Aminu ma zata yi subar garin dan ba zata iya da jaraba da kwaÉ—ayinku ba, dan ta lura talauci ke damunku, wai ko wacce ta kwaso yunwa kun zo kun saki ciki sai É—irkan abinci kuke yi kamar mayu.
Inalillahi wa inna ilaihir raji'un! mu suka yiwa wannan zagi, amma Allah ya ɗebe musu albarka, In Sha Allah yadda ta wulaƙanta mu itama sai ta wulaƙanta a duniya.
Cewar Hauwa cikin baƙin ciki kamar zara rushe da kuka dan sosai maganganun da Najwa ta faɗa mata sun daki zuciyarta, tsanar da takewa Sameeha ya ƙara ninkuwa, ji take da za a bata damar kashe mutum guda to Sameeha ce zata kashe dan duk duniya ba tada maƙiyiyar data wuce ta, nan ta baza kunne Najwa tana ta faɗa mata maganganu na ƙarya tana hawa ta zauna, daga Ƙarshe Najwa fashewa tayi da kukan ƙarya tana cewa.
Wlh yaya abin da ciwo sosai jiya da kyar nayi barci akan abinda ya faru, wlh ba dan Sameeha 'yar uwata bace da sai nayi hanyar da sai na auri mijinta naga iya ƙarshen wulaƙanci da iskanci.
Wani 'yar uwa? abin da babu haramci, ai wlh da ba ƙaramin baƙin ciki zata shiga ba ace 'yar uwarta ce ta aure mata miji, amma wlh da hakan zai faru dana fi kowa farin ciki, ke ni sai yanzu naji ɗan farin ciki da wannan maganar taki, saboda barinta gidan bashi ne mafita ba ayi mata kishiya da kuma wacce ta sani shine zai fi girgizata ta shiga tashin hankali, kinga mu farin ciki goma da ashirin, kuma nasan ke ba zaki yi irin halinta ba tunda tarbiyya ba ɗaya ba.
Yaya nifa ba zan iya ba dan wannan yadda bata so a raɓeta sai ta kashe mutum akan ayi mata kishiya, tsoroma take bani, dan sosai nasan ƙulle ƙullen asirin da take ƙullawa mijinta, shiyasa ta mallake shi. Au na shiga uku nayi suɓul da baka ashe da yaya nake maganar, dan Allah karki faɗawa kowa wannan maganar dan Ikram ke faɗa mini a matsayin sirri.