← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 103

Sashe 56

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hmmm dole ki naÉ—e tabarman kunya da hauka Sameeha, domin yanzu ne na tabbatar da wacece ke tunda daga fita idda sai aure, kamar kina jira na sake ki, kin bani mamaki ban zaci haka daga gareki ba, nagode wa Allah daya bayyana mini ke wacece kuma In Sha Allah ki zuba ido zan nima lafiya duk inda yake koda nan da birnin sin ne zanje domin nima na yi aure, dama dakon sonki ne yasa nake ganin zan iya komawa ga Allah a yadda nake, amma yanzu kin shayar dani gubar mamaki daya zaburar dani akan na nima lafiyata, kin nuna mini ke É—in 'yar Adam ce Sameeha wato butulu.

Me nayi maka dana zama butulu Aminu? kawai dan zan yi aure kake faɗa min baƙaƙen magana saboda son zuciya, kar ka manta ƙaddara ita ta haɗamu kuma itace ta rabamu.

Kaddara ko kuma cin amanata da kika yi Sameeha, ai da ban kamaki da yaran nan ba da yanzu muna zaman aurenmu.

Zaidu ne ya fizge wayar daga hannun Sameeha ya kara a kunnensa, da yake duk suna jin maganar Aminu saboda sunyi shuru kuma volume ɗinta ana ji sosai koda bata saka handsfree ba, Zaidu yace cikin ɓacin rai.

Dan Allah karka sake kiranta ka nima ɗaga mata hankali tana cikin farin ciki, tunda kai ka saketa kace baka yi da ita duk halaccin data yi maka ta zauna da kai tsawon shekara shida ba ka da lafiya amma ka saketa akan abinda ba kada tabbas, dan haka ta samu wanda yake sonta kuma yake ganin mutuncinta gidan mutunci ba irin 'yan uwanka ba marasa mutunci, yara kuma kar Allah yasa ka kawo su ka riƙe su In Sha Allah zata haifa mana wasu a sabon gidanta.

Bai jira ya yi magana ya kashe wayar yana huci, Umma ta riƙe haɓa.

Ashe shima baida mutunci ina yi masa kallon salihi, koda yake ai nono guba Hauwa ta sha ta sake masa, ina ganin abin nasu ya samo asali.

Nifa ina ganin kishi ne yasa shi fusata haka, ko uban waye yace ya sake ta oho.

Cewar Zaidu, Umma tace.

To kishi sai ya saka idonsa ya rufe ya rika faÉ—in magana sai kace wanda cutar É—an kanoma ya kama, haba abin ya yi yawa, ni nayi mamakin ma yadda ya samu labarin auren abinda akayi magana yau yau amma har magana ta isa gareshi shi da yake Abuja.

Ai kiwon mutum ake yi Umma, da alama ƙila ya saka masu yi masa bincike akanta ne suna faɗa masa halin da take ci, in ba haka ba taya daga magana yau har ya samu labari.

Cewar Ikram cikin faɗa, nan dai suka dinga juya maganar Sameeha dai ta kasa cewa komai sai maganganun Aminu ne suke yi mata yawo a zuciya, dan sosai lamarin ya taɓa ta ba yi zaton jin waɗannan kalamai a bakinsa ba, kira daya ƙara shigowa wayarta yasa ta duba taga number ce da tun ɗazu da take magana da Aminu ake kiranta, har ya katse bata ɗaga ba sai ma miƙewa tayi ta wuce ta ɗauki buta ta wuce bayi dan tayi fitsari, tana shiga ta saki kukun da take dannewa, sai dai bata bari tayi mai sauti ba dan kar su ji ta, gabaɗaya duk farin cikin da take ciki ya yaye sai baƙin cikin abinda Aminu ya yi mata yanzu daya maye gurbin zuciyarta, ko a mafarki bata taɓa tunanin zai yi mata haka ba, babban baƙin cikinta yadda ya gasgata ta aikata masha'a da 'yan matan nan, har gobe ba zata iya yafe musu ba dan duk sallah tana kai kukanta gurin Allah akan ya saka mata tare da jera musu Allah ya isa, babban farin cikinta yadda su Hauwa basu san dalilin mutuwar aurenta ba, da sun sani ta tabbatar ba zasu taɓa barinta ba dan sun riƙa zuwa kenan suna niman rikici da ita, haka tasha kukanta ta gama ta wanke fuska ta fito ta wuce ɗaki suf-suf bata bi ta kansu Ikram ba, su dai kallo suka bita dashi dan sun san in tana cikin damuwa to shuru take yi bata magana da kowa, sai ta kaɗaita kanta ita kaɗai tana sharɓan kuka, Ikram data bi bayanta da kallo har ta shige sai ta juyo tana cewa.

Umma kuka fa tayi a bayi, baku ga yanayinta ya sauya ba.

Na gani tunda nasan halinta, ku rabu da ita da kanta zata saki ranta, kuka da damuwa dole tayi domin duk inna tuna da wannan sharri da 'yan matan nan suka yi mata sai na tsine musu tare da addu'ar Allah ya tona musu asiri.

Ameen nima wlh ina yin addu'ar Allah ya hana musu kwanciyar hankali.

Cewar Zaidu, haka suka cigaba da hira wanda duk rabi akan zancen Sameeha ne.

Aminu kam wayar yabi da kallo lokacin da Zaidu ya kashe kiran, ya tsugun kan guiwarsa yana jin wani ɗaci a makoshinsa, jikonsa har wani kalkarwa yake tsabar damuwar daya samu kansa, dana sanin sakin Sameeha ya rufe shi sai yaji dama saki ɗaya yayi mata ko biyu yadda zai samu damar gyara aurensu ta dawo masa, tabbas yadda yake ji a zuciyarsa hakan yana nuna shine ya zalunci Sameeha, domin kuwa dama a tsakanin ma'aurata duk wanda yayi zalunci to tabbas yana gamuwa da dana sani a gaba kuma wanda aka zalunta yana riga yin aure, bai san hawaye yake yi ba sai da ya taɓa kuncinsa ya shafa kafin ya gane haka, shima yasan duk maganganun daya faɗa mata ɓacin rai ne dan har gobe zai shaidi kyawawan halayyarta, sai ya miƙe cikin sanyin jiki yana ambaton sunan Allah dan hakan ne kaɗai zaisa ya samu sassaucin halin da yake ciki.

*Barkanmu da Sallah fatan munyi sallah lafiya Allah ya maimaita mana yasa muna cikin yantattun bayi. Ameen.*
[4/17, 5:45 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

35.

Aminu bai taɓa zaton Abin da ciwo ka saki mata wani ya aura ba sai yanzu, bai kawo zai damu ba in yaji Sameeha zata yi aure ba, sai gashi abu yana niman zama masa ƙaya a maƙoshi, zazzaɓi mai zafi yaji ya kamashi kuma a haka ya kwana, wanda da kyar barci ya ɗauke shi. Washegari da wuri ya shirya ta tafi asibiti, dan ya ɗauki alwashin nimawa kansa lafiya ko nawa zai kashe, sannan ma dole ne ya amsa auren da Hauwa ta samo masa domin ya huce takaicin Sameeha, zai yi fatan ya samu lafiya kafin bikinsa duk da ba yi da tabbacin zai samu lafiyar, amma ya ɗaura niyya sai inda ƙarfinsa ya ƙare.

*

Ibrahim.

Tunda aka sanar dashi an gama komai na aurensu an saka rana sai yaji hankalinsa ya kwanta, dan sosai ya kamu da son Sameeha da ko magana basu taɓa yiba a tsakaninsu, hakan yasa shi kiran Khairy yace ta tura masa Number ɗin Sameeha, domin yana so su ɗan saba kafin bikinsu. Data turo masa Number ne sai ya soma kiranta a lokacin, sai yaji call waiting, ya kira sau biyu duk tana waya hakan sai ya bashi mamaki da tunanin da waye take magana da shi haka, duk da yana da tabbacin ba tada zawarawa amma jikinsa yana bashi kamar da wani take magana, nan take ya ji kishi ya ɗarsu a zuciyarsa wanda bai taɓa tsammani ba saboda shi mutum ne da ba ruwansa da wani kishi shiyasa matarsa Nabila take yin yadda taso, bata zama a gida kuma hakan ba ya wani dame shi bane, amma kam yadda yake jin Sameeha a zuciyarsa komai ma zai iya faruwa. Bayan ya bada wasu mintuna sai ya kuma kira, a wannan lokacin ne yaji bata yin waya sai dai bata ɗaga ba, hakan yasa ya miƙe da sauri ya shiga bedroom ɗinsa ya sauya kaya ya fito falo ya samu Nabila tana cin abinci.

Sai ina kuma? Naji kace zaka yi barci da wuri saboda da safe zaka wuce Abuja.

Taɗi zani wajen ƙanwarki.

Kallonsa tayi sheƙeƙe tana 'yar dariya.

Wasa kake yi, dan nasan ba kada wata mata sama da ni Nabila. Kama daina wannan zencen dan nasan ba mai yuwuwa bane.

Allah ko Hajiya Nabila, to ki zuba ido kiyi kallo domin wannan karan da gaske nake ba wasa a ciki, idan naje zan kira ki ki gaisa da ita domin ki tabbar. Kuma ki fara lissafin abubuwan da kike buƙata na faɗar kishiya, sai na baki kuɗin ki haɗowa kanki.

Baki sake Nabila ta bishi da kallo har ya fice daga falon ta kasa yin magana, da farko ta ɗauka wasan daya saba yi mata ne yayi, amma kuma yadda taga yana maganar fuskarsa washar ta soma gasgata haka, nan take taji abincin ya fice mata a rai ta tura plate ɗin ta soma kiran wayar wata ƙawarta Shema'u, tana ɗauka ta koro mata bayani tana ƙarawa da cewa.

Allah zuciyata ta karaya ina ga da gaske yake duk da shi ya tabbatar mini da baya sha'awar mata biyu.

Hmmm kin zauna ya gama jirgaki kin hau kin zauna, an faɗa miki namiji ba ɗan kunama bane, sai kin saki jiki kin daidaita zama ya gantsara miki cizo, kina tunanin yadda kike yawo ƙasa ƙasa ba kya zama hakan ba zai dame shi ba ko, to ko wannan dalilin zai sa ya ƙara aure kuma dama 'yan uwansa tuntuni suka so ya ƙara, kinga kuwa dole watarana zasu ci galaba akansa ya amince, idan zaki tashi tsaye gwara ki miƙe dan wlh in kika bari wata ta shigo zata amshe komai na uwargida tunda ke baki ɗauki auren a bakin komai ba sai niman kuɗi.

Idan akan niman kuɗina ne to wlh yaje yayi ta auren ai ba kaina zata zauna ba, kuma nasan dai har abada bata isa ta kamo ƙafata ba tunda ni ina da kuɗi, kuma ba daga gidan talauci ya aureni ba.
Chapter 56 · 0% Book details