← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 103

Sashe 68

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ibrahim ya miƙe yana murmushi ya wuce ɗakinsa tana biye dashi. Sai da ta kammala yi masa komai da ta saba kafin suka fito falon suka sabu Amrah har tayi barci, Ibrahim da kanshi ya ɗauketa ya kaita dakin Sameeha kana ya fito, Abi shima yace zai kwanta Sameeha ta rakashi ɗakinsa ta dawo, tana zama Ibrahim yana cewa.

Da babansu zai yi haƙuri daya bar mana yaran nan zasu riƙa ɗebe mana kewa dan ina son yara sosai.

Hmmm Aminu bazai barsu ba, yanzu ma dan yanada dalili shiyasa ya kawo su, wai aure zaiyi.

Aure kuma? Ya samu lafiya ne?

Yace yana dubanta dan Sameeha ta faÉ—a masa dalilin baida lafiya ne suka rabu. Tayi murmushi tana cewa.

Ya samu kenan tunda gashi zai yi aure.

Ko kuma zai yi na huce takaici ba tunda ya ganki da wani mijin, ke ki barmu mu maza fa, har yanzu yana jin haushin auren da kika yi duk da shi yayi sakin, to Allah ya basu zaman lafiya, ya zaki da yaran nan kema zaki Kaduna bikin Najwa.

Dasu zan tafi suje su ga su Umma, kaga sa sada zumunci da 'yan uwa.

Hakan yayi amma ki sanar da babansu kar yazo kuma yaji sunje Kaduna yayi faɗa yace bazai ƙara kawo su ba.

Wlh bazan faÉ—a masa ba in yaji ma yace bazai kawo su ba shi ya sani, yanzu ma bani nace ya kawo su ba.

Allah tawan, ashe kin iya faÉ—a kema?

Ya faɗa yana 'yar dariya itama murmushi ta mayar masa ta miƙe tana cewa suje yaci abinci ita yau taci nata da yara bata jira shi ba.

Su Hajiya Meeha har an fara wareni saboda ganin yara ko, ina ganin tare ma zamu Kadunan nan.

Wayyo ba haka bane Mijin so na É—an tuna baya ne da nake ci tare da su. Amma zaka bari na sauka a gidan umma ko.

Naƙi wayon a gidana zaki sauka, ko da yake gidan yayarki zan sauka har mu dawo dan haka kije gidan umma wasa nake miki.

Ina godiya babban mutum Allah ya tsare mini kai ya ƙara sutura ya kare ka daga idon maƙiya.

Ameen matar so Allah yayi miki Albarka ya bamu aljanna maÉ—aukakiya.

Sameeha ta amsa da amin ta matsa kusa dashi ta manna mata kiss a gefen kuncinsa domin nuna masa jin daɗin addu'arsa, shi kuma kamota yayi ta mannata jikinsa ya shiga kissing ɗinta kamar sai haɗiye ta, da kyar ta kwace daga riƙon da yayi mata ta wuce dinning da gudu yabi bayanta yana dariya. Hmmm su soyayya daɗi amma in kayi dace da masoyi.

Washe gari.

Ƙarfe goma da kwana a Kaduna tayi musu, su Abi sai murna suke yi da farin cikin son ganinsu Umma, da driver ya ƙarasa dasu ƙofa suka fita da sauri suka shiga gidan da gudu, Sameeha tana dariya tace.

Yau zamu sha karamniya.

Ai gwara kusha, yaushe rabonsu da haka.

Cewar Ibrahim, haka suka fito suka jera zuwa cikin gidan. Umma tana ɗaki taji ihunsu Abi da sauri ta fito dan ta tabbatar saboda abin da mamaki, suna ganinta suka isa suka rungumeta ƙam suna murna, bata dawo daga mamakinta ba sai taga shigowar su Sameeha wanda a zatonta Aminun ne ya kawo yaran, har suka ƙaraso Ibrahim ya rusuna har ƙasa ga gaisheta ta amsa fuska sake tana cewa ya shiga ciki mana ya zai tsaya a waje, yace yana sunne kai ƙasa.

Umma zan dawo anjima yanzu ana jirana ne, na dai shigo ne mu fara gaisawa.

Allah Sarki to ba damuwa Nagode Allah yayi albarka.

Ibrahim ya amsa da amin kana yayi musu sallama ya wuce, su kuma suka shiga ɗakin umma suka zauna, umma ta kasa haƙuri tana cewa.

Sai gaki tare da yara ya aka yi haka?

Hmmm bari dai mu huta Umma zan baki labari, ina Yaya Zaidu da Anwar.

Sunje kasuwa yin cefane, Ikram ma tana hanya tace zata zo tunda taji a gida zaki sauka wai itama zata zo ta kwana biyu.

Mayyata kenan, duk abinda nayi sai ta kwaikwaya, tazo din masha hirar da muka jima bamu yi ba.

Tana rufe baki suka ji an buɗe gate an shigo, ganin sabon takalimi ƙofar ɗakin umma yasa Ikram ta buɗe murya tana oyayo Anty Sameeha, su Abi suka fita da sauri suka isa suka rungumeta, Ikram ta riƙe su tana tambayar yaushe suka zo.?

Tare da Mamanmu muka zo.

Abi ya bata amsa, da mamaki ta ƙaraso cikin falon tana riƙe da haɓa tace.

Anty ya aka yi su Amrah suka je gunki?

Kedai zauna mu gaisa kafin a kaiga yin labarin.

Cewar Sameeha, Ikram ta ƙarasa ciki ta zauna tana gaida umma, daga bisani ta gaisa da Sameeha, a lokacin su Zaidu suka dawo suma suka shigo falo suka zauna suna murnan ganin juna.
[4/26, 7:42 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

41.

Matsuwar da Ikram tayi akan ta faÉ—a musu yadda akayi yara suka zo gunta yasa Sameeha basu labarin komai, sosai suka yi mamakin wai aure zaiyi Zaidu yace cikin É—an murmushi.

Auren dai huce takaici zaiyi amma yasan zai samu lafiya ya sake ki.?

Ka sani ko ya dage da niman magani ya dace shiyasa zai yi auren.

Cewar Ikram, Zaidu yaja tsaki.

Ashe dagangan ya saki Sameeha ko da yake wataƙila dalilin zargin da yake yi mata yasa ya saketa, Allah dai ya tsinewa waɗanda suka aikata miki haka, nifa nafi zargin su Hauwa ne suka shirya miki haka dan ya sakeki tunda ba ƙaunarki suke yi ba.

Ba abin mamaki bane yaya Zaidu Allah ya saka mini ya tona asirinsu.

Cewar Sameeha fuskarta a dagule dan baƙin ciki take ji duk lokacin da aka tuna mata abinda waɗannan 'yan matan da suka ja mata saki uku. Umma tace cikin kulawa.

Allah ya sanya alkhairi ya basu zaman lafiya yasa zata riƙe yaran nan amana.

Duk suka amsa da amin kana Umma ta É—aura da cewa.

Anjima da yamma bayan sallar la'asar sai muje gidansu Najwa mu tayasu aiki zuwa dare Zaidu sai yazo ya É—aukeku ni acan zan kwana da safe zan dawo nayi wanka na sauya kaya na koma.

Nifa umma bazan je yau ba ki barmu kawai muyi hirarmu in yaso gobe in Allah ya kaimu maje.

Cewar Ikram, Sameeha ta ce.

Ni gida naso zuwa na gaishe da Hajiya kafin magrib sai na dawo.

Yauwa muje can na rakaki Anty dan wlh badan Inna ba bazamu je bikin Najwa ba mara mutunci uwar cin Amana.

Ke Ikram bana son shirme fa wai ke abu baya wucewa a gurinki ne, ni wlh bansan ina kika samo riƙo ba, sam bakya barin abu ya wuce kinta mita da naci, karna sake jin haka in ba haka ba ranki zai ɓaci.

Cewar umma cikin faɗa, Ikram bata kuma yin magana ba dan Wlh sosai take jin Haushin Najwa akan abinda tayi mata, nan umma tace ta tashi ta sauya kaya ta shiga kitchen ta ɗaura musu abinci, haka ta miƙe ta shiga uwar ɗakan umma ta sauya kayan jikinta ta fito zuwa tsakar gida dan ɗaura girki, su Umma suka cigaba da hira Anwar ya fito dan ya yiwa Ikram jajjage. Da yamma umma ta tafi gidansu Inna su Sameeha kuma suka wuce gidanta ita da Ikram da yaran gabaɗaya a motar zaidu daya kaisu, daga nan Sameeha zata ɗauki tata motar dan suyi amfani da ita gurin biki.

****

Hauwa.

Suna can babban gida ana ta aikin biki ba kama hannun yaro, dan sosai suka yi gayyatar 'yan uwa da abokan arziki saboda su nunawa duniya wannan karan biki nasu ne sai abinda suke so yake faruwa, shiyasa tun biki saura kwana biyar ta koma babban gida da kwana uzuri mai ƙarfi ke kaita gida ta yi ta dawo, tun jiya take zuba ido taga 'yarta Adama tazo dan haka suka yi da ita in biki saura kwana biyu zata zo ta kwana har sai an kammala biki washe gari ta koma, ta kuma kiranta a waya bata ɗagawa hakan yasa ta ce in yamma tayi bata zo ba zata aika ɗanta yaje yaji ko lafiya. Ɓangaren Adama kuwa tun shekaran jiya laraba take yiwa mijinta mitar ya barta Alhamis taje gida bikin kawunta yace shi bai amince saboda ya gaji da yawan fitanta, ta bari ranar bikin Asabar sai taje washegari kuma ta dawo wato kwana ɗaya ya bata, tace ita fa hakan bai yi mata ba nan ya fice ya barta tana surutai. Washe gari haka ta kuma yi masa magana zata tafi yace bai amince ba saboda baƙin ciki har da kuka tayi masa amma ko a jikinsa ya ficewarsa. Yau Juma'a tana ganin ƙila ya barta taje tayi kwana biyu amma sai yace sai fa ranar biki zata je, nan ne Adama ta zage tayi masa rashin mutunci ta inda take shiga bata nan take fita ba, haushi ya rufe mijin nata bai san sadda ya rufeta da duka ba ita kuma ta shiga auna masa zagi tana yi masa Allah ya isa, takaici yasa mijin yace cikin fushi.

Tunda baki san darajata ki je gida na sake ki saki uku, na gaji da halinki kullun cikin ƙunsa mini baƙin ciki kike yi, sannan nasan kina yi mini asiri amma na jure saboda nasan baya tasiri akaina domin duk abinda kike yi kin fallasa shi a kunne na ji, darajar yaranmu naketa dubawa amma tunda lamarinki ya zama haka na gama datse igiyar auren, yara kuma mahaifiyata zata riƙe mini su sai ki tattara ki tafi gidan ubanki kisha shagalin biki da hujja, ko ki yiwa Kawun naki zaman ɗaki tunda kin zama sakakkiya.

Na shiga uku Basiru ni ka saka, dan Allah na tuba ka janye sakin nan wlh ko bikin ba zani ba, wayyo Allah na tono mini asiri dan Allah ka rufa mini.
Chapter 68 · 0% Book details