← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 103

Sashe 90

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asalin mujaheed su 'yan jahar Gombe ne, mahaifinsa da mahaifiyarsa duk 'yan can ne aiki ne ya kawo babansu garin Kaduna har suka haɗu a nan, shine babba sai ƙannensa mata huɗu duk sunyi aure sai autansu namiji daya rage a gaban mamansu. Mujaheed irin yaran nan ne da basu son wahala kuma basa son karatu balle ya amfani kansa, yafi sha'awar rayuwar yaran masu kuɗi wanda komai sai dai ayi musu ga hutu da jin daɗin rayuwa, sai dai kash shi ba a irin wannan gidan ya taso ba dan babansu ƙaramin ma'aikacin gomnati ne, kafin ya mallaki gida ma sai da suka yi yawon haya har Allah yasa ya samu wani bashi a ma'aikatarsu ya saya gida shi a na cirewa a albashinsa har ya gama biya, da kyar Mujaheed ya kammala secondary ya fara poly bisa matsawar mahaifinsa sai kuma a lokacin ne ya kwanta dama bisa rashin lafiyar zawo da amai da ya kamashi cikin dare kan aje asibiti da safe ya cika. To tun bayan rasuwar mahaifinsu rayuwar tayi musu zafi ɗan sadakar da suka samu na abinci da kuɗi daga ma'aikatar su baba shine suke tsakura har yazo ya ƙare. Mujaheed tuni ya watsar da karatu ya soma bige bige irin harkan waya ya saya ya sayar, watarana aka kawo masa wayar sata ya saya da bincika ya tashi aka zo aka kamashi sai da ya kwana biyu a cel da kyar aka sake shi wanda ƙanin babansu sai da ya baro Gombe yazo akan matsalar, Allah yasa shima ɗan sanda ne shiyasa aka kashe maganar, kafin ƙanin babansu ya tafi sai da ya bashi kuɗi masu kauri akan yaja jali ya tayar da ɗaya masu hayan shagon gidansu ya zuba kayan daya dace, abu kamar wasa Mujaheed ya fara sayar da manja mangyaɗa da su maggi da sauran kayan masarufi, a hankali ya fara bunƙasa wanda a wannan lokacin ne ya tattaro aure domin yana da budurwar da yake mugun so, mamanshi taƙi yarda akan ba yanzu ba ya bari nan gaba, amma ya dage akan zai yi aure wanda yasa shi zuwa Gombe ya sanar da 'yan uwan babansa, su sun mara masa baya a cewar su hakan shine zai sa ya ƙara hankali tunda ya kai munzalin yayi, yana da shekara ashirin da bakwai a lokacin, hakan yasa dole mahaifiyarsu ta amince amma tace dole sai dai ya auri 'yar ƙawarta da take nan Gombe shekarunta sha bakwai, dan a lokacin take kokarin gama secondary, Mujaheed ya amince ganin Safara'u ba mummuna bace shi dai auren yake so. Sai da ta kammala karatunta na secondary kafin aka saka biki wata biyu aka ɗaura ya kawota nan Kaduna gidansu ciki da falo daya gyara, nan ya soma sabon rayuwa cikin rufin asirin Allah. Abinda ya fara haifar masa da matsala da matarsa tun sa'ilin data samu ciki ta soma ƙazanta kala kala har sai da ya dawo ya daina cin abincinta yace ma ta daina girkawa sai dai suci a gurin mamansu, a hankali ta fara sire masa dama ba wani sonta yake yi ba aure ne na biyayya, daga nan ne ya fara niman pyan mata sai dai kuma baya niman daidai shi sai wacce tafi ƙarfinsa, sannan bai tsaya a ɗaya ba hakan yasa 'yan kayan shagonsa suka fara ƙarewa saboda yana yiwa ƙadangarun bariki hidima, shi dai ba zina yake ba amma 'yan taɓe taɓe yana yi, a haka matarsa ta haihu namiji suka saka wa yaron sunan babansu sai suka fara kiranta da maman baba. Watan Safara'u biyar da haihuwa ta kuma samun ciki, sosai Mujaheed yaji haushinta wanda har maganin zubar da ciki ya bata sai dai cikin bai zube ba a haka ya haƙura har tazo ta haifi 'yarta mace suka saka mata Jamila, daga nan ne Mujaheed ya ɗauketa aka saka mata implant shekara biyar dan yace baya son haihuwa tunda ba yi da hali ga rayuwa tayi tsada, da yake ba tada wayo ta yarda aka saka mata, dan sosai take sonsa amma kuma ba ta san ya zata kyautata masa ba, Safara'u irin matan nan da basu iya magana ba duk abinda ta yanko bata taunawa take faɗa, ga ƙazanta ga rashin iya kwalliya ga kuma rashin iya girki, haƙuri kawai yake da ita saboda mahaifiyarsa da take bashi haƙuri take kuma ƙin yarda ya muzguna mata domin ɗiyar ƙawarta ce, sai dai a kullun faɗa mata yake yi duk lokacin daya samu matar data dace dashi wacce zata kula dashi zai aureta, mahaifiyarsa ta bashi wannan damar tunda suna sa xtra ɗakuna a gidan tasan babban matsalar ace haya, kuma ba zai sha wuyarsa ba tunda suna da gidan kansu, wannan ƙarfin guiwar auren da mamamsu ta bashi yasa shi ƙara ƙaimi wajen niman 'yan mata, a hakane kayan shagonsa ya ƙare tas ya dawo abinda zasu ci yana yi musu wahala, sai ɗan kayan girki irinsu daddawa kayan miya da komai na hajar girki da maman ke sayarwa, to sa shine suke samun na abinci, shi kuma ya fita yayi bige bigensa in ya samu ya kawo in bai samu ba ya dawo hannu rabbana.

Wani abokinsa mai wankin mota ne ya kawo maga shawarar ko zai nima tuƙi gidan masu kuɗi shima in ya dace, duk wata sai samu albashi kuma in yayi sa'a har abinci za a riƙa bashi in dai yayi biyayya yadda ya kamata, dan zama haka bai dace dashi a matsayinsa na magidanci ga yara sun taso suna buƙatar a sakasu makaranta, nan take Mujaheed ya amsa shawararsa dan ya jima yana tunanin me ya dace dashi, amma tunda ya iya tuƙi yasan zai ci abinci dashi, hakan yasa Samaila ya ce masa zai haɗashi da wani alhaji da yake wanke masa mota dan yana shiri dashi sosai, Mujaheed yaji daɗin haka tare da yi masa godiya.

A cikin kwanakin Samaila ya haɗashi da Alhaji Baita wanda shine har yanzu yake aiki dasu tsawon shekara huɗu kenan, tsabar tusa kai da yayi a gidan kowa yana sonsa musamman yadda hajiya take yabon halinsa saboda yana matuƙar kwantar da kai da yi mata biyayya, sannan bai da kuiya komin karamin aike zai je, tun ana biyansa dubu sha biyar a wata yanzu ya kai ana biyansa dubu arba'in duk wata, ga kuma yadda suka sake masa da motocin gidan duk inda zaya yakan yi ƙaramar murya gurin Hajiya zata amince masa su bashi key, ya zamana ko aikensa zayi sai ya zaɓi motar da zai je a cewarsa yafin son wacce ba tada matsala saboda yaje ya dawo akan lokaci, da wannan damar ne yake yiwa 'yan mata ƙarya yake kuma kashe musu kuɗi, saboda ba iya salarinsa yake samu ba yana ɗan samun ihisani gurin yaran gidan dana baƙi in sunyi, sannan duk azumi abinci da kuɗi Alhaji ke bashi mai yawa domin Alhaji Baita yana kyautatawa ma'aikatansa sosai. Dalilin daya saka Alhaji yayi faɗa akan rashin dawo masa da mota jiya saboda tun shekaran jiya ya turashi gurin bakanikensa a yiwa motar sabis saboda zai je Abuja da ita, shine Kuma Mujaheed ya samu damar yin tafiyarsa Kano don bikin wani abokinsa da za a ɗaura auren a can da nufin washe gari ya kwaso amarya a motarsa, to a ranar daya kai motar aka gyarata sai ya haɗa baki da bakaniken akan zai yi amfani da motar ya bashi cin hanci. Alhaji ganin mota ta kwana ba a dawo da shi ba yasa shi kiran bakanikensa shine yace da safe zai sallami motar, a haka ne motar har dare bata dawo ba shine Alhaji ya kira bakaniken yaji ko an gama ya kira Mujaheed ya amso masa, bakanike dan kar ya ɓata hanyar cin abincinsa yace tun rana Mujaheed yazo ya ɗauka, dalilin da yasa kenan Alhaji yaita faɗa dan zuba masa ido yayi yaga ko zai dawo da motar da dare amma yaji shuru, shiyasa tun wurin sha biyun dare ya rika kiransa Mujaheed ya ƙi ɗauka, sai ya kira bakanike ya sanar dashi ya sanar da Alhaji tun rana ya basu mota, shiyasa da asuba ya fito daga Kano saboda ya dawo da wuri duk da yasan sai ya sha faɗa.

Cigaban labari.

Mujaheed bai bar gidan ba sai yamma lokacin tashinsa aiki, ya shiga yayi sallama da hajiya nan ta bashi ragowar naman kai daya fara lalacewa tace ya kai gida ko zasu iya sarrafawa, ya amsa yana godiya ya fito ya samu abin hawa, tun a hanya ya kira Sama'ila yace masa.

Abokina zan samu mota mai zafi a gunka kuwa? dan yau ina so na fara niman wata mai zafi.

Akwai mota amma wlh sai ka biyani dan gomnati ta hana aikin banza, sannan awa biyu zan baka dan mai motar da safe zai amsa.

Karka damu inna zo zamu yi ciniki ka tsumayeni bayan sallar magrib.

Ok Samaila yace ya kashe wayar. Mujaheed yana isa gida ya dire ledar naman kai a gaban mamamsu da take zaune a tsakar gida tana tankaɗen gari, yaransa sun zo suna yi masa oyoyo ya amsa yana yi musu wasa kana daga bisani ya sallamesu, sai ga matarsa ta fito tayi masa sannu da zuwa tare da ruwa a cofi, a daƙile ya amsa sannun ya bita da harara tare da kofin data miƙo masa.

Dalla malama nace miki kishi nake ji, ki matsa mini daga nan kan nayi bol dake, nayi tafiya na dawo amma baki san ki tsaftace jikinki ba kiyi kwalliyar tarbata ba, sai tarin tsami da hamami dana ji daga jikinki, wlh ƙazantarki kullun gaba take yi.

Nafa yi wanka, kuma Allah na saka turare.

Safara'u ta faÉ—a tana turo baki, sai ta wuce, Mujaheed ya bita da jan tsaki, mama ta ce cikin faÉ—a.

Haba Jaheedi nace ka daina yi mata irin haka In Sha Allah zata bari dan ina ta nuna mata, kai da ka dawo daga tafiya meye na ƙorafi.

Mama kema kinsan halinta ai haƙuri kawai nake yi, bama wannan ba ga naman kai hajiya tace na kawo muku ku sarrafa mana.

Kai haba? Kashe zamu sha farfesu, aiko yanzu zan tashi na É—aura dan mu karya dashi, kaga da safe sai ka siyo mata biredi mu haÉ—a muci.
Chapter 90 · 0% Book details