Sashe 98
Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shuru tayi tana faɓe baki, Mujaheed yaja guntun tsaki ya miƙe ya shiga bayi yayi wanka da alwala kana ya fito itama ta shiga tayi nata. Wajen ƙarfe takwas da kwata aka aiko yara suka kawo musu abin kari kunun Tsamiya a katon jug sai kosai a ƙaramar kula, Najwa ta amsa ta aje har Mujaheed ya fito daga uwar ɗaka cikin shirin fita yana gyara zaman hular kansa ya zauna a cushing.
Har an kawo abin kari kenan? Samo mana kofi ki zo mu karya.
Najwa ta miƙe ta ɗauko kofi biyu ta aje tana zuba kunun taji wani baƙin ciki ya rufeta, sai da ta miƙa masa ya amsa kana ya buɗe ƙosan yana hamdala.
Yauko zan yi kari mai nauyi zanji daÉ—in kunun nan.
Aiko kai ne zaka sha dan banga dalilin da ina amarya za a tarbeni da kunu da ƙosai ba a abin kari, duk talauci da lalacewa ai na cancacni biredi da kayan tea ko ba kwai.
Haba Najwa ki zama mai godiyar Allah wani ruwan koko ma nima yake bai samu ba, amma ke kin samu har da ƙosai da zafinsa kina kushewa, na kula kema kina da hangen nesa kuma ya kamata ki dawo da tunaninki daidai tunda tsakanin ni da ke mun san juna ba sauran ƙarya, haka muke rayuwa a gidan nan dai dai ƙarfina ba zaki zo ki sauya mini tsari ba.
Dole kace haka mana tunda ka riga kaci moriyar ganga dama, ka gama yi mini ƙarya ka aureni, ai wlh banda darajar iyaye baka isa nayi zaman aure da kai ba domin nafi ƙarfinka.
Murmushi Mujaheed yayi wannan karan bai tanka mata ba ya cigaba da karinsa ita kuma bini bini tana jan guntun tsaki, daya gama zai fita ta tareshi da.
Ka bani kuÉ—i zan samawa kaina abinda zan ci.
Idan ba zaki ci wannan ba ki zauna da yunwa cikinki ne. Ni dai bazan yi miki abinda banda halinsa ba. Ki saka hijab muje mu gaishe da mama idan kin gadama.
Yauwa gwara daka ce inna ga dama dan maman ba ta kowa bace.
Girgiza kai Mujaheed yayi tare da kwafa ya fice, ya kula Najwa tanada rashin kunya kuma dole ya seta mata hanya dan bazai ɗauki raini ba tunda Safara'u ba haka take masa ba, ya tsaya a ƙofar ɗaki har fito sanye da hijab yayi gaba ta bishi a baya, a nan falon mama suka tadda su gabaɗaya suka karya dan Safara'u komai take yi a dakin mama barci ke mayar da ita ɗakinta, suka zauna a tabarma da Mujaheed ya shimfiɗa daga gefe suka gaisa da mama ta amsa cikin fara'a tana tambayar Najwa kwanan baƙunta, tace lafiya lau kai a sunkuye kamar wata salaha, a nan ne Mujaheed yake cewa.
Mama dama nace yau da safe sai muyi maganar rabon kwana tunda ga Safara'u ga ki, ina ganin in Najwa ta gama sati É—ayanta sai a fara rabon kwana biyu biyu ko wacce mai girki sai ta girka duk abincin gida.
Baban Jamila ai tun yanzu amarya take fara girki tunda kwananta ne, ko ya kika ce mama.
Cewar Safara'u cikin zaƙuwa, Mujaheed ya danƙara mata harara.
Uban waye ya yace ki saka baki ina magana, bana son sakarci.
Haba Jaheedi meye kuma haka ai gaskiya ta faÉ—a, amarya gobe In Sha zata amsa girki har sai ta cike kwanakinta kan Safara'u ta amsa.
Dan Allah ina da magana.
Najwa ta faÉ—a tana É—ago kai, Mujaheed da shima bai gamsu da maganar mama ba yace tayi maganarta.
A gaskiya tun farko Mujaheed baka sanar dani kana da mata ba sai da aka kawo ni ne nasan da haka, kaga kuwa yanke mini hukuncin yin girki bai taso ba in dai za ayi mini adalci, tun farko ban zo gidan nan da tunanin yin girki da yawa ba balle rabon kwana amma tunda hakan yazo mini a ƙaddarata dole ne ya fita duk kan hakkinmu matsayinsa miji, dan haka rabon kwana bibbiyu yayi sai dai gaskiya bazan iya girki haka ba ko wacce ta girka abinda zata ci duk mai miji ta girka da miji in ba miji mace ta girka ita kaɗai.
Yarinya baki isa ki tsara mana tsarinki ba, batun bakisan kina da kishiya ba wannan tsakaninki da Jaheedi ne ki sauke akansa, amma haÉ—a girki ba fashi dole ne duk mai girki ta girka duka gida sannan wacce ba tada girki itace keda alhakin sharan gida da wanke bayi da wanke wanke, mai girki girki kaÉ—ai zata yi a ranarta sai in ta fita tayi sauran ayyuka kinji na gaya miki, wannan dokata ce dole a bi.
Dokarki ce wannan ba dokar Allah ba kuma ni dokar mijina itace ya zama wajibi nabi domin shine ya aje ni ba zaman wani zanyi ba. Mujaheed kayi magana da mahaifiyarka duk dokarta ta tsaya akanka amma ni bazan bi dokarta ba domin ba haka musulunci ya tanadar ba hakkina a wuyarka yake.
Lallai yarinyar nan ba kida kunya ni kike faÉ—awa haka.
Mama ta faÉ—a tana nuna kanta, Safara'u kuwa tafÉ—i ta ce tana girgiza kai, Mujaheed ya sauke ajiyar zuciya.
Mama kiyi hakuri zan fahimtar da ita Najwa muje É—aki muyi magana.
Wlh Mujaheed bazan iya duk abinda ta faÉ—a ba ina da bayi da kitchen a É—aki z me zai haÉ—ani da shara wanke bayi da wanke wanke, wannan ai zalunci da son rai ne.
Ke Najwa ya isheki haka! mahaifiyata ba tsararki bace da zaki riƙa faɗar duk abinda yazo bakinki.
Barta tayi mini rashin kunya, dama ba tada tarbiyya, kuma ki sani na amince da aurenki ne kawai domin ki zo ki riƙa gyaran gida kina wanke bayi da shara dan aikin Safara'u ba iya shi tayi ba domin ke kin fita waye da sanin duniya, idan kuma kin saka iskanci zaki wa aurenki domin wannan auren bazai je ko ina ba dan ba zamu iya ba.
Wannan ya tabbatar da ni baki ɗauke ni a matsayin 'yarki ba kuma wlh ba zaki taɓa juyani ba domin ba ke nake aure ba, ashe ba don Allah kike son zama da shi ba saboda naki cikar burin ne ga 'yar aiki ya auro ko, to ban ga uban da ya isa ya tilasta ni akan haka ba, mama kin so kanki kin ji.
Tasss Mujaheed ya kwaÉ—a mata mari Najwa ta dafe tana murmushin takaici.
Ai dama tunda na tabbatar da kai matsiyaci ne to tabbas zan ga fiye da haka a gunka, kuma Allah ya isana.
Tana gama faɗar haka ta miƙe fuuuuu ta bar ɗakin cike da tsananin takaici, babu abinda yafi ɓata mata rai sama da wai ya aureta ne domin ta zama musu 'yar aiki, yanzu ne ta gane tsagwaron rainin wayon da suke da shi, lallai bata jin wannan auren zai je ko ina, a fusace ta ɗauki wayarta ta kira Anty Saleema domin ita ce kaɗai zata iya seta mata hanya a yanzu, wayar ta kusa tsinkewa ta ɗaga Anty saleema ta ce.
Mara mutunci to miye kike kirana kin gama watsa mini ƙasa a ido, gashi kin ƙi Alh. Atiku to Malam ya bashi 'yarsa zai aura 'yar uwargidanmu, kinga kinyi asara domin na samu labarin wanda kika aura matsiyaci ne yayi miki karya, halan har yanzu kina gida baki koma ɗakinki ba?
Najwa fashewa da kuka tayi tana magana cikin kuka a haka ta bata labarin duk abinda ya faru yanzu da maganganun mamanshi, murmuahin takaici Saleema tayi.
Yanzu wa gari ya waya, wanda ya buga sammako, ni me zan miki bayan kin ɓata komai da hannunki, na tabbatar da Alh. Atiku kika aura wlh sai ya mayar dake sarauniya amma ba kida rabo, dan ko kin fito babu abinda Alh. Atiku zai yi dake domin kuwa malam ya gama yin aiki akan 'yarsa kuma Atiku ya ruɗe akanta sai ɓarin kuɗi yake musu. Ni baƙin ciki kika yi mini amma baki mini ni kaɗai ba har da ke.
Na shiga uku Anty ya zanyi dan Allah in kashe auren nan in dawo gunki, wlh zanyi miki biyayya nasan zaki samo mini miji mai kuÉ—i.
Wa? wlh Najwa badai gidana ba malam ko mai kalarki ya gani sai ya hanata shiga gidanmu, dan haka ki zauna a inda ƙaddararki take dan kuwa baki zo duniya a sa'a ba.
Najwa ta rushe da kuka tun ba aje ko ina ba taji ba zata jure zaman auren ba.
Ba kuka zaki ba ki tashi ki nimawa kanki 'yanci dan yanzu an daina zama haka, ki tura mini kuÉ—i in kina da shi nasa ayi miki aikin mallaka yadda zaki juya mijin da uwarsa.
To to anty kamar nawa zan turo?
Dubu É—ari yayi dan aiki zan saka ayi miki mai kyau.
Wlh banda su duka sai dai ƙila ki samu hamsin da wani abu.
Ki turo su na cika miki badan halinki ba, yar banza ana nuna miki abu kina runtse ido, gashi ba aje ko ina ba kin gane kuranki.
Nagode nagode anty sai kin jini.
To zan tura miki account number É—ina in kin saka ki sanar dani.
Da haka suka rabu, Saleema ta saki shewa tana dariya.
Shegiya kuÉ—ina da kika É—auka sun dawo cikin ruwan sanyi har da riba, babu abinda zan yi miki halinki ya amshe ki a gidan, in kin kaso auren kya nima gidan zama ba dai nan ba.
Tayi maganar a fili tana 'yar dariya sai ta fice ta cigaba da harkanta. Najwa kam bata san fitan Mujaheed ba dan shuru shuru har daga bisani taji hirarsu mama a tsakar gida hakan ya tabbatar mata da ya tafi aiki, dole dai wannan kunu da ƙosan ta karya da shi dan ba tada wani mafita.
*****
Jamila.