Sashe 94
Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cewar wata figigiya data fice tana surutai, wacce aka kira da j'Jimmai ta bi bayansu suka fita Najwa ta koma ta zauna a gefen gado ta dafe kanta da hannu bibbiyu ta jijjigashi saboda nauyin da yayi mata, ga ƙirjinta da taji kamar an tokare da abu mai nauyi, ta kasa gasgata abinda idanunta suke gani, jin zuciyarta take kamar zata face dan raɗaɗi da zafin da yake yi mata, sai ta buɗe baki iya ƙarfinta ta saki wani irin ihu sai kace mai tashin jinnu, gani take hakan shine kaɗai zai sama mata sauƙin yanayin da take ciki, sai ta kuma ƙara sakin wani ihun ta fashe da gigitaccen kuka babu hawaye, haka ta miƙa ta zare ɗankwalin kanta ta barbaza gashin kanta tana kai koma jikinta rawa kawai yake yi, ga wani gumi da take ji ya rufeta.
Wannan ihun da ta yi yasa 'yan uwan ango ruɗewa da tunanin ko mahaukaciya Mujaheed ya auro, nan take ƙanwarsa Jimmai ta kirashi a waya, yana ɗagawa ta sanar dashi yazo amaryansa ba lafiya, cikin tashin hankali ya nufo gida dan dama ya sallami abokansa yace baya buƙatar rakiyarsu, saboda bai san wani tarba zasu samu ba a gurin Najwa, yana shiga gidan ya taddasu sun yi cirko cirko a tsakar gida, ya tambaye su tana ina? mama tace.
Tana É—akinta, yarinya sai tsala ihu take yi kamar hauka sabon kamu.
Mujaheed bai tsaya jin maganar mama ba ya wuce ciki, direct ya shiga uwar É—aka, yadda ya ganta shima ya ji tsoro, Najwa kuwa tana ganinsa ta tsayar da kallonta gareshi sai a sannan ne taji hawaye ya soma kwaranya daga idonta yana sauka a kuncinta, ssi ta nuna shi da yatsa.
Mujaheed kai waye? waya turoka ka kazo ka yaudareni da zantukanka na ƙarya, nan ina ka kawo n?i ba haka muka yi da kai ba, meyasa ka zamo wanda zai rushe mini duk wani farin cikin rayuwata. To wlh bazan zauna da kai ba ka sakeni kawai domin ni ba ayi ni dan zama a irin wannan gidan ba, ni ba matar da zata zauna da kishiya bace, Allah ya isa tsakanina da kai kacuceni ka rusa mini rayuwata, a karo na biyu zan ƙara zama bazawara.
Sai ta tsuguna tana rushewa da kuka, Mujaheed ya risina dan ya kamata ya bata haƙuri, Najwa data ɗago kai iya ƙarfinta ta wanka masa mari.
Karka kuskura ka taɓani wlh.
Mujaheed ya dafe kuncinsa yana kallonta dan sosai ya tsorata da ita, bai taɓa zata zai fuskanci irin wannan ƙalubalen ba, yana ganin ai soyayyarsa tayi nisa a zuciyarta ko dan saboda nasarar yayi akan haka zata haƙura ta zauna dashi, sai kuma ya gane maganganunsa na ƙarya sune take so ba shi ba, ya miƙe ya tsaya yama kasa magana banda kallonta da yake yi, Najwa ta miƙe ta raɓe shi ta wuce zuwa falo Mujaheed yabi bayanta, kitchen yaga ta shiga ba jimawa ta fito riƙe da wuka a hannunta, Mujaheed da mugun sauri yayi baya yana cewa.
Najwa meye haka? Me zaki da wuƙa?
Kashe ka zanyi muddun kaba ce ka sake ni ba dan bazan taɓa zama da kai ba.
A'a Najwa dan Allah ki mayar da wuƙar nan.
Mujaheed ka sake ni tun kafin na illataka wlh bazan zauna da kai ba.
Shikenan ki aje wuƙar muyi magana.
Ya faÉ—a a kiÉ—ime yadda yaga ta nufo shi gadan gadan dan babu alamar wasa a maganarta, Mujaheed yayi tsalle ya haye kujera ya shiga kwalawa mama kira.
Mama! Mama! ki zo Najwa zata kashe ni Mama.
Bai rufe baki ba Mama ta shigo ɗakin, ganin wuƙa ƙiri ƙiri za a kashe mata ɗa sai ta saki salati tana cewa.
Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, Mujaheed ka auro mahaukaciya zoka fita ta nan kafin ta yi maka illa.
Mama ta nuna masa hanyar da zai bi, Najwa ta isa gurin ta tare, Mama tayi baya tana salati, Mujaheed haka yayi ta maza ya diro ƙasa ya tsaya Najwa tana kai masa wuƙa yana gocewa, a haka ya samu damar cafke hannunta ya kama gam ya kwace wuƙar kana ya juya ya fice da gudu da wuƙar a hannunsa, dama tuni mama ta fita tana bada saƙon a fita a kira maza su kawo musu ɗauki, sai ga Mujaheed ya fito a lokacin, Najwa ta durƙushe a ƙasa ta saki marayan kuka wanda yake tattare da tsantsar baƙin ciki, sai da tayi mai isarta kafin ta miƙe ta koma uwar ɗaka ta yafa gyalenta ta ɗauki ƙaramar jakarta kana ta ɗauki ɗankwali ta riƙe a hannu ta saka takalminta, sai ta fito ta tadda su a tsakar gida suna mayar da magana, suna ganinta duk suka yi shuru ta tsaya tana cewa.
Idan baka aiko mini da takardar saki ba to ka saurari sammaci daga kotu.
Tana gama faɗar haka ta juya ta fice daga gidan, Mujaheed ya yi yunƙurin bin bayanta mama ta dakatar da shi.
Kasan Allah ba zaka bita ba bar ta tafi gwara ma ka saketa dan kar ta kashe mana kai abanza, saboda wannan da gani mahaukaciya ce.
Mama wlh da hankalinta kuma duk laifina ne dana yi mata ƙarya amma In Sha Allah komai zai yi daidai dan ina ƙaunar matata ba zan iya sakin ta ba wlh.
Au haka kace ko, to idan tayi ajalinka shikenan Allah ya jiƙanka.
Tana gama faÉ—ar haka ta wuce É—aki cike da takaici, haka sauran suka dinga mayar da magana, Mujaheed komawa É—akin yayi ya zauna ya rungume hannunsa yana tunanin abin yi. Najwa kuwa tana fita ta samu mashin ya É—auketa akan É—ari biyar ta hau ta nufi gida.
[5/23, 7:35 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*
56.
Najwa.
Tana isa gida ta shiga kai tsaye babu fargaba ko shakkar ba zasu karɓeta ba, kamar wacce aka koro idanunta nan a koɗe ta shiga, sauran matan da basu samu damar kaita ba sune suka yi tozali da ita, suna ganinta suka saki salati da tambayar lafiya? ina sauran matan da suka yi mata rakiya zuwa gidanta?, dan har lokacin basu ƙaraso ba, inna data ɗan miƙe haƙarƙarinta a gado dan ta huta kafin 'yan kai amarya su dawo, jin an ambaci Najwa da salati yasa ta sauko ta fito tana salati, tana ganinta kuwa gabanta yayi mummunar faɗuwa, ta tsaya ta kasa yin magana ita kuma Najwa jikin bango ta raɓe tana matsa yatsunta ga gyalenta ya rufe fuskarta balle a san wani matsayi idanunta yake ciki, shigowar 'yan kai amarya yasa gidan ya hautsine suna ta zambaɗawa abokan ango zagi akan rashin dawowa dasu da suka yi ba, a lokacin ne goggo ta ke cewa inna.
Wlh mun ci uban tafiya kafin muka kai babban titi muka samu mota bus ta ɗebomu, ga su can mun barsu da Junaid zai biya kuɗin motar, dana san ba zasu dawo damu ba ai da da shirina na fita yadda zan yiwa kaina taimakon gaggawa, ga ƙafafuna har zugi suke yi mini dan wahala.
To ai amaryar da kuka gama wahala akanta gata ta rigaku dawowa, mun É—auka ma ko kun san da dawowarta ko faÉ—a aka yi a gidanta ba a rabu ta daÉ—i ba.
Cewar wata tsohuwa dangin inna, ai da tsananin mamaki duk suka bi inda aka nuna Najwa, sai suka saki salati suna mamakin ganinta, nan suka shiga mayar da zancen a can gidan suka barta ya akayi harta rigasu dawowa? kuma lafiya lau ba abinda ya faru na rikici a gidan, a lokacin baba ya shigo Junaid na biye dashi a baya suna maganar rashin mutuncin mai bus akan dole dubu biyar aka biya shi, ganin kowa a tsaye sunyi cirko cirko yasa su tambayar meke faruwa. Inna data kasa tsayuwa ta ja ƙaramar kujera ta zauna tana nuna musu inda Najwa take tsaye.
Gata nan ta kuma dawowa har ta riga waɗanda suka kaita saurin shigowa gidan, ban san me ta aikata ba, ban san me Najwa take son zama ba, ita kaɗai mace a cikin yaran nan amma tana son ɗaura mini mummunar hawan jini wanda ƙila sai tayi ajalina hankalinta zai kwanta.
Inna ta ƙare maganar tana matsar kwallar baƙin ciki, baba salati ya saki yana ambaton sunan Najwa, Junaid kuwa wani uwar tsawa ya daka mata yana nuna ta da tsaya.
Me ya dawo dake? Meya faru kuma zaki dawo mana gida bayan mun sallameki.
Wlh Allah ni ba zan koma gidan Mujaheed ba, bazan iya zama da shi ba saboda makaryaci ne yaci amanata ya yaudareni ya aureni da ƙarya, duk kuɗin da yake faɗa karya ne gidan da aka kaini wlh ba shi bane wanda ya faɗa zan zauna, bai sanar dani yana da mata ba, komai nashi shiri ne kamar an haɗa baki dashi ne domin a cutar dani.
Najwa ai baki gama ganin komai ba domin kuwa irin Mujaheed ne ya dace dake, sam ba kida godiya Allah komai naki baki sanya tsoron Allah a ciki sannan kin ƙi yarda kin yi kuskure, aurenki na baya baisa kin gane kurenki ba balle ki shiga hankalinki, to hassadarki itace ta kawo ki wannan matakin kuma wlh dole ki koma ki karɓi ƙaddarar da kika zanata da hannunki, baki isa ki mayar damu mutanen banza ba, maza juya mu tafi tun kan raina ya ƙara ɓaci dan kin san zan iya karya ki wlh.
Haba yaya miye laifina dan na zaɓawa kaina inda zan huta, taya na bar gida irin wannan in yi fatan samun irinsa, ni ba zan koma ba, ba zan zauna da makaryaci ba kuma...
Bata kai aya ba Junaid ya nufe ta gadan-gadan zai rufeta da duka sai ta zabura ta ɓoye a bayan wata mata ta soma kuka, Baba da baƙin ciki yasa ya kasa magana tun ɗazun ya dakatar da Junaid yana cewa.