← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 103

Sashe 47

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cewar Sameeha suka fito daga gidan suka shiga mota sai da tayi Bisimillah da addu'a kafin ta kunna motar tana jinta kamar sabon hawa dan ta jima bata yi tuƙi ba, sannan a wani ɓangare tunanin yaranta ya dameta dannewa kawai take yi. Haka suka kama hanyar unguwar rimi Ikram sai hira take yi mata ta amsa mata wani wani kuma tayi shuru har suka isa tangameman gidan su Khairy dan sosai ta gane kwatancen da ta yi musu kuma sun tsaya a hanya sunyi tambayar gidan Alh. Ali Turaki nan aka nuna musu hanyar da zai sadasu da gidan sai gasu a ƙofar gate, ta buga hon aka buɗe mata gate ta cilla motarta cikin gidan, yadda taga baban gida ne har da titi a ciki yasa ta ruɗe ta rasa ina zata yi parking sai da wani security yazo ya nuna mata gefen hagu yace ta shiga titi tayi parking gurin wasu fulalowi dan duk ko ina motoci ne kamar ana gasarsu, ga kuma kanofi da aka kafe daga can ɓangaren dama duk maza ne a gurin, bata ma san ta ƙofar da zasu bi ba su shiga sashin gidan, nan ta kira Khairy ta faɗa mata sun iso ta fito ta shiga dasu, sai tace ta yi hannun dama ta wuce wannan kanofi ɗin gata nan zuwa. Haka ta kashe mota ta fito riƙe da jakarta ta gyara zaman gyalen a kafaɗa, suka fara tafiya har suka kawo gurin mazan nan sai duk Sameeha taji ta tsargu kamar ita kaɗai ake kallo sai ta ƙara sauri dan su wuce gurin gashi ta ɗaure fuska hanya kawai take kallo, Ikram tana biye da ita a baya dan ta kasa kamota saboda saurin data ƙara, can ta hango Khairy tana tahowa bata san sadda ta saki murmushi ba dimple ɗinta ya lotsa wushiryar ta fito har ta ƙarasa gurinta, khairy ta rungumeta tana cewa.

Oyoyi ƙawata sannu da zuwa. Ikram ya hanya ya kuka baro umma.

Lafiya lau tace a gaishe ki tana muku murna Allah ya yiwa karatunsa albarka.

Cewar Ikram, Amin ta amsa ta kama hannun Sameeha suka wuce wani madaidaicin gate, suka shiga wani gida a ciki, har babban falonsu daya sha kayan alatu ta kaisu ga mata cike a falon wasu sai hotuna suke wasu suna cin abinci wasu kuma suna zaune a kujeru da carpet suna kallo, Khairy har gaban wata dattijuwa ta kai Sameeha ta zauna a ƙasa kusa da karar ta, matar tana kan kujera ko ba a faɗa ba itace mahaifiyar su Khairy dan ta hango kamarsu, Sameeha cikin girmamawa ta gaisa da umma tare da juyawa ta gaida sauran mata tana yi musu Allah ya sanya alkhairi, Ikram ma bata yi ƙasa a guiwa ba ta shiga gaishesu suna amsawa, Hajiya ta kalli Khairy da sai dariya take tace.

Wannan ita ce Sameeha ko.?

Ta faɗa tana nuna Sameeha wacce nauyinta yasa ta ƙara sunne kai tana murmushi, cikin sauri khairy tace.

Hajiyarmu ita ce dan Allah baki ga kamanninta da Mubeenarmu ba, wannan kuma ƙanwarta ce.

Aiko dai suna yanayi da ita, Hajiya Fatima gafa mai kama da É—iyarmu.

Ta faɗa tana magana da ƙanwarta Fatima, Da sauri ta juyo dan tana magana da wasu mata tana cewa.

Wallahi tunda suka shigo naketa kallonta sai dai tafi Mubeena haske, Allah dai ya jikanta.

Duk suka amsa da amin, nan fa Khairy ta wage murna tana cewa.

Jama'ar gidan nan ku zo ga Sameehata ta zo ku fito ku ganta ku kwashi gaisuwa.

Nan fa duk hankalin mutane ya dawo gunta suka fara dan dazo a falon, waɗanda suke ɗakuna suka soma fitowa sai faɗi suke ina take ina take?. Lamarin yayi matuƙar bawa Sameeha mamaki yadda kowa keson ganinta, Ikram kuwa sakin baki tayi tana kallon ikon Allah, ta rasa ma me zata yi tunani akai, falon ya ƙara cika sosai Sameeha ko kunya ce ta hanata ɗago kai tare da mamakin wannan tururuwa da ake yi dan aganta, ta rasa me Khairy ta sanar dasu ko kuma kila suna son ganin me kama da Mubeenansu ce. Anty Aisha ce ta tsallako ta zo gabansu ta zauna itama ta ɗago kan Sameeha tana dariya.

Ke É—ago mu ganki sai sunne kai kike kamar wata amarya.

Aisha ku barta ta huta haka kun sa ta kasa sakewa, ke Ƙanwata taso mu shiga ciki dan ba zasu barki ba.

Cewar Anty Amina data kama hannunta ta shiga janta, Ikram ma ta miƙe ta bi bayansu, Hajiya tana cewa.

Ki sauke su falon Abbanku tunda ba kowa a can dan Allah kar a takura mata.

To anty Amina tace sai Aisha itama ta bisu. A wani katon falo aka sauke su ga lafiyayyun kujeru na alfarma sai kace mai É—akin yana raye, ga katon hotansa a jingine a bango ga kuma sauran hotunan da yake tare da iyalinsa gana Hajiyarsu, na yaran ma ga nasu, sai wani tashin kamshi ke tashi a falon. Bayan sun zauna Amins tace.

Ni ce Amina wacce kika taɓa yin waya da ita. Muna farin ciki da zuwanki domin kin kore mana kewar Mubeena.

Shigowa Khairy tare da wata mata yasa suka yii shuru har suka ƙaraso riƙe da tire biyu duk da kuloli da kuma drinks da plate, Aisha tace.

Yauwa gwara da kuka kawo in taci ta ƙoshi sai ta fito muyi hotuna. Ni bari na je naji da baƙina.

Ta miƙe ta fita, Anty Amina ma fita tayi tare da matar da ta taya khairy kawo musu abinci, nan fa ta shiga zuba musu waina da miya yaji ƙashin rago, ga kuma fried rice mai kyau ga pepper cikin da kuma samosa da meat pie da aka saka a foil paper, ga drink na kanti da kuma kunun aya da zoɓo, Sameeha ta kallesta tana cewa.

Duk wannan abincin ina zamu kai shi? Sannan me kika faÉ—awa 'yan uwanki suke ta son gani na ne?.

Ku zaku cinye abincin mana, sannan sun ga mai kama da Mubeena.

Anya zan yarda dake kuwa.?

Sameeha ta faÉ—a tana 'yar dariya, Khairy ma dariya tayi tana cewa.

Ni dai ku ci abinci ku ƙoshi gani nan zuwa.

Ta faÉ—a ta wuce, koda ta fita tambayar inda yayansu Ibrahim yake tayi amma aka sanar da ita kamar baya nan tun É—azu, dan mutane suna ta zuwa suna tambayarsa ba ya nan. Sai ta wuce É—akin Hajiya da niyyar ta É—auki waya ta kira shi.
[3/4, 10:56 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

30.

Ikram saukowa tayi kan carpet inda aka jera musu abincin ta soma ci tana cewa.

Wlh yau sai nayi halin Najwa na kwaÉ—ayi, sai na cika cikina sosai na kwashi gara.

Ki dai ci a hankali karki sa muji kunya.

Cewar Sameeha data sauko itama ta wanke hannu a ruwan da suka kawo musu, sai ta fara cin wainar ta kai lomar farko sai taga wani ƙashi ya biya mata ta ɗauka ta kai baki tana yagar naman jikin ƙashin, sai ga Ibrahim ya fito daga cikin wani ɗaki kuma dai dai setinta, yana buɗe kofar suka yi ido biyu da Sameeha, bata san sadda ta saki ƙashin ba ya faɗi ƙasa ta sunne kai tana yiwa kanta dariya dan wlh dama a ɗarare take ci saboda kar wani ya ganta, tana mugun jin kunyar cin abinci a baƙon guri, Ibrahim ya zauna a cushing yana danna waya yayi kamar bai gansu ba, Ikram ce ta gaishe shi cike da ɗan tsoro dan ta gane shi shine Senator ɗinsu, dama data ga hotonsa a falon tana ta tunanin kamar ta taɓa ganinsa sai da ya fito ne ta gasgata shine Senator da akayi saɓensa watannin baya kuma shine yaci dan shi ma suka jefawa ƙuri'arsu. Kenan shima yayan Khairy ne, tace a zuciyarta cike da tsantsar mamaki da tunanin khairy ba ta ɗauki duniya da zafi ba har ta iya mu'amala dasu ta jawo su jikinta. Ibrahim ya amsa mata a daƙile fuska a ɗaure, saboda barci ya tashi kuma ga yunwa yana ji, Ikram ta cigaba da cin abincinta. ganin da alama an karramasu ne yasan abinci lafiyayye ne a kular daya gani, sai ya buɗe baki yana cewa.

Ke É—auki plate ki saka mini abincin dake kular.

Sai da Ikram ta yi waige waige dan a zatonta da wata yake yi sai kuma taga ba kowa sai su ne a falon, shi kuma bai sake maimaitawa ba ya cigaba da latsa waya. Ikram ta haɗa ido da Sameeha sai ta ƙifta mara ido akan ta zuba masa, Ikram ta buɗe baki tace.

Akwai waina da shinkafa wanne zan saka?

Fried rice ce?

Eh.

Oka saka kaÉ—an sai ki kawo mini coke kuga É—aya da ruwa.

To tace masa sai ta ɗauki plate mai kyau ta zuba masa ta saka masa naman kazan da yawa a gefe, sai ta saka cokali ta miƙe tare da bottle water da kuma coke drink ta kai masa ya amsa ya ajiye akan cushing ya miƙe ya saka wayarsa a aljihu ya ɗauki abincin da ruwan ya koma ɗakin data fito ya turo ƙofa, yana rufewa Ikram ta waro ido waje.

Anty kin san wanene shi? Sanator ɗinmu ne fa na nan cikin Kaduna, ashe yayan Khairy ce bata taɓa faɗa mana ba, wlh shine dan na shaida hotonsa sosai shi muka sakawa ƙuri'armu lokacin kina Lagos aka yi zaɓe.

Ashe shiyasa ya fito yana jin kansa sai wani É—aure fuska yake yi.

Hmm mulki kenan anty, gaskiya su Khairy ba ƙaramin arziki garesu ba, nayi mamaki data ke zuwa gidanmu har taci abincinmu.

Wannan shi ake kira da gadon arziki ba wanda suka yi haye ba, kuma in da dukiya akwai tarbiyya to dole za kiga haka. Ni saka mini shinkafar na fasa cin wainar.
Chapter 47 · 0% Book details