← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 103

Sashe 91

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mama ta faÉ—a cike da farin ciki dan tana jin batun nama ta saki fushinta, Mujaheed dama hakan yake so sai ya gyara zama yana cewa.

Mama nafa samu matar aure a hanyar dawowa ta Kano, kuma wannan karan da gaske nake yi.

Allah Jaheedi? kana ganin ba matsala? ni tausayin Safara'u nake yi ta zauna da kishiya yarinya ce har yanzu, ban da Allah ya tsagaita mata haihuwa da yanzu kunyi yara hudu ko biyar, ina ga watan gobe zaku shekara bakwai da aure.

Mama macen da bata kula da kanta ba taya zata kula da 'ya'yanta, bayan yanzu ma kece take bari da wahalar yaran, gwara da haihuwar ta tsaya kinga amarya tazo ta zuba nata guda biyu, daga nan yara huÉ—u sun ishe ni.

Ƙarya kake yi wlh Jaheedi, yara kam yanzu ka saka ƙafa ko ku ku shida na haifa banda Allah yasa babanku ya rasu ƙila da kunfi haka, dan haka ina son ganin jikoki da yawa ga gidanan muna da wajen kula dasu. Amma ɗiyar wacece ka samu.

Anjima zan fara zuwa hira a nan Badarawa take.

To madalla Allah yasa albarka yasa rabonka ce. Kaga sai ka soma gyaran É—akin can kayi masa fenti ka gyara silin da kuma simintin daya fashe.

Ai har da bayi zan yanka ta bayan can in gina mata ta uwar É—aka, sai kuma nan gaban zan gina mata kitchen kinga ba ruwanta da tsakar gida sai ta fito shanya.

Tofa amma kasan Safara'u sai ka yi mata haka, dan ita ciki da falo ne kawai.

Wlh bazan yi asarar kuÉ—ina ba Mama, sanin kanki ne bayin tsakar gidan nan in ba ke ce kika wanke ba ko kika matsa mata ba yi take yi ba, in yi mata bayi a É—aki ai wlh watarana É—akin ba zai shigu ba, kitchen kuma garin sakacinta taje ta ja mana gobara, gwara ta tsaya a yadda take, wannan ma dan 'yar gayu ce kuma 'yar zamani shiyasa zan yi hakan.

Jaheedi adalci dai nake nuna maka kuma tun yanzu ya kamata ka fara.

Mama zanyi wa Safara'u komai amma banda bayi da kitchen a É—aki. Ni bari naje masallaci ana kiran sallah daga can zan wuce hira.

Allah ya bada sala ka dawo lafiya.

Cewar mama, sai ga Safara'u ta fito daga É—aki ta zauna a tabarma kusa da mama.

Ya zaki zauna kina jin ana kiran sallah, maza tashi dalla komai naki sai an gyara miki mace sai kace saniya.

Kai mama shi yamin kema ki mini da wanne zanji? kuma ai ina iya ƙoƙarina.

Dalla can ai gashinan garin sakacinki zai sa Jaheedi ya ƙara aure.

To mama in ya ƙara kaina zata zauna, ai kinga nima na huta da wahalar sharan gidan nan in tazo ta riƙa yi ta girka mana abinci.

Eh lallai yau na ƙara tabbatar da ba kida hankali, wato wautarki harta kai haka, Kishiya fa ake maganar za ayi miki amma ko a jikinki.

Kaina farau hmmm, ya yi mana kin ga wlh ya auro mana 'yar aiki ko mama, ke ma kya samu ki riƙa hutawa kina barcin rana.

Shashasha, ai dama amarya tana zuwa zan sakar muku komai nima na huta amma baki isa ki miƙe ƙafa ki bar mata mijin ba, tashi kije kiyi sallah kan ki cika ni da kayan takaici.

Safara'u ta miƙe tana dariya kuma ko a jikinta, gani take yi in ya ƙara auren itama zata huta da wahalar aikin gidan.

***

Najwa.

Bayan sallar isha'i Mujaheed ya kirata akan yazo ƙofar gidansu, da sauri ta miƙe ta shiga ɗaki dan dama tana zaune a tsakar gida ne, ta saka hijab ta sanar da inna tayi baƙo, inna tace a dawo lafiya.
[5/15, 10:28 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

54.

Najwa tana fita ta ganshi a daidai setin gidansu a jikin mota ya tsaya yana kaɗa key, shigar ɗazun ce ta gani a jikinsa amma kuma da rantsastsiyar mota, ta saki wani murmushi dan ga dukkan alamu yanzu ne ta samu miji wanda take ganin yafi Aminu komai, kuɗi kyau da ƙuruciya gwanin birgewa, ta isa gareshi suka gaisa kana yayi mata tayin su shiga mota suyi hira, ba musu suka shiga ta zauna a gefensa, ƙamshin dake tashi a motar ma ba a magana wanda yasa Najwa lumshe ido ta buɗe, da alama wannan ɗan gaye ne tace a ranta, nan suka soma hira yana zabga mata ƙarya ita kuma tana gyaɗa kai tamkar mai haddar maganarsa. A lokacin ne baba ya dawo ya shiga gida yana mamakin ganin mota a ƙofar gidansa, ya zata baƙi suka yi dan motar tinted ce ga kuma duhun dare ba wutan nepa ba za'a gane da mutum a ciki ba, ya shiga yana cewa inna.

Motar waye na gani a ƙofar gida.?

Ɗazun nan Najwa ta fita ƙila kona baƙonta ne.

Amma ban ganta a wajen ba.

Ba mamaki ko suna cikin motar.

Ashsha! subhanallahi yaushe ta fara hira a mota? kinga Saleema ta ɓata tarbiyyar yarinyar nan ko.

Yace cike da faÉ—a ya fice waje, yana isa jikin motar ya kwankwasa sai Mujaheed ya sauke glass Najwa tayi saurin cewa.

Baba na ne.

Ke dan gidanku hira kike yi a mota maza ki fito nan Shashasha.

Najwa jiki na rawa ta fito baba ya nuna mata hanyar gida suf suf ta wuce, Mujaheed ya sunne kai yana bawa baba haƙuri baba yace.

Yaro ban yarda da hirar mota ba, domin in dai kai ɗan mutunci ne ba zaka so a yi hira da ƙanwarka a mota haka ba, dan haka daga yau karna ƙara ganin haka, kuma in da gaske kake yi ka fito bana son ka ɓata mata lokaci.

In Sha Allah baba zan gyara kuma da gaske nake da zarar mun fahimci juna zan yi mata magana na turo manyana.

To hakan yayi sai ka gaida gida.

Baba ya faɗa yana juyawa, Mujaheed har cikin ranta yaji daɗin yadda baba yayi masa, hakan ya bashi tabbacin gidan akwai tarbiyya, sai ya ƙara samun kwarin guiwa tare da ganin ya samu mata sai inda ƙarfinsa ya ƙare, sai ya ja mota cike da tsantsar farin ciki ya nufi gida.

Najwa kuwa tana shiga gida ta shige É—akin inna tana cewa.

Inna kinga Baba ya koro ni dan kawai ina hira a mota.

Yayi mini dai dai wlh ai kema kin san ya hana ki hira a motar saurayi.

To amma ai ba wani abin zanyi ba kuma wlh mutumin kirki ne shi.

Mutumin kirkin gidanku, kaga 'yar banza ana nima miki mutunci kina turewa, to daga yau inna ƙara ganin kin yi hira a mota zan baki mamaki, naga ma iskancinki gaba gaba yake yi, to zan saka ƙafar wando ɗaya dake.

Cewar baba da ya shigo ya tsinkayi maganar Najwa, sai tayi mukus ta ƙi cewa komai dan tasan halin baba ba wasa, inna ma ta ɗaura da nata faɗar baba ya wuce yana cewa.

Gwara dai ki mata faÉ—a taji, in ba haka ba ta saka tsiya na bada ita sadaka. Dan lamarin ta ya fara isata.

Sai ya shige ɗaki Najwa dai ƙunƙuni take yi a dole bata son faɗar, inna ma sai da ta gaji da faɗar dan kanta tayi shuru. Tun daga wannan ranar kusan kullun sai Mujaheed yazo hira amma yafi zuwa da yamma saboda a lokacin ne yake da damar fita da motar gidan da yake driver, Najwa kuwa ganinsa da mabanbanta motoci yasa ta ƙara dulmiyar da zuciyarta akan ƙaunar aurensa.

***

Bayan wata guda da sati biyu da haɗuwarsu Mujaheed ya turo manyansa aka yi maganar aure, wanda aka saka wata biyu mai zuwa. Musamman baba ya saka Junaid akan ya je ya bincika wanene Mujaheed domin kar a kuma yin aure irin na Aminu duk da shi wannan ya bayyana kansa, Junaid ya tambayi Mujaheed ranar daya zo hira sunan unguwarmu, bai musa ba ya faɗi sunan unguwar gidan da yake aiki bai kawo ko bincikensa zasu yi ba, a nan ne Junaid yaje unguwar ya yi bincike har ya gano asalin Mujaheed ɗan abakwa ne, da gidansu da komai sai da ya binciko nan ya gane duk zancen daya ji Najwa tana faɗawa inna cewar mai kuɗi ne ƙarya ne amma sai yayi muƙus bai faɗawa baba asalin bincikensa ba ya ce masa ya bincika mutumin kirki ne kuma yana da sana'a mai kyau, domin yana so Najwa ta aureshi ta hakane zata gane kurenta ta ragewa kanta dogon buri ƙila hakan zai sa ta gyara zuciyarta.
Chapter 91 · 0% Book details