← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 103

Sashe 58

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ƙare maganar yana yi mata jinjina da babban yatsarsa na hannu, sai da ta saki murmushi kana ta juya ta soma tafiya, har ta kusa shiga gida taji ya kira sunanta ta juyo sai ya lumshe mata ido ya buɗe yana sakin kayataccen murmushi, bata san sadda ta mayar masa da murmushin ba kana ya ja mota ya wuce ita kuma ta shiga gida. Sosai Ibrahim ya soma tasiri a zuciyarta, bata taɓa zaton zai kasance mai sauƙi har haka ba, lokaci guda ya yaye mata damuwar Aminu wanda hakan yasa ta shiga gida fuska sake, ko da su Umma suka ganta haka ba wanda ya tambayeta domin sun san dalili, haka ta kwana tana tuna Ibrahim da magnganunsa wanda In ta tuna Aminu sai ta ji ba wani ɓacin rai sosai da take ji kamar ɗazun, Ibrahim ya maye mata gurbin damuwarta, a karo na biyu tana jin sata sake bawa soyayya dama domin ta ƙara kwankwaɗar zaƙinta, dan ga dukkan alamu Ibrahim wayayye ne kuma ɗan zamani, wataƙila ma yafi Aminu iya wasu abubuwan, musamman fannin nuna soyayya a zahiri.

*****

Tum daga wannan ranar Ibrahim ya cigaba da kafa gwamnatinsa a zuciyar Sameeha, tun tana noƙewa har ta soma sakin jiki dashi suna hira, sai dai sunfi yin waya saboda baya zama, a hankali Sameeha ta yakice damuwar Aminu ta fuskanci gaskiya, kuma tun ranar daya kira bai kuma kiranta ba sai dai waya da take yi da yaranta, sannan ta zage sunata shirye shirye duk da ba wani shagali zasu yi ba saboda ita bata ƙaunar bidi'a Umma ma tace ba zasu yi komai dan albarkan aure take buƙata. Shamsu kuwa ya gama samun zuciyar Ikram, sosai yake samun damar zuwa hira kuma bata taɓa jin ta gaji da ganinsa ba dan ta kamu da sonsa na bazata, gabaɗaya ko wani ɓangare shiri suke na biki.

Itama Nabila tanata nata shirin saboda tunda taje gurin malamin da Shema'u ta rakata ya yanko mata maƙudan kuɗi tace ba zata iya ba, dan bata yarda tayi asarar kuɗi ba tunda ta samu labarin an gama maganar aure biki ya rage, a kan haka saida suka yi faɗa da Shema'u kan ta bata kunya a gun malam, daga baya ne suka shirya ta cigaba da sabgoginta, domin Ibrahim miliyan biyar ya tura mata akan ta ƙara jali sannan ya ce ta faɗi kuɗin da zata haɗawa kanta a kwati, tace miliyan shida shima bai musa ba ya bata dan a zauna lafiya tunda bata nima ɗaga masa hankali ba, hakan yasa taji aurensa ma bai wani dameta ba tunda ya bata wannan kuɗin, ita kuɗi sune rayuwarta bata yarda tana wasa da su ba, shiyasa sam bata bin malamai a ganinta asara zata yi, tunda gashi bata je gunsu niman sa'a ba amma tana samu kasuwanta yana bunƙasa.

Najwa kuwa danne duk baƙin cikinta tayi ta shiga jikinsu Sameeha dan ayi biki da ita taga duk abinda suke shiryawa, tun Ikram bata sake mata ba har ta mance komai suka cigaba da hidimarsu, duk da a gun Najwa na ciki na ciki.

*****

Biki saura kwana biyar.

A ranar ne aka kawo akwatin su Sameeha wanda set bibbiyu ne, set na farko guda biyar da kit, na biyu kuma uku da kit, babu bambanci a kayan da aka zuba sai zinarin Sameeha da yafi na Ikram tsada, da kuma key motarta da aka saka yafi na Ikram ɗin, gida ya cika da 'yan uwa ana kallon kayan arziki bayan dan ginsu ango sun tafi, Khairy dai tana nan maƙale da Sameeha dan kusan tafi zuwa gidan akan can gidansu. Najwa kamar zata haɗiye rai dan baƙin ciki, jikinta har wani ɗumi ya ɗauka ta kasa tsayuwa sai ta zauna tana kallo yadda ake ɗaga kayan arziki, Inna Rakiya kanwar Umma tace.

Ni wlh nama kasa magana da ganin waɗannan kaya, ina ganin mijin Sameeha yafi na Ikram kuɗi dan wlh sarƙar zinarinta tafi tsada nesa ba kusa ba, ga motar ma sun faɗa. Wai yaya wani miji ne Sameeha ta samu haka? Kunga fa manyan leshi da atamfa da iya ganinka baka san ya zaka daɗi kuɗinsu ba, jama'a ban taɓa ganin akwati haka ba wlh tunda nazo duniya, ko aurenta na farko wane da wannan kaya.

Nan fa kowa ya shiga faÉ—ar albarkacin bakinsa ana ta yaba kaya, umma dai dariya take ta yi ta kasa rufe baki, innar Najwa tace.

Wannan yara ai sunyi goshi suna da ƙashin arziki Allah ya basu, ita Sameeha ta bar gidan kuɗi ta ƙara faɗawa gidan daya fi na baya ma, dan ganin kayan nan ya nuna babban mai arziki ta samu, Ita kuma Ikram ta faɗa gidan sarauta wanda ko a mafarki bamu taɓa zaton haɗa jibi da mulki ba. Kai Alhamdulillahi haihuwa tayi mana rana, ina ma ace yaya yana raye yaga wannan ranar farin ciki haka, Allah ya jikanka yaya Amadu, bayanka tayi kyau wlh.

Ta ƙare maganar tana matsar kukan farin ciki, haka dai kowa yake faɗar albarkacin bakinsa, Najwa kuma tana ƙara shiga tashin hankali na baƙin ciki kamar ta haɗiye rai ta mutu, bata iya jurewa ba ta miƙe ta fice ba tare da an kula da ita ba, ta tari napep ya wuce da ita tana matsar kwalla dan sosai taji baƙin ciki da ƙunci ganin akwatinan su Ikram, bata taɓa zaton zasu kai haka ba, yanzu ne take ƙara raina kanta dan tabbas darajar raƙumi yayi nesa da ƙasa, sun yi mata fincinkau a komai, dan tasan wlh Aminu bai da kuɗin da zai yi mata irin wannan kayan, saboda a cikin arzikinsa da zuciyarta take hasashe bai kama ƙafar mazajen su Sameeha ba, ji take kamar tsiya da talauci a kanta a ka ƙare, sam bata taɓa samun saurayi mai mugun kuɗi ba sai dai 'yan kuci ku bani, ita dai tana ganin kyanta bai amfaneta da komai dan da kyau zai jawo mata arziki da sai ta auri mijin daya taka na su Ikram, amma sai gashi ta ɓige da auren mijin da Sameeha ta bari bisa cin amana, wanda ma bata da yaƙinin zaman auren zai yi mata daɗi, haka ta dinga share hawaye tamkar wacce aka yiwa mutuwa.

*Duk wacce ta karanta mini littafi bata biya ba, ta sani ta karanta da hakkina kuma In Sha Allah sai Allah ya saka mini.*
[4/19, 6:46 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

36.

Najwa gidansu Nafeesa ta wuce, ko da ta isa ta samu suna shirin zuwa dinner É—in wata 'yar kanwar Hajiyarsu, amma a yadda Nafeesan ta ganta yasa ta jata É—akinta suka zauna gefen gado tana dafa kafadar Najwa.

Meke faruwa ƙawata? Na ganki a hargitse ne kamar kin gamu da abin furgici.

Su Sameeha sun fini komai Nafeesa banda abinda zan yi gogayya dasu domin duk mazajansu sunfi Amunu da komai, akwatinansu abin kallo ne wanda ya gigita lissafina da tunanina nasan ni ban zo duniya a sa'a ba, komai nice ƙarshen baya ina ganin har na mutu bazan taka matsayin da nake buri ba a rayuwata ba.

Nan ta kwashe labarin akwati ta faɗa mata komai da idonta suka gani, tana faɗi tana kuka hawaye shaɓe shaɓe. Sai da takai aya kafin Nafeesa ta ja numfashi ta sauke a hankali tana cewa.

To sai me dan anyi musu kaya haka? Dama dole ki saka a ranki zasu samu haka domin kuÉ—in sadakinsu kawai ya nuna akwatinsu zai zo da kaya irin wannan, bana so kina saka damuwar su fiki kowa fa da arzikinsa, ina ce kema kin samu cikar burinki na auren Aminu, wanda shima ba talaka bane yana da kuÉ—i sosai, na tabbatar hatta motar hawa zaki samu a gidansa, kuma dama babu yadda za ayi kice komai daidai zaki samu dasu Sameeha domin yatsun nannunmu ma ba É—aya bane, dan haka ki cire komai a ranki tunda kema ba talakan zaki aura ba.

Amma Nafeesa duk yadda naso ba haka nake samu ba, bana so ko kaɗan su fini jin daɗi a gidan miji, burina kafin aga wani abu mai kyau da tsada a hannun 'yan danginmu an fara gani a hannuna, a kullun burina na kasance sama da kowa, sai dai burina ba zai cika ba tunda su Sameeha sun zama zakaran gwajin dafi, akomai suke fara tare mini hanya su rigani isa kafin na kai. Ni bikin ma bazan sake zuwa ba suyi kayansu dan kar baƙin ciki ya kashe ni a banza.

.

Aiko baki isa kice ba zaki je ba, in ba haka ba da wuri zasu gano kina musu hassada, gwara ki shiga a dama dake ta yadda zaki yi ƙoƙarin ganin abubuwa kema ki tsara aurenki da yadda zaki zauna a gidanki yafi nasu, idan fa kina so ki fisu to dole sai kin riƙa binsu kina shige musu tare da sanin duk halin da suke ciki, ta hakane zaki gina naki rayuwar yadda kike muradi, dan haka nima zan shiga bikin a dama dani dan na riƙa ƙara miki karfin guiwa, bana so ki sare akan cikar burinki.

Allah ko Nafeesa? kina ganin hakan za mu yi?

Sosai ma kuwa, yanzu ma tashi zaki yi ki wanke fuska na ara miki kayana ki raka ni dinner É—in 'yar uwarmu kiga yadda ake shagalin masu kuÉ—i, shima wani darasin zaki É—auka.
Chapter 58 · 0% Book details