Sashe 69
Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hmmm daga baya kenan, kuma saki uku nayi miki ko ke mahaukaciya ce baki tantance saki.
Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, a cikin fushi kayi dan son Manzon Allah da darajar Umma ka mayar dani ɗakina, saki uku cikin fushi saki ɗaya ne, Basiru nice fa Adamarka karka mance soyayya da ƙauna.
Ina cikin hankali nayi wlh sarai nasan me nake yi, saki uku nayi kuma babu zancen gyara ki tattara ki bar mini gidana tun kafin inyi miki watsi dasu, 'yar iska mara tarbiyya sai yanzu nasan na yiwa kaina zaɓen tumin dare nabi hasken fata.
Yana gama faɗar haka ya fice fuuu kamar guguwa, Adama ihun kuka ta fashe dashi tana ambaton ta shiga uku ta lalace, ga wajen idonta daya kumbura mata da duka har idon ya tara jini, ta miƙe ta zauna gefen gadonta ta shiga tuna rayuwarsu ta baya tasan Basiru yayi haƙuri da ita saboda ta jima tana bashi matsala, duk kuwa da tutiyarta asirin mallaka da tayi masa shiyasa take samun galaba akansa baya yi mata wani hukunci, yau kam tasan kadarinta ya karye ta kashe aurenta da kanta a dalilin auren kawunta Aminu, bata san ya zata yi da wannan ƙunshin baƙin ciki data haɗawa kanta ba, tana kallon wayarta tana ringing amma ta kasa zuwa ta ɗauka wanda tasan bai wuce maman ta ne ke kira, haka ta cigaba da kuka tana tunanin yadda makomar rayuwar zai ƙare in ta koma gidansu zawarci, ta ina zata fara? Yadda tasan halin mamanta sai a hankali tasan dole zasu riƙa kai ruwa rana musamman a gurin abinci, yaranta guda uku ta duba kiri kiri yanzu ba zasu tashi a gabanta ba, na goyen ne ya rarrafo yazo ya dafata ya miƙe yana gwalan gwalan biyun sun tafi makaranta, ɗaukanshi tayi ta goya a baya dan dama ta gama shirya shi kenan suka fara rikici da mijinta, kaico da dana sani ne ya cikata tana cizon yatsa, musamman in ta tuna irin kulawar da mijin ke bata, bata rasa ci da sha ba balle sutura dai dai gwargwado yana sauke hakkinsa na miji akanta, tana kuka ta saka hijab ta ɗauki jakar kayanta data haɗa na cin biki da kuma ƙaramar jakar gayu da takalmi da ta saya sabo na biki ta rataya ta fito ta rufe ɗakin ta ratsa matan gidansu da suke jiran fitowarta suna gulma, suna ganinta suka yi gum sai kallonta suke kamar sun samu madubi, to me ya rage mata da zata ɓoye, sakinta dai aka yi kuma ba kome, hawayen dake zuba bai fasa fita ba haka ta ratsa ta wuce, tana saka ƙafarta a waje yaji yo shewarsu dan dama gidan an haɗa makirai, shiyasa bata shiri dasu sosai saboda saka ido da gulmarsu, baƙin ciki goma da ashirin ga abin faɗa amma ba halin tayar da kwanji, dole ta wuce jiki a sanyaye ta isa titi ta samu abin hawa ya wuce da ita gidansu.
Data isa gida kayanta ta aje ta fito zuwa babban gida lokacin anata ƙoƙarin tafiya masallacin juma'a, tana shiga ta tadda mata da yawa a tsakar gida ana ta hada faten tsaki a ƙatuwar tukunya, ganin basu ganta ba sunata hira yasa ta ratsesu ta nufi can ɓangaren Laure tasan Mamanta tana can, tana isa kuwa ta same su sun baje a tabarma sunata shan rake ana hira, Adama ganin Hauwa yasa ta saki kuka dan sosai kukan yazo ta kasa danne shi, Hauwa ta miƙe da sauri tana faɗin lafiya ina sauran yaran? Mutanen da suke gurin suma tambayar lafiyar suka yi kowa ya baza kunne, Hauwa ta isa gurin adana ta tsaya sai Adamar ta faɗa jikinta tana.
Mama Basiru ya sakeni.
Da sauri Hauwa ta toshe mata baki tana wato ido waje dan tayi matuƙar kaɗuwa da sakin, kuma bai dace mutanen da ke gurin kowa ya ji ba, qi kamar ta tona musu asiri ne maƙiya suyi dariya, sai ta jayeta daga jikinta ta kama hannunta suka wuce ɗakin Laure, matan dake gurin wannan da kallon wannan ana gulma da ido, sunƙi magana saboda tsoron rashin mutuncin Hauwa. Da suka gisha ciki har sai da suka dangana da bedroom ɗin Laure wacce suka samu ta gama shiri zata fito dan wanka tayi, ganin Adama tana kuka ta tsaya turus tana kallonsu har suka ƙaraso ciki, Hauwa cike da tashin hankali tace.
Me kika yi masa ya sakeki, Adama kin tona mini asiri ina cikin tsaka da farin cikin bikin Aminu zaki zo mini da labarin daya hautsina mini hanjin cikina, Allah yasa saki É—aya yayi miki akau kome, dan wlh bazan jure ganinki a bazawara ba a gidana, ai ABIN DA CIWO.
Adama ta ƙara rushewa da sabon kuka ta shiga cewa.
Akan zanzo biki tun jiya ya hana ni, yau nace masa zanzo ya tubure dole sai gobe na koma jibi, shine rikici ya ɓarke a tsakaninmu daga bisani ya rufeni da duka yana zagina nima ina ramawa, shine daga ƙarshe yace ya sakeni saki uku.
Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, na shiga uku ni Hauwa ina zan saka kaina da wannan ƙunshin baƙin cikin Adama, meyasa zaki biyeshi ki jawo ya sake ki har uku? da kin kirani ko kin ɗauki wayata da naketa kira da zance ki haƙura goben kya zo, yanzu dan ubanki ina kike so zan tsoma zuciyata tayi mini sanyi. Ashe haka saki yake da zafi? ashe ABIN DA CIWO har haka, Laure kinji tashin hankalin da yarinyar nan ta jawo mini ina tsaka da farin ciki.
Sai muryan Hauwa sirƙe tayi baya zata faɗi dan sosai jikinta yayi sanyi taji kamar an cire mata lakka, Laure tayi saurin riƙeta ta zaunar a gefen gado tana cewa.
Dan Allah kibi komai a hankali Hauwa In Sha Allah komai zaiyi dai dai, karki jawowa kanki wani ciwon yanzu maƙiya suyi mana dariya. Ke kuma Adama baki kyauta mana ba meyasa zaki biye shi? ai in Namiji ya kafe akan abu haƙura ake abarshi dan in kika matsa sai naki ran ya ɓaci, gashi nan kin jawo mana abin magana, Allah ya kyauta.
Ta ƙare maganar tana jan dogon tsaki, Hauwa ta fashe da kuka dan shine kawai zata yi taji sauƙin baƙin cikin daya turniƙeta, Adama ma kukan ta cigaba da yi Laure kuma tana tausarsu. Duk yadda Hauwa take burin in an kammala fate zata sha sai gashi ta kasa ko da loma ɗaya ne, Adama ma ta kasa cin komai Laure ce ta ɗan tsakura dan ta gusar da yunwa, itama abin ya dameta dan duk abinda ya samu Hauwa tamkar ita ya sama saboda shaƙuwarsu, haka suka yini a ɗakin Laure sun kasa fita har aka kira sallar magrib, zuwa lokacin labarin sakin Adama ya shiga cikin gidan sai gulma ake yi, su Sa'a da salma har ɗaki suka samesu suka jimanta, dan abin bai yi musu daɗi ba ko kaɗan, haka su yaya Alhasan da Kamalu sam basu ji daɗin lamarin ba, Aminu ma daya samu labari lokacin daya zo sosai abin bai yi masa daɗi ba, haka suka taru suka dinga lallashin Hauwa akan tayi haƙuri ta sake ayi biki bayan komai ya lafa zasu bi zancen, in da yuwuwar gyara sai a gyara auren, dole yasa ta saki ɗin duk da na ciki yana ciki.
****
Gidansu Najwa.
Ya cika da mutane ana ta gyaran kayan abincin gobe ɗaurin aure in Allah ya kaimu, itama tanata nata hidimar dan sosai take shirin zuwa gidan miji, Nafisa kuwa ita ce amara ƙirjin biki dan komai ita ta tsara sai sauran ƙawayensu na biki, Binafa sun so zuwa amman saboda kar Sameeha ta gansu yasa suka bari sai bayan biki suje suga ɗaki ita da ƙawarta Hanan. Kowa ka gani yana cikin farin cikin bikin, umma ce takewa Inna maganar kai kayan amarya tace.
Zulai ya batun kayan É—akin Najwa ko an kaine? naga baki yi maganar ba.
Wlh in gaya miki 'yan uwan ango suka sama mana sauƙi, tun saura kwana biyar suka turo da mota akan a kwashe kaya su zasu gyara mata ɗaki, mantawa nayi ban faɗa miki amma tuni aka yi gyaran ɗakinta, kaita ne ya rage.
Amma kuwa sun sama mana sauƙi sun kyauta, da haka ake dangin miji aiko da ko wace mace ta dace, lallai Najwa tayi dace da dangin miji sai dai fatan zaman lafiya ya kauda sharrin shaiɗan a ciki.
Inna ta amsa da amin tare da sauran matan da suke gurin, haka suka cigaba da hirar suna yabon dangin da Najwa zata shiga.
Washe gari.
Da wuri su Sameeha suka shirya suka tafi gidansu Najwa dan basu tsaya jiran umma ta dawo ba balle su zo tare, duk da ba haka Ikram taso ba Sameeha ce ta matsa su tafi da wuri, a motarta suka wuce tare da yara da Anwar. Suna isa É—akin Inna suka fara shiga suka gaisheta tare da Allah ya sanya alkhairi, kafin daga bisani suka fito suka samu su Umma a tsakar gida suka gaishesu sannan suka saka musu hannu wajen gyaran alayyahun miyar tuwon shinkafa, yara kuma suka haÉ—u da sauran yara suka soma wasansu, Anwar kuma ya fita waje saboda shi da girmansa. Najwa koda tagansu É—auke kai tayi zata wuce Sameeha ta ce cikin zolaye.
Najwa Amarya ba magana ne ya shirye shirye, gaskiya me kwalliyar nan ta fito dake da kyau, bari nazo na ɗaukeki hotuna kuma muyi tare kafin mu ɓata namu kwalliyar.
Au Sameeha ashe kun zo ya gida.
Ai sai Ikram da Sameeha suka kalli juna yadda ta iya kiran sunanta ba anty gatsar cike da rashin kunya, Sameeha jiki a sanyaye ta amsa da lafiya kafin ma ta kuma magana Najwa tayi gaba, Ikram cike da takaici tace ƙasa ƙasa.
Ai gashi ta nuna miki ita din mara mutunci ne, meyasa ma kika kula ta, wlh Anty Sameeha na rasa wani irin zuciya ce dake.
Ki rufe mini baki bana son maganar.