← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 103

Sashe 78

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yayar banza yayar wofi muguwa azzaluma shaiɗaiya, idan sunan Sameeha bai fita daga bakinki ba wlh sai ba kasheki in yaso nima a kasheni. Kin tarwatsa mini farin ciki na da ni da iyalina, Hauwa kin zame mini matsala a rayuwata. Kece kika saka na rasa lafiyata wanda ya jawo dalilin dana rabu da mata ta, tun lokacin da kika kirani kika fana mini rasuwar Umma nayi accident a lokacin na rasa mazantakata na rasa lafiyar da zan kusanci matata, tsawon shekara shida Sameeha tayi dani tana haƙuri ba tare dana sauke hakkin aurenta ba, bayan mun dawo Kaduna kika matsa mata kika dinga yi mata bita da ƙulli duk saboda son zuciyarki bayan Sameeha ni take rufawa asiri take zaune dani nakassashe, ban faɗa muku ba ta hana ma na sanar da kowa, bayan na saketa kika nuna kinfi kowa murna kika je kika ci musu mutunci kika kwaso yara, kika dage akan sai nayi aure na amsa miki domin na nuna miki kinyi kuskure dan nasan ni ba mai lafiya bace, babu macen da zata zauna dani a haka, amma saboda ki muzgunawa Sameeha kika haɗa baki da 'yar uwarta Najwa kika fitar da Sameeha a gidanta sannan kika aura mini Najwa dan kwai ki kai Sameeha ƙasa saboda kin tsaneta, to ni kika tsana ba ita ba, nine baki so nine kikewa hassada da baƙin ciki Hauwa, to Albishirinki zan bar miki duniyar kici abinda zaki ci a ciki, kuma na saki Najwa domin bazan yarda na zauna da ita a matsayin auren cin amana ba, babban farin cikin da nake ji inna tuna an saki Adama 'yarki saki uku lokaci ɗaya kamar yadda na saki Sameeha, Allah ya nuna miki cewar shi ba azzalumin bawansa bane sai dai bawa ya zalunci kansa, kuma alhaki kuikuiyo ne gashi ya biki, ita kuwa Sameeha ta samu mijin daya fini, 'yan uwan da suka fiku inda ake yi musu so domin Allah, tana cikin farin ciki da ahalinta Allah bai bari sun wulaƙanta ba ya ɗagasu ya ɗaukaka daraja su wanda sai dai gani sai hange, wannan izina ce a gareki dama duk mai irin halinki kuma ki saka a ranki ɗan uwanki Aminu ya mutu wannan da yake a gabanki wani ne sabo bai sanki ba, ban san daga ina kike ba, Allah ya isa tsakanina dake.

Ya ƙare maganar yana nuna ta da tsaya duk ya haɗa guimi saboda masifar da yayi, Hauwa kuka kawai take yi cike da tsantsar bakin cikin abinda Aminu yayi mata, ya wulaƙantata a gaban dangi, ya tona mata asirin mutuwar auren 'yarta da suke ta rufa rufa yanzu kowa yasan saki uku aka yi mata wanda a dalilin aurensa ne aka sakeleta. Mutane kam jugum jugum suka yi suna jin abin mamaki, musamman da Aminu ya faɗi rashin lafiyarsa, sunyi matuƙar tausaya masa, waɗanda basu san halin Hauwa ba yau sun sani sai um um da baki suke yi kowa yana tsoron furta nashi sanin halinta ta balbalesu da faɗa, duk da Aminu ma yayi mata hukunci harda fasa baki. Yaya Kamalu da Alhasan sun fito suma sunji komai da kunnensu, ba ƙaramin mamaki kalaman Aminu ya basu ba musamman na rashin lafiyarsa da kuma Najwa 'yar uwar Sameeha ce, basu ga laifin dukan Hauwa da yayi ba dan ita taja ta kuma zubar da girmanta, Aminu ya juya a fusace zai fita Alhasan ya kira sunansa sai ya juya, Aminu ya fashe da kuka ya isa gurinsa ya ɗaura kansa a kafaɗar Alhasan shi kuma yana dukan bayansa akan yayi hakuri, Aminu ya ɗago yana nuna musu Hauwa.

Kunganta ita ce gabaɗaya ta rusa mini rayuwata, duk da na yarda da ƙaddara amma itace sila.

Yana gama faɗar haka ya juya ya fice daga gidan yana share hawayensa, su Alhasan basu hanashi ba domin yana buƙatar kaɗaici, kallon Hauwa suke yi zaune a ƙasa sai suka danƙara mata mugun kallo kana Alhasan yayi waje Kamalu ma yabi bayansa, koda suka fita sai dai suka tadda kurar motar Aminu dan tuni yayi gaba abinsa, nan suka zauna ƙofar gida suna mayar da magana dan sosai suma suka ji kamar su rufe Hauwa da duka, suma banda a tsaye suke da haka zata tasa rayuwarsu a gaba dan Hauwa tana da mugun sa ido da shiga harkan da ba nata ba. Hauwa kuwa miƙewa tayi jiki a sanyaye ta wuce sashin Laure duk abin duniya ya dameta, domin wulaƙantata da Aminu yayi a bainan nasi ya tsaya mata a rai matuƙa, ga kuma tona sakin da aka yiwa 'yarta, ji tayi idan bata rama abinda yayi mata ba bata haifu ba, sai ta saka rayuwarsa a uku masifa ta yadda sai yazo akan guiwarta yana bata haƙurin abinda ya aikata mata, dan wlh idan zata ja duwawu ne sai ta lalata dukiyarsa dama duk wani abu daya ke taƙamata dashi, girgiza kai kawai take yi tana cizon leɓenta da ƙan8ance idanunta, tana jin su Laure suna bata haƙuri amma bata su take ba dan alwashin sai Aminu ya wulaƙanta take a zuciyarta.

******

Najwa.

Suna shiga gida ta wuce É—akinta tana kuka, Junaid ya shiga É—akinsa shima ya ciro belt É—insa ya sameta a É—akin ya shiga dukanta yana cewa.

Wlh idan ban dukeki ba bazan huce takaicin baƙin ciki da kika ƙunsa mana ba, kinci mutuncin gidanmu kin ɓata manq sunanmu, shegiya mai mugun hali Allah ya wadaranki Najwa.

Yaya ka kashe! nima na huta na tsani komai bana son wannan rayuwar ka kashe!

Najwa tana faÉ—a cikin gunjin kuka tana kuma sosa jikinta da dukan da yake yi mata, sauran 'yan biki ne suka shigo É—akin suka ceci Najwa, Salima ta wanke Junaid da mari tana zaginsa.

Dan ubanka kasheta zaka yi, ka bari muji da abu É—aya mana, ace jiya jiya aka É—aura aure an sakota kazo kuma zana dukanta da wannan zata ji.

Junaid ƙofa yayi ya fice abinsa ransa a matuƙar ɓace, Salima tabiyo bayansa ta tsaya a tsakar gida.

Wlh babu wanda ya isa ya ƙara dukanta idan baku sonta ni ina sonta, haka kawai da wanne zata ji? Ai kowa ma yana kuskure sai ayi mata uzuri, dan haka yau ɗin nan zan tafi da ita kano ta cigaba da zama a guna ba zaku ƙara ganinta ba sai kun nimeta.

Da kin kyauta kuwa Salima, kinga kin sauƙaƙa mana baƙin cikin da ta ƙunsa mana bamu ganta ba balle mu riƙa tuna abinda ta aikata, sannan ma kin rage mana zagin mutanen unguwa, in dai Najwa ce na yafe miki ita ba kano ba ki wuce kano da, ita ai dama ba a ɗaya a dangi, na tabbatar idan Najwa tayi gadon mugun hali to kuwa a gunki ta gado shi, dan kema babu irin surutun da baki saka iyayenmu ba har suka bar duniya da tabonki.

Dama ai da abu ya taso saika goranta mini kuma su Mama basu bar duniya ba saida suka yafe mini komai, aure ne dai naƙi zamansa kuma yanzu Allah ya shieyeni ina zaune a gidan aure har da yara, abu ya wuce amma kullun sai ka dawo da magana baya, ni ba cikin shege nayi ba ko wani mugun abu, aure ne dai naƙi zamansa nayi har guda Huɗu, a na biyar ne na zauna kuma bazan zauna namiji yana cuta mini ba, ko yanzu baban su Lukuman ya yi mini iskanci zan cikawa wandona iska bazan zauna ba wlh.

Allah ya kyauta. Dan haka ni na sallami kowa biki ta watse kowa ya zo ya kama gabansa tunda me auren ma an sakota saboda mugun halinta.

Baba ya kuma faɗa ya fice daga gidan, nan fa sauran 'yan uwa kowa ya fara haɗa kaya, inna kuwa tunda ta kwanta a gado ta rufe ido bata motsa ba kuma bata son yin magana, tana jin abinda ya wakata da baba da Saleema saida tayi murmushin takaici dan kuwa baba Gaskiya ya faɗa Najwa halinta ta ɗauko dama ba a ɗaya a dangi, ga shegen son duniya da rayuwar ƙarya, haka ta gama zaga gidajen aure huɗu wanda kowa yasan arzikinsu take bi in taga bata samu yadda take so tasa miji ya saketa dole, wannan ne kawai ta zauna dan shima malami ne wataƙila wajen niman asiri ya ganta ya kuma maƙale mata saida ya aureta, daga bisani ma ya kafeta ya mallaketa shiyasa ta kasa kwakkwaran motsi a gidan dan mugun tsoronsa ma take ji, inna taji daɗin ma ta tafi da Najwa wataƙila malamin zai koya mata hankali ita ma ta dawo hayyacinta, dan zata saka baba ya kirashi ya faɗa masa komai ta yadda Najwa sai ta so dawowa nan kuma ba halin haka, sannan ya aurata mata duk wanda ya gadama zata so hakan ya faru.
[5/6, 7:57 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

47.
Chapter 78 · 0% Book details