← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 103

Sashe 3

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna fita tsakar gida suka sanar da 'yan uwa cewar zasu tattara su koma family house É—insu dake unguwar dosa, sai su cigaba da hidimarsu saboda dama jiran dawowarsu suke yi su koma can, suka saka aka yi shara ciki da waje aka yi mofin kitchen da falo gida ya dawo hayyacinsa duk da ba wani gyara ya samu mai kyau ba, suka kwashe murhu da tukunya suka saka a baron da aka É—auko shi dan daga can babban gida suka É—auko, saboda Umma ta siya musu tukwane da kuloli saboda sha'ani, Laure takan ba da hayarsu a bata kudi, kuma ba wanda ya hanata dan saboda gadara da take a gidan kuma ba umma balle Abba a raye, haka suka tattara da yara suka wuce ba tare da sun yi musu sallama ba, da yake ba wani nisa sosai a tsakaninsu wasu a kafa suka tafi babban gida, wasu kuma suka tari napep ya karasa da su, Laure da Hauwa sune karshen tafiya suka jera a kasa suna yi suna surutu cike da takaicin abinda su Alhasan suka yi musu, Hauwa ta mele baki tana cewa.

Ni Sameeha tafi bani haushi, ai da taso karemu lokacin da yaya Alhasan ya fara magana sai tayi kokari ta tare shi, amma sai da suka kare mata cin mutunci kafin ta iya saka baki.

Ni kin san miye ma? na kula da shi tunda suka shigo wani gani gani take mana da kallon raini ita matar Alhaji, wlh yarinyar nan nan gaba Allah kaÉ—ai yasan iskanci da wulakancin da zata yi mana, dan haka ni zan kama kaina dan bazan bari raini ya shiga tsakaninmu ba.

Haba Yaya Laure wane ita? ai uban kuturu yai kaÉ—an, kuma bata isa ta hana mu zuwa gidan É—an uwanmu ba dan a sama ta same shi wlh, in kuma ta kawo mana wargi sai nayi sanadin da tabar gidan mu aura masa wacce muke so.

Allah yasa Aminu kar ya baku kunya dan naga yana mutuwar son Sameeha kamar ta gama da shi.

To na nawa kuma, ko kin mance mahaifin mamanta malami ne ai tuni aka kafe sunan Aminullahi a allon ƙarfe, sai yadda tayi da shi dan an wanke an bashi ya sha.

To Allah ya kyauta amma in tasan wata ai bata san wata ba mu zuba mu da ita.

Yauwa yanzu naji batu ai sai dai muga bayanta ba dai mu taga karshenmu ba, wlh yadda na tsani mutuwata haka na tsani ganin Sameeha a gidan Aminu tunda ta nuna mu bamu isa da ita ba. Amma gobe In Sha Allah zan dawo gidan na ja mata layi dan nan ba Lagos bane, mun dawo kusa da juna komai da zata yi yana kan idonmu.

Hmmm har kin tuna mini da batun yar aikin da kika ce na samo, jiya agent É—in ta kira ni ta sanar dani an samu.

Yauwa yaya Laure zamu je kuwa tare, dan mu ga yarinyar kuma mu ɗaurata a hanyar yadda muke so,  kinga kenan zamu rika jin labarin duk abinda ke faruwa a gidan.

Cewar Hauwa tana wani sha'umin murmushi, sosai suka cigaba da fito da hassadarsu akan Sameeha, bayan in an tsaresu ba su da wani hujja da zasu faÉ—a laifin da Sameeha ta yi musu, kawai daibbakin ciki daular da take ciki suke yi kuma sun kasa juyata kamar yadda suka so.

***

Sameeha.

Sai da ta tabbatar da sun fita kafin ta fito falon ita da yara, sai ta fita tsakar gida taga sun gyara gidan amma akwai sauran inda ya dace a share sannan akwai inda ya kamata a saka ruwa a wanke, ba zata iya wannan aikin a ranar ba sai dai ta bari zuwa gobe in Allah ya kaimu tayi. Babban gida ne da aka zuba masa kudi aka kerashi yadda ake son ya kasance, falo biyu ne a gidan falon farko shine na Sameeha da ɗakuna guda gudu, ɗaya na ta ɗaya na Abi ɗaya kuma na Amrah, sai guda ɗaya extra saboda baƙi, sai katon kitchen da store a ciki an zuba komai na buƙata sannan akwai bayi ɗaya a falon duk da a ko wani ɗaki da bayin, sai falon Aminu da yake madaidaici da ɗakuna biyu, ɗaya bedroom ɗinsa ɗaya kuma ya aje muhimman takardunsa wato study room da kuma kayan motsa jikinsa, an zuba komai dai na buƙata. Sannan can bayan gida akwai BQ guda biyu da bayi da kitchen sannan akwai bishiyoyin mangoro da gwaiba har da gwanda da lemu, yar karamar garden dai da rumfar shan iska da kujeru, sai parking space a nan farfajiya an ajera mota uku a ciki, ɗaya na Aminu ɗaya na Sameeha hotuwar nashi da yake hawa ya bar mata sai ya saya sabo, sai na ɗaya na kai yara makaranta, ga kuma ɗakin me gadi a bakin gate komai dai gwanin sha'awa. Sameeha da ta koma falo sai ta aika Abi ya amso key ɗin ɗakunansu dan duk suna rufe, kuma key yana hannun yaya Alhasan sai da suka zo ne ya bawa Aminu su, da ace su Hauwa sun samu key ɗin da fa sun gama ganin sirrin gidan da komai yadda zasu ji daɗin karaswa, tana tsaye sai ga Aminu ya fito daga falonsa tare da Abi, da murmushi ta kalle shi tana cewa.

Allah yasa bamu tasheka a barci ba.

A'a idona biyu tunda na shiga nake amsa waya kin san harkan aikinmu ba hutu, amma gaskiya gidan nan sai kin kira su Ikram sun zo sun tayaki gyara dan sam bai gyaru yadda ya kamata ba.

Eh dama na bari gobe In Allah ya kaimu sai nayi aikin yanzu me zan É—aura maka kaci, dan mu muna da abincin tarba da ummanmu ta yi mana, kasan can zamu kwana.

Eh da yake ni ba ɗan umma bane dole a ware ni, to nima dani zaku tafi in cika cikina a can in yaso sai na wuce can babban gida in kara gaisawa dasu Yaya, ƙila ma na kwana can.

Abban Amrah na isa nace kai ba É—an umma bane, kawai banyi maka tayin zuwa ba ne dan baka ce zaka ba.

To yanzu nace zani Madam Meeha matar Aminun Alhaji Ado.

Sai ta kwashe da dariya yaran suna taya ta shima dariya yayi sai ya wuce ya buɗe ɗakinta suka shiga suna wow wow kamar motar asibiti, an zuba funitures masu tsanani kyau da burgewa wanda suka yi oder daga company MG Furnitures wanda show room ɗinsu yake Freetime house kusa da asibitin giwa kan titin Ali Akilu. Zaku iya tuntuɓarmu a nan 09034940106 domin karin bayani akan ko wani irin kaya da kuke muradi.

Bayan sun gama ganin ɗakin Sameeha haka suka fito suka shiga ganin ɗakunan dake falon har zuwa kitchen komai yaji an zuba kuɗi kuma buƙata ta biya, bayan sun shiga store ne suka tadda an buɗe buhun shinkafa ɗaya an ɗiba, ga kuma mai dake galam da aka diba shima, Aminu ya buɗe freeza da aka zuba musu kaji ɗanye gyararru da ganda da kifi. Ya ƙirga kajin yaga guda takwas madadin guda goma sha biyar da yaya Kamali ya faɗa masa an zuba a ciki, ya juyo fuskarsa cike da ɓacin rai.

Amma wlh Hauwa da Laure sun wuce gona da iri, na tabbatar sune suka yi wannan aikin, ashe abincin da suka dafa namu suka ɗiba, na ɗauka taya murnan nasu da gaske ne da suka cika mana gida suka ɓata, gaskiya dole na taka musu burki dan bazan jure wannan cin kashin ba.

Haba Aminu in rai ya ɓaci hankali ke nimoshi, 'yan uwanka ne fa suka ci abincin nan, arziki ne ma ayi maka irin haka, idan ba suna ganin kai nasu ba ne taya zasu yi haka, ni dan Allah karka yi musu magana faɗar da su Yaya Kamalu suka yi musu ya isa kar kazo kayi magana su mayar da abin wani iri.

To amma fisabilillahi ba zasu iya faɗa mini za suyi abu ba sai dai kawai mu dqywo mu tadda gida kaca kaca, ashe ma abincin gidan suka ɗiba suka yi wannan wandaƙar, duk lemuka da ruwan dana siya mana wanda zamu jima muna amfani dasu shi suka kwashe suka shanye, wannan ai haukane da mugunta..

Kayi hakuri dan Allah kuma kayi musu uzuri na tabbatar ba zasu sake yin haka, Abi da Amrah kuje ku É—auko hula da hijab da jakata mu wuce gidan umma.

Ta kare maganar akan yaransu, sai suka fice da sauri ita kuma ta mayar da kallonta gurin mijinta.

Dan Allah Abba Amra komai ya wuce kuma bai dace kana irin wannan maganar a gaban yaran nan ba hakan ba tarbiyyarmu bace.

Wlh raina ne ya ɓaci amma zan kiyaye, mu je gidan Umma dan naga la'asar ta kawo jiki.

To tace masa sai suka fito, yaje inda motarsa take ya cire mata riga ya budte ya shiga ciki ya kunna ya kawota tsakar gidan, suka shiga gabaÉ—aya mai gadi ya buÉ—e musu gate suka fice.

Ummu Sultan da Samha ce.
[1/28, 4:03 PM] Rahma Kabir: *ABIN DA CIWO*

Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 3.

Gidan Umma.

Suna isa rafin guza Aminu yayi parking a ƙofar gidansu Umma suka fito ya rufe mota suka ɗunguma cikin gidan da sallama, da gudu kanwarta Ikram ta fito ta zo ta rungumeta tana murna sosai da ganin yar uwarta, Anwar ma ya fito yana dariya ya gaishe da Aminu, Aminu ya amsa yana kama hannunsa tarw'e da tambayarsa makaranta, Umma da yaya Zaidu suka fito suna yi musu maraba, sai suka yada zango a barandar gidan kan shinfiɗar babban tabarma, nan suka shiga gaisawa daga bisabi suka shiga hirar yaushe gamo, sai umma ce ta katse hirar tana cewa.

Sameeha maza tashi ku shiga ciki abinci yana nan a falo ki zuba muku dan na san da wuya in kunci wani abu.

Wlh kamar kin san muna jin yunwa kuwa, Abban Amrah, Abi da Amrah mu shiga ciki kun ji mu fara cika k'kundunmu kafin mu cigaba da hira, dan yau nasan sai dare ya raba muna aikin abu guda, duk sai an bani labaran abubuwan da faru da bamu nan.
Chapter 3 · 0% Book details